Shigowar sanyi: ’Yan kasuwa wasu na kuka wasu na murna

A daidai lokacin  da sanyi ya fara kankama a wasu sassan qasar nan musamman a Arewaci, kasuwanci da dama sun shiga cikin matsala saboda koma-baya da suka samu da kuma tabarbarewar farashi saboda buqatunsu ya yi qasa, wasu kuma kasuwancinsu ya bude ne saboda ana qara buqatarsu. Shi dai yanayin kasuwanci ya gaji hakan, duk […]

Shigowar sanyi: ’Yan kasuwa wasu na kuka wasu na murna

Shigowar sanyi: ’Yan kasuwa wasu na kuka wasu na murna

A daidai lokacin  da sanyi ya fara kankama a wasu sassan qasar nan musamman a Arewaci, kasuwanci da dama sun shiga cikin matsala saboda koma-baya da suka samu da kuma tabarbarewar farashi saboda buqatunsu ya yi qasa, wasu kuma kasuwancinsu ya bude ne saboda ana qara buqatarsu.

Shi dai yanayin kasuwanci ya gaji hakan, duk yanayi akwai irin kasuwancin da ya fi ja. Wannan ne ya sa Aminiya ta rairayo yadda yanayin sanyi da ya fara kunno kai yake shafar kasuwancin mutane.

A bangaren masu kasuwancin tufafin sanyi na gwanjo, kasuwarsu takan bude a irin wannan lokaci. A lokacin da wakilinmu ya isa babbar Kasuwar Jos da ta ’Yan Katako duk a Jos, ya gane wa idonsa yadda mutane suke ta sayen kayayyakin gwanjo.

A cewar Alhaji Ashura Babangida Isah mai sayar da gwanjo a garin Jos, “farashin gwanjon yana nan bai tashi ba. Amma kasuwa ta bude domin tun safe za ka ga mutane sun cika kasuwannin da ake sayar da gwanjo.”

A Kasuwar ’Yan Lemo, wakilinmu ya zanta da tsohon shugaban Qungiyar Masu Sayar da ’Ya’yan Itatuwa ta Najeriya Alhaji Salisu Abubakar Mai Lemo wanda ya bayyana cewa ko a lokacin sanyi suna samun ciniki.

Shi ma a zantawarsa da wakilinmu wani mai masana’antar yin ruwan sha na Leda na Ray Smith da ke Unguwar Abadawa a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, Mista Johnson Onwudiwe ya bayyana cewa a wannan lokaci da sanyi ya shigo, kasuwar sayen ruwa takan ja baya, inda wani lokaci ma sai dai su ajiye wasu motocin da suke kai ruwan zuwa wurare saboda rashin ciniki.

Shi kuma farashin abinci sun yi qasa a babbar Kasuwar Hatsi ta Saminaka kamar yadda Sarkin Hatsin Kasuwar Saminaka, Manu Isah Idris ya bayyana.

Aminiya ta gano cewa da ana sayar da buhun masara Naira 8,500 zuwa Naira 9,000 amma yanzu ana sayarwa Naira 6,500. Buhun shinkafa mai bawo kuma Naira 10,000 amma yanzu Naira 8,000. Haka kuma da ana sayar da buhun waken soya Naira 16,000 zuwa N17,000 amma yanzu ana sayarwa Naira 12,500.

A yankin Kudu maso Kudu kuma, yanzu ake tsananin zafi, inda wakilinmu ya ruwaito cewa su kuma a wannan yanayin na zafi ne kwakwar manja da goro suke yin ’ya’ya.

Sakataren Qungiyar ’Yan Kasuwar Goro Alhaji Bello Umar Fago ya bayyana wa Aminiya cewa, “Goro ya fi tsada bana saboda bai yi ’ya’ya ba sosai. Kafin zafin nan ya shigo muna sayen kowane buhun goro Naira dubu 4 da 500, amma yanzu muna sayensa Naira dubu 12.”

