Shigo-shigo-ba-zurfi
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara waiwayar yankin Arewacin kasar nan da wasu manyan ayyukan raya kasa, domin kuwa a ranar Larabar da ta gabata Majalisar Ministoci ta bayar da wasu muhimman kwangiloli guda biyu da za su daukaka matsayin shiyyar Arewa-maso-Yamma, inda daya daga cikin wadannan ayyukan kuwa shi ne na farfado da filin […]
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fara waiwayar yankin Arewacin kasar nan da wasu manyan ayyukan raya kasa, domin kuwa a ranar Larabar da ta gabata Majalisar Ministoci ta bayar da wasu muhimman kwangiloli guda biyu da za su daukaka matsayin shiyyar Arewa-maso-Yamma, inda daya daga cikin wadannan ayyukan kuwa shi ne na farfado da filin jirgin saman Malam Aminu Kano, wanda za a batar da Naira sama da miliyan dubu dari shida don aiwatarwa. Gudan kuma shi ne aikin tagwayen hanyoyin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya, a kuma zarce da su har Kano, yayin da za a fadada su har fallan-uku, a kuma shimfida sabuwar kwaltar nylon a bisansu.
Babu shakka wadannan ayyukan za su inganta matsayin garuruwan Abuja da Kaduna da Zariya da kuma Kano ganin cewa suna da gagarumiun muhimanci a shiyyar Arewa-maso-Yamma da kuma Babban Birnin Tarayyar Abuja. Inganta filin jirgin saman Malam Aminu Kano zai dawo da martabar tashar jirgin saman a makwafinsa na daya daga cikin filayen jiragen sama na farko da Turawa suka kakkafa a nahiyar Afirka don hulda da kasarsu a zamanin da suke mulkin mallaka. Su kuma wadancan tagwayen hanyoyin da za a narkar da Naira sama da miliyan dubu kari da hamsin da biyar don sabuntawa nan da shekaru uku masu zuwa za su taimaka wajen habaka tattalin arzikin garuruwan da ayyukan za su shafa, za su kuma inganta zirga-zirgan bil-adama da kayayyakin sayarwa da na amfani a gidaje da wuraren aiki da kuma saukaka jigilar amfanin goma zuwa manyan kasuwanni.
Hobbasar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi dangane da haka ya biyo bayan korafe-korafe ne da mutanen da suka zurara masa fiye da rabin kuri’un da suka mayar da shi shugaban kasa a zaben shekrar 2019 suka yi ta yi ne suna cewa ya fi mayar da hankali ga shiyyar Kudu-maso-Yamma, inda aka dade da aiwatar da wasu muhimman ayyukan layukan dogon jirgi da ingantattun hanyoyin mota da kuma samar da wutar lantarki ba daukewa a dan-tsukin garuruwan Lagos zuwa Ibadan, inda kuri’un da al’ummomin yankin suka ba shi ba su kai kashi daya bisa uku na yawan wadanda mutanen shiyyar Arewa-maso Yamma suka ba shi ba.
Shi ya sa mutanen shiyyoyin Arewa ke cewa duk da haka nan dai an kyauta da aka waiwaye su a lokacin da ake matukar bukatar ayyukan raya yankunansu, domin a cewarsu da babu ai gara ba dadi, kuma wanda ya ba ka gutsurten goro watarana bari ma zai mika maka. To amma sai dai akwai wadanda ke ganin cewa ai akwai ayyukan wasu tagwayen hanyoyi masu muhimmancin gaske da aka faro aikinsu tun l farkon hawan Shugaba Olusegun Obasanjo a karon farko, fiye da shekaru goma sha hudu, an kuma yi nisa da su, amma aka watsar da aikinsu. Akwai tagwayen hanyoyi daga Kano, wadanda suka ratsa ta cikin jihohin Jigawa da Bauchi da Yobe har zuwa Maiduguri a Jihar Barno da kuma wadanda suka tashi daga Babban Birnin Tarayyar Abuja zuwa Lokoja wadanda ke da gagarumin muhimmanci wajen bubbude shiyyoyin da suka ratsa ta cikinsu amma ba a waiwayarsu balle a san lokacin kammaluwarsu.
