Shin a ci gaba da bikin tuna ranar 12 ga Yuni ko a dakatar?
A kowace shekara, 12 ga watan Yuni na zama wata muhimmiyar ranar tunawa da soke zaven dimokuraxiyya da aka gudanar a 1993, inda aka tabbatar da cewa marigayi Chif M.K.O. Abiola ne ya lashe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a ci gaba da bikin tuna ranar ko kuwa a daina? Ga […]
A kowace shekara, 12 ga watan Yuni na zama wata muhimmiyar ranar tunawa da soke zaven dimokuraxiyya da aka gudanar a 1993, inda aka tabbatar da cewa marigayi Chif M.K.O. Abiola ne ya lashe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a ci gaba da bikin tuna ranar ko kuwa a daina? Ga ra’ayoyin da wakilanmu suka kalato daga mutane daban-daban:
Bai kamata a ci gaba da bikin ba – Ado Ibrahim
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Malam Ado Ibrahim Kwaya: “A ganina, kebe ranar 12 ga Yuni na duk shekara don tunawa da zaben marigayi Moshid Abiola hakan ba ta ma taso ba kwata-kwata. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, hakan ba komai zai haifar ba in banda kara yada siyasar bangaranci, kasancewar ’yan bangarensa ne ke hura wutar sai an yi hakan. Kuma ma ai hakan kan iya sake rura wutar siyasar kabilanci. Matukar an amince da wannan batu, to hakan kan iya sa kowa ma ya fito da bukatunsa.”
Bai dace a ci gaba da bikin ba – Malam Abba
Sani Gazas Chinade, a Damaturu
Malam Abba Mai Kayan Mota: “A ra’ayina, gaskiya ranar na da muhimmanci amma kuma duk da haka ba ta kai a rika tunawa da ita ba. Dalilina kuwa shi ne, ai akwai ranakun faruwar abubuwa masu matukar muhimmanci fiye da hakan amma ba a sa ranar tunawa da su ba. Don haka a gaskiya ban ga dalilin ci gaba da aje wata takamammar rana don tunawa da ranar zaben marigayi Abiola ba amma kuma in gwamnati ta yi hakan ba ni da ja.”
Ya kamata a ci gaba da bikin – Bello Gwadabawa
Nasiru Bello, a Sakkwato
Bello Gwadabawa: “Ya kamata a ci gaba da tunawa da ranar tun da ba gwamnati ce ta ayyana ranar a matsayin abar tunawa ba, kawai wasu jama’a ne na yankin Yarabawa suka ga ya kamata su yi don tunawa da dimokuradiyyar wancan lokaci da bukatar bikin ya harzuka mutane su rike sadaukarwa abin yi kamar yadda Abiola ya aikata. Wannan abu ne mai kyau ga talakka ya rika tuna fafutikar wani jigonsa don ya zama abin koyi kuma wanda ake tunawa da shi a ranar ana ganin shi ne ya lashe zabe a lokacin. Tuna rayuwarsa da Yarabawa ke yi abu ne mai kyau kuma ina goyon bayan su ci gaba da yi har koyaushe.”
Bai kamata a ci gaba da bikin ba – Abubakar Kilgori
Nasiru Bello, a Sakkwato
Abubakar Kilgori: “Wannan bikin sam bai dace a ci gaba da yinsa ba, don an wuce gona da iri. Wannan wuce makadi da rawa da Yarabawa suke yi a lokacin bikin, ya kamata gwamnati ta sanya musu aya haka nan, don ba Abiola ne kawai gwarzon dimokuradiyya a Najeriya ba. Akwai Shehu Musa da Sardauna da Azikiwe da sauransu amma ba wanda aka kirkiro wata rana don tunawa da wani abu da ya same shi na murna ko akasin haka. A wurina, tunawa da 12 ga Yuni abu ne da Yarabawa ke yi don nuna yanki da kabilanci, wanda ya kamata a kasar nan a kawar da haka, mu zama kasa daya al’umma daya don samun ci gaba mai dorewa.”
A dakatar da bikin ya fi – Umaru Muhammad
A.A. Masagala, a Benin
Malam Umaru Muhammad Zariya: “A gaskiya ni a yadda na fahimta, irin wannan bikin tamkar neman maida kasa ba ta da wata doka daga bangaren hukuma, duk da cewa mulkin dimokuradiyya muke a ciki na ’yanci amma ai ya kamata a duba a gane yaya ’yancin yake a dimokuradiyya? Ba wai kowane yunkuri na al’umma ne zai kasance ’yanci ba, domin wani yunkurin idan ya je ya dawo a karshe sai ya kawo fitina a kasa, tunda duk mai hankali ya sani biki ana yin sa ne a kan wani abu da al’umma suka samu na farin ciki. Don haka da wannan dalilin ya sa ban yarda ma bikin ake yi ba a 12 ga Yuni, don haka bana goyon bayan cewa a ci gaba da yin sa; tun da wani abu ne da nake ganinsa na nuna rashin da’a ga gwamnati. Kuma idan har hakan ya samu gindin zama ya dore, to lallai sai an samu matsala a nan gaba; don haka a bi hanyar ruwan sanyi a soke shirin da sauran mai kama da hakan.”
A ci gaba da bikin – Kabiru Abdullahi
A. A. Masagala, a Benin
Kabiru Abdullahi: “Ni a ra’ayina, ina ganin ya dace a ci gaba da yin bikin 12 ga Yuni, domin tunawa da tarihin wani dan siyasa kuma dan takarar shugabancin kasan da ya ci zabe aka hana shi. Sai dai kuma akwai abin lura a nan, shin masu yin bikin ba su da wata manufa ta nuna bambancin kabila ko neman tunzura al’ummarsu? To idan babu wannan, ya dace su ci gaba da yinsa saboda haka ina ganin idan ana yin bikin ne domin tunawa da shi, to wannan ya yi daidai; domin idan an ce a hana to sai a yi la’akari kuma da yadda sha’anin siyasa a kasar nan yake tafasar da zukatan wasu ’yan Najeriya da kuma kasancewar siyasar kasar mai sarkakiya ce. Barin masu yin bikin su ci gaba da abinsu ya fi zama alheri tsakaninsu da sauran mutanen Najeriya.”