Shigo da motocin kasaita: Kwastam ta dakile masu zagon kasa

Rundunar Kwastam ta FOU shiyya ta ‘A’ da ke Ikeja a Legas, ta yi nasarar dakile shirin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya da wani dan kasar Lebanon Mista Fares Chawich da Cif Emmanuel Ekong dan Najeriya suka yi, ta hanyar hada baki da wasu jami’an kwastam da suka rubuta takardun biyan kudin haraji na […]

Shigo da motocin kasaita: Kwastam ta dakile masu zagon kasa
Shigo da motocin kasaita: Kwastam ta dakile masu zagon kasa

Rundunar Kwastam ta FOU shiyya ta ‘A’ da ke Ikeja a Legas, ta yi nasarar dakile shirin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya da wani dan kasar Lebanon Mista Fares Chawich da Cif Emmanuel Ekong dan Najeriya suka yi, ta hanyar hada baki da wasu jami’an kwastam da suka rubuta takardun biyan kudin haraji na bogi suka biya kudi Naira dubu 404 a maimakon Naira miliyan 232 ga wasu kananan motocin kasaita guda 7 da kiyasin kudinsu ya haura Naira miliyan dubu 1 suka fitar da su daga tashoshin jiragen ruwa na kasa.

Yanzu haka hedkwatar Hukumar Kwastam a Abuja ta dakatar da wadannan jami’ai daga aiki har zuwa lokacin da aka kammala bincike a yayin da aka kama Mista Fares Chawich aka gurfanar da shi gaban kotu amma ubangidansa Cif Emmanuel Ekong ya yi layar zana. Su kuma motocin na kasaita da aka boye su a cikin gidan Cif Emmanuel Ekong da ke GRA Ikeja, an mayar da su zuwa ofishin rundunar kwastam ta FOU ‘A’ da ke Ikeja.
Da yake yin bayani ga wakilinmu bayan nuna motocin ga ’yan jarida a ofishinsa da ke Legas, Kwamandan rundunar, Kwanturola Turaki Usman Adamu ya ce, “Binciken kwakwaf da muka gudanar ne ya kai ga wannan gagarumar nasara da muka gano ainihin sunayen jami’an da aka hada baki da su suka sanya hannu a kan takardun bogi suka fitar da motocin daga tashoshin jiragen ruwa, ba tare da biyan harajin da ya dace ga aljihun Gwamnatin Tarayya ba. Mun dade muna gudanar da irin wannan aiki a baya domin dawo da martabar Kwastam ta fannin kawar da bata gari daga cikin jami’anmu kuma wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.”
Ya ce: “Tun da batun gyara ake yi dole mu ma’aikata da ’yan kasuwa da jama’a baki daya mu hada kai domin yin gyran da kanmu da zai ceto kasarmu daga tabarbarewar tattalin arziki saboda babu wanda zai zo ya yi mana wannan gyara daga waje.”
Kwanturola Turaki Usman, ya kawo misali da daya daga cikin wadannan motoci wacce aka yi mata kira ta musamman mai suna Marsandi BRABUS G800 ta shekarar 2013 da aka sayo ta a kan kudi Yuro miliyan 1 da dubu 200 (kwatankwacin Naira miliyan 276) amma aka canza takardunta da sunanta zuwa karamar Marsandi 340 aka biya mata harajin kudi Naira dubu 404 kacal a maimakon naira miliyan 78.
Ya ce, kafin a kama shi “sai da na aika masu rubutacciyar takardar sammaci cewa, su kawo mana hakikanin takardun wadannan motoci da halaccin shigowa da su cikin kasa amma suka ki zuwa, shi ne dalilin da yasa na bayar da umarnin lika wa motocin takardun hana amfani da su zuwa lokacin da za mu kammala bincike. Daga baya wannan mutumi ya zo dauke da takardun motocin a hannunsa da muka gano an canza shekarun da aka kera su da sunayensu da harajin kudi Naira dubu 404 kacal wanda hankali ba zai dauka ba. Muka nuna rashin amicewa da takardun na sa wanda ya nemi alfarmar lokaci da zai dawo ya biya halastaccen haraji. Amma a maimakon haka sai ya shigar da kara kotu yana neman mu biya shi diyyar Naira miliyan 10 saboda mun shiga muhallinsu da lika takardu a jikin motocinsu ba tare da izni ba kuma ya nemi kotu ta dakatar da mu daga karbar kudaden harajin. Kotun ta ce ba ta da hurumin sauraron karar kuma Hukumar Kwastam tana da ikon shiga cikin irin wannan wuri domin gudanar da aikinta ba tare waranti ba. A daidai wannan lokaci ne wannan mutumi ya cire takardunmu daga jikin daya daga cikin motocin da ya fara amfani da ita ba tare da saninmu ba. Matakin raina mahukuntan Najeriya da wannan kwara dan Lebanon ya dauka shi ne yasa na bayar da umarnin a kama shi kuma a kwaso motocin daga cikin gidan a dawo da su ofishinmu.”