Shigo da hatsi kasar nan kalubale ne ga manomanmu – Penbeguwa
Kungiyar Masu Noman Hatsi ta Jihar Kaduna ta koka kan yadda ake barin wadansu na safarar hatsi zuwa kasar nan musamman masara inda suka ce hakan kalubale ne ga manoman kasar nan. Shugaban Kungiyar Alhaji Haruna Ahmad Pambeguwa ya bayyana haka, inda ya ce barin a rika shigo da hatsi cikin kasar nan ya kawo […]
Kungiyar Masu Noman Hatsi ta Jihar Kaduna ta koka kan yadda ake barin wadansu na safarar hatsi zuwa kasar nan musamman masara inda suka ce hakan kalubale ne ga manoman kasar nan.
Shugaban Kungiyar Alhaji Haruna Ahmad Pambeguwa ya bayyana haka, inda ya ce barin a rika shigo da hatsi cikin kasar nan ya kawo babban cikas ga harkar noma musamman a yankunan karkara.
Ya dai bayyana haka ne a lokacin wata ziyara da ya kai ofishin shugaban wani shiri da aka samar da ke tallafa wa manoma wajen sayar da kayan noma wato APPEALS Project a Kaduna.
Ya ce shigo da masara da aka yi ya shafi farashin hatsi a kasuwannin jihar inda a cewarsa hakan bai dace ba domin yana shafar ribar manoma.
“Muna son gwamnati ta dakatar da shigo da hatsi musamman masara da ake yi cikin kasar nan saboda hakan na shafar harkar noma. Muna sane da cewa akwai mutanen da ke shigo da hatsi duk da cewa an rufe kan iyakokin kasar nan. Wannan na shafar farashin kayan hatsi musamman masara,” inji shi.
Ya ce babu dalilin da za a bar wadansu su rika shigo da masara kasar nan tunda manoman kasar nan za su iya noma fiye da abin da ake bukata a kasar nan har ma su sayar ga kasashe makwabta.
Alhaji Haruna ya bayyana cewa sun ziyarci ofishin Appeals ne domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen taimaka wa ’ya’yan kungiyar ta yadda za su rika sayar da kayayyakinsu na gona cikin sauki.
A jawabin Ko’odinetan APEALS Alhaji Yahaya Aminu ya ce an fito da tsarin ne domin bai wa kananan manoma dama ta yadda za su inganta kayan gonarsu musamman hatsi domin su samu saukin sayarwa.
Ya bayyana shirinsu na wayar wa manoma kai ta yadda za su rika inganta abin da suke nomawa da koyar da su dabarun da za su rika ajiye abin da suka noma na tsawon wasu lokuta kafin su sayar ba tare da sun lalace ba.
Alhaji Yahaya Aminu ya kuma ce kofarsu a bude take wajen saurarar matsalolin manoma ta yadda za a inganta kasuwancinsu.