Shigowar ’yan bindigar ƙasashen waje ta gigita Sakkwato
Al’ummar Jihar Sakkwato sun koka kan yadda ’yan bindiga ’yan ƙasashen waje da aka fi sani da Lakurawa ke ƙaruwar a yankunansu
Al’ummar Jihar Sakkwato sun koka kan yadda ’yan bindiga ’yan ƙasashen waje da aka fi sani da Lakurawa ke ƙaruwar a yankunansu.
’Yan bindigar da ke kyautata zaton sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar da Mali, sun sun kafa sansani a dajin Tsauna wanda ya ratsa kananan hukumomi uku a jihar Sakkwato har ya zuwa Jamhuriyar Nijar.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Tsauna da Tunbulukun a Ƙaramar Hukumar Illela; sai Bauni, Karma, Munwadata, da Gwaro a Ƙaramar Hukumar Tangaza da kuma yankin Gudungudun a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa.
Majiyoyi sun ce ’yan bindigar suna da irin akidar Boko Haram kuma sun shafe sama da shekaru uku a yankin.
- ’Yan bindiga sun sace mata 4 a asibiti a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Yadda Mutanen Maiduguri Za Su Kubuta Daga Illolin Ambaliya
Sun bayyana cewa da farko ’yan bindigar ’yan kasashen wajen sun haɗa kai da ’yan fashin daji da ke addabar al’ummomin, kafin daga bisani suka yi rikici da su.
“Bayan sun fatattaki ’yan fashin daji da dama, sun sanya wa waɗanda suka tsira da ransu aƙidarau, tare da kafa dokar Shari’a a kan al’ummomin yankin.
“Yayin da suke ba da kariya daga ’yan fashin daji, suna aiwatar da tsauraran dokoki Muslunci, ciki har da hukunta mutanen garin saboda aske gemu ko sauraron kiɗa,” in ji wani mazaunin, wanda ya nemi a sakaya sunansa.
Mazauna yankin, waɗanda galibinsu Musulmi ne, sun ce duk da cewa ba sa adawa da Shari’ar Shari’a, amma ba su amince da yadda ’yan bindigar kasashen wajen suke aiwatar da ita.
Sun yi nuni da cewa hukuncin ya wuce gona da iri kuma koyarwar Musulunci ba ta goyi bayan hakan ba.
“’Yan bindigar ba su kashe mutanen yankin ko yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.
“A maimakon haka, sun mayar da hankali ne wajen kai wa jami’an gwamnati da jami’an tsaro hari.
“Yawancin manyan hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro a yankin ana alakanta su da su.
“Al’ummomin sun kai rahoto ga hukuma, amma babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka.
“Wani yunkurin da sojoji suka yi ya yi sanadin mutuwar ’yan bindiga biyu, amma babu wani mataki da aka dauka tun daga lokacin,” in ji wani mazaunin garin.
Mashawarcin Gwamna Ahmed Aliyu kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman (mai ritaya) ya ki amincewa ko kuma musanta kasancewar ’yan bindigar a yankin.
Amma ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin ganin ta kare dukkan al’umma daga barazanar ’yan ta’adda.
Sai dai wata majiyar tsaro ta tabbatar da kasancewar ’yan bindigar a Dajin Tsauna, inda ta ce, “Mun samu rahoton sirri kan kasancewar su a dajin Tsauna, kuma muna duba lamarin. Ina tabbatar muku da gaske za a yi wani abu.”
A baya dai an fatattaki ’yan bindigar a wani samame da sojojin Najeriya da jami’an hukumar DSS suka kai a shekarar 2021, amma daga bisani ’yan bindigar suka sake dawowa yankin.
Har ya zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sanda da ke Jihar Sakkwato da kuma rundunar sojojin Najeriya ba su bayar da amsar tambayar wakilinmu game da lamarin ba.