Dangane da haka ne ake ganin mayar da hankali a yanzu kan wasu ayyuka a yankin Arewa na da alaka da siyasa da kuma zaben shekarar 2019. Irin wadannan ayyukan da za a tsira, a kuma kayyade lokacin kammala su fiye da wa’adin da gwamnatin da ta tsire su za ta yi bisa mulki, su ne matattakalan da gwamnati ke son bi don ta sake hayewa a karo na biyu, saboda idan ta fara aiwatarwa za ta kuma dan jinkirta don ta shafawa talakawa mai a baki cewa za ta kammala idan har sun sake amince mata ta zarce a karo na biyu. Ta haka ne sai ta samu amincewa muddin dai talakawan sun yarda da cewa idan ta zarce za ta ci gaba da gudanar da aikin. To amma akwai tabbacin cewa gwamnatin za ta kuwa cika alkawarin kammala irin wadancan ayyukan da ta faro a karon farko kuwa? Ai ga shi nan haka ne ma Gwamnatin Olusegun Obasanjo ta yi game da wadancan hnyoyin daga Kano zuwa Maiduguri da kuma Abuja zuwa Lokoja, kuma har yanzu ba a kammala ba. Irin wannan al’amari shi ake kira sayen biri a bisa domin kuwa talakawa ba za su iya ta hikankance sakamakon zaben da za a yi ba nan gaba.
To a yanzu an ga alamun irin kamun ludayin da gwamnatin tarayya ke son yi a shiyyar Arewa-maso-Gabas game da wadancan ayyukan hanyoyi da kuma filin jirgin sama, kuma ana iya cewa ta turza. Amma ai sauran gwamnatocin jihohi na wannan shiryar ba su taka wata rawar da za a yaba da ita ba wajen cika alkawurran da suka dauka yayin yakin neman zabe. Alal misali a Jihar Kaduna talakawa ba su dokin kwanzarta gwamnatinsu saboda a cewarsu babu wasu ayyukan a-zo-a-gani da ta aiwatar, sai dai ‘yan kanzaginsa ne sukacika duniya da yare a kafafen yada labarai kullu-yaumin game da ayyukan da ayyukan da ba a tabbatar da su ba, wadanda suke cewa ana ta shimfidawa a ko ina a fadin jihar.
A takaice dai ana iya cewa babu wata hanyar mota da ta hade wata karamar hukuma da wata, wacce aka shimfida mata kwaltar nylon, wacce kuma tsawonta ya kai kilomita ashirin da biyar da gwamnatin Jihar Kaduna za ta bugi kirji ta ce ta gina. Wadanda ma take tinkaho ta giggina ‘yan gutsul-gutsul ne a cikin wasu ‘yan unguwanni da aka bude su da rairayi ko burji, aka kuma zizara musu ‘yar kwaltar da aka hada da kura-kuran duwatsu. Ruwan daminar da aka yi a shekaru biyun da suka shude sun wanke hanyoyin har sun koma gidan jiya da wuya kuma masu amfani da su ke gane bambancinsu da yadda suke tun can fil-azal.
Baicin haka nan kuma ga ayyukan tagwayen titunan cikin unguwannin Dosa da Rigasa da Barnawa da aka faro kusan shekaru uku, amma an kasa kammalawa, kuma tun da ya zama wajibi ababen hawa su yi zirga-zirga bisansu ba abin da haka ke haddasawa illa kurar da bulbule mazauna wuraren suna kwalliya da ita, suna kuma fama da ciwurwukar da ba su iya samun magungunan warkarwa a asibitocin da gwamnatin ta kasa kulawa da su. A tadaice dai ana zargin cewa haka nan za a bar aikin wadancan hanyoyin unguwannin cikin garin Kaduna har sai Gwamnatin Nasir el-Rufa’i ta kusa kai karshen wa’adinta sa’annan ne za ta waiwaye su da niyyar janyo hankulan jama’ar wuraren cewa za ta kammala musu ayyukan idan har suka amince za su sake zabenta ta koma bisa mulki. Anya kuwa talakawa za su iya amincewa da wannan shigo shigo ba zurfin?