Shi kuwa Alhaji Nalami Nasiru dan kasuwar kayan abinci, ya ce an samu rangwame a kayan masarufi, “ Buhun Gero da muna sayensa Naira dubu 15 amma yanzu Naira dubu 11 yake. Wake da Naira dubu 30 yake, yanzu kuma Naira dubu 24. Garin kwaki da muna sayen daro Naira dubu 6 da 500, amma yanzu muna sayensa Naira dubu 3 da 200.”

A Jihar Katsina, Muntari Allah Wahid shugaban Qunagiyar Masu Sayar da Kayan Shayin Ataye wanda ake kira shayin buzaye ya bayyana cewa an fi sayen kayan shayin ataye lokacin sanyi. “Yanayin sanyi ya fi kawo mana ciniki kusan da qarin kashi biyu bisa uku na lokacin da ba a sanyin har da lokacin damina. Ka ga a yanzu mu a nan Jihar Katsina yanzu ne sanyin ya fara leqo kai, amma gaskiya tun yanzu an fara kasuwa. Wasu Shayin suke saye wasu kuma kayan shayin. Kuma duk da cewa sanyi na qaruwa hira na raguwa, mu ciniki yana qara sama.

Shi kuwa Malam Sama’ila daya daga cikin mutanan da muka tarar yana shan shayin cewa ya yi, “Ai duk lokacin sanyi babu abin da jikin mutun ke buqata irin wani abin da zai dumama jiki. Shayi kuma na daya daga cikinsu musamman irin wannan da ake hada wa da ganyaye. Kafin shigowar sanyi nakan sha shayin Naira 100 zuwa 150, amma tun yanzu na fara shan na 200 bayan na 200 da nake tafiya da shi gida.” inji Malam Sama’ila.

A Jihar Sakkwato kuwa, Alhaji Bello Jariri wanda aka fi sani da Aljeriya wanda ya kwashe fiye da shekara 12 yana kasuwancin ababen sha masu sanyi cewa ya yi idan sanyi ya zo, yakan juya akalar kasuwancinsa zuwa sayar da kayayyakin dafa ruwa da dumama daki “yanayin sanyi da ke taba kasuwancinmu bai wuce wata uku, in hakan ya faru sai na mayar da qarfi bangaren kayan wuta irin su butar dafa ruwa da hitar dafa ruwa da ta dumama daki domin wancan yakan tsaya” a cewar Aljeriya.

Malam Musa mai sayar da tufafi a tsohuwar Kasuwar Sakkwato, shi kuma cewa ya yi, “bara na samu cinikin kayan sanyi amma na safar hannu da abin rufe baki da huluna, amma riga da wando da bargo ba a samu kasuwa ba sosai.”

Malam Ibrahim Adamu wani mai sayar da rigunan kwat a daya daga cikin kasuwannin Abuja ya ce, “A yanzu haka rigar kwat ba ta wuce Naira 300 idan ma har an saya, wanda ke hade da wando kuma bai wuce Naira 600. Idan sanyin hunturu ya buga, muna sayar da riga kadai Naira 500 sannan wanda ke hade da wando Naira dubu 1.” A Jihar Kano kuwa ’yan kasuwar gwanjo tuni suka fara darawa saboda yadda kasuwarsu ke ja, inda shaguna da yawa suka mayar da hankali wajen bude dilar kayan sanyi.

Wani mai sayar da rigunan sanyi mai suna Malam Bature Auwal ya shaidawa Aminiya cewa, “A gaskiya ba kamar yadda mutane ke tunani cewa muke qara kudin kayayyakin saboda mun ga lokacin buqatarsuya zo. Abin ya samo asali ne daga inda muke saro kayan. Yanzu misali dilar kayan da muke samu a Naira dubu 100 yanzu sai mun sa Naira dubu 150 za mu samu. Kin ga kuwa ai dole mu fitar da kudinmu sannan mu yi maganar riba.”