Shin a ci gaba da ba tsagerun Neja-Delta tallafi ko a dakata?

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana ci gaba da biyan tsofaffin masu tayar da kayar baya na yankin Neja-Delta tallafi, bayan dakatar da hakan da ta yi watan Fabrairun da ya gabata. Shin a ci gaba da ba tsagerun tallafin ko a dakata? Ga yadda jama’a suka bayyana ra’ayinsu: Kada a ci gaba […]

Shin a ci gaba da ba tsagerun Neja-Delta tallafi ko a dakata?
Shin a ci gaba da ba tsagerun Neja-Delta tallafi ko a dakata?

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana ci gaba da biyan tsofaffin masu tayar da kayar baya na yankin Neja-Delta tallafi, bayan dakatar da hakan da ta yi watan Fabrairun da ya gabata. Shin a ci gaba da ba tsagerun tallafin ko a dakata? Ga yadda jama’a suka bayyana ra’ayinsu:

Kada a ci gaba da ba su – Malam  Dawud

Daga Adam Umar, Abuja

Malam Dawud Isa: “A ci gaba da ba su tallafi bai da amfani. Dalilina kuwa shi ne ana tallafawa mutum ne don ya tallafawa kansa har ya tallafawa wani. Sai dai su akasin hakan a ke samu, suna amfani da tallafi da kuma horo da a ka ba su ne wajen musgunawa al’umarsu da kuma sauran al’ummar kasa baki daya”.

Kada a ci gaba da ba su – Abdallah Caps

Ba na goyan ci gaba da biyansu – Malam Abdullahi

Babu laifi a ci gaba da ba su – Aliyu Abubakar

Daga Mohammad Yaba, Kaduna

Aliyu Abubakar: “Idan har ba su zai samar da zaman lafiya ya kamata a ci gaba da ba su domin ni babu abin da muke so a kasar nan da ya wuce a samu zaman lafiya. Ba ni san jin an fasa butu ko kuma wai bam ya tashi. Bayan haka ai tsohon Shugaban kasa marigayi Umaru ’Yar’adu’a shi ma ya ba su tallafi don haka babu laifi idan Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ci gaba da ba su”.

A ci gaba da ba su tallafin – Hassana Arkila

Daga Hamza Aliyu, Bauchi

Honarabul Hassana Arkila: “A gaskiya ina goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba tsagerun Neja-Delta tallafin alawus-alawus domin ta haka za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Babu dalilin da zai sa gwamnati ta dakatar da ba da kudaden tun da an dauki tsawon lokaci ana ba su. Mutane da dama a yankin ba sa noma sannan kuma ba su da tsaftataccen ruwan sha da sauransu”.

Ya dace a ci gaba da biyansu – Bello Dallaji

Daga Mohammad Yaba, Kaduna

Bello Idris Dallaji: “Gaskiya ina ganin ya da ce a ci gaba da ba su tun da ai ba Shugaba Muhammadu Buhari  ne ya fara ba su tallafin ba, kuma ni ina ganin rashin ba su ko in ce janye basu tallafin ne ya sa suka dawo da kai hari tare da fasa bututun mai. Saboda haka  idan aka ci gaba da ba su zai taimaka wajen hana su ci gaba da fasa bututun mai wanda fasawan na janyo matsala ga tattalin arzikin kasar nan. Ci gaba da ba su shi ne daidai a ra’ayina”.