Shin akwai amfani a tafiye-tafiyen da Shugaban Kasa ke yi?

A ’yan kwanakin nan ana cece-ku-ce kan yawan tafiye-tafiyen da Shugaban Kasa ke yi zuwa kasashen waje, har ma jam’iyyun adawa suna zargin cewar Shugaban Kasar ya kasa zama a gida don aiwatar da ayyukan ci gaban jama’ar da suka zabe shi. Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin jama’a kan wadannan tafiye-tafiye da Shugaban Kasar ke yi […]

Shin akwai amfani a tafiye-tafiyen da Shugaban Kasa ke yi?

A ’yan kwanakin nan ana cece-ku-ce kan yawan tafiye-tafiyen da Shugaban Kasa ke yi zuwa kasashen waje, har ma jam’iyyun adawa suna zargin cewar Shugaban Kasar ya kasa zama a gida don aiwatar da ayyukan ci gaban jama’ar da suka zabe shi. Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin jama’a kan wadannan tafiye-tafiye da Shugaban Kasar ke yi kamar haka:

 

Tafiyarsa Rasha kawai ce na ga amfaninta – Umaru Gwandu

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Akwai abubuwan da ya kamata Shugaba Buhari ya rika kula da su a tafiye-tafiyensa wato harkar difilomasiyya amma ba ruwansa da ita. Shi ne ya sanya dukkan tafiye-tafiyensa ban ga wani tasiri ba, tafiyarsa kasar Rasha ce kawai na ga amfaninta a dukkan tafiye-tafiyensa. Harkar difilomasiya ce ya kamata Shugaba Buhari ya inganta ba yawan tafiye-tafiye ba.

 

Ba mu ga amfanin tafiyar ba – Muhammad Ibrahim Amunike

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A gaskiya mu sam ba mu ga amfanin irin wadannan tafiye-tafiye da Shugaban Kasa yake yi ba. Domin duk tafiyar da yake yi har yanzu ba mu gani a kasa ba. Don hakaina ganin gara ya zauna a gida Najeriya ya yi ayyukan da za su taimaki al’umma ganin halin da jama’ar kasar nan suke ciki na halin ha’ula’i. Ya kamata Shugaban Kasa ya daina wadannan tafiye-tafiye ya tsaya ya kula da gida.

Ka ga mu al’ummar Arewa maso Gabas ba mu ga komai na ayyuka a wannan shiyya tamu ba, mussaman a Jihar Borno.

 

Tafiye-Tafiyen suna da amfani – Malam Isa Garun-Ali

Daga John D. Wada, Lafiya

Ba shakka wadannan tafiye-tafiye da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke yi suna da amfani, don a gaskiya al’ummar Najeriya suna amfana da tafiye-tafiyen. Kamar yadda ka sani babu wata kasa da za ta iya samun ci gaba a dukkan fannonin rayuwa da kanta ba tare da ta nemi hadin kan takwarorinta wasu kasashen daban ba. Shi ya sa yake tafiya yana samar mana hanyoyin ci gaba kuma alhamdullillah a takaice zan ce muna ganin sakamakon tafiye-tafiyen a kasa.

 

Tafiye-tafiyen suna da amfani – Ibrahim Mai Kassu Goronyo

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari yake yi suna da alfanu ga kasa, muna da kyakkyawan zato  gare shi, ba zai yi abin da bai da alfanu ga Najeriya ba. Duk lokacin da ya fita ya dawo sai ka ji an ba da bayanin dimbin nasarorin da aka samu a tafiyar da ya yi. Dubi zuwansa Saudiyya yadda aka samu cimma matsaya za a zo a gyara matatun manmu don kara bunkasa tattalin arzikinmu, ga saka hannun jari da bunkasa kasuwancinmu da sauran abubuwan gina kasa da tafiyar za ta kawo. Dubi tafiyarsa kasar China yadda aka cimma matsaya kan musayar kudi da sauran kasuwanci, tun a yanzu muna ganin sauyi da alfanun tafiye-tafiyen

 

Gaskiya akwai amfanin sosai –Ibrahim Lawal Maishago Area 11

Daga Muhammad Aminu Ahmad

A Gaskiya tafiye-tafiye da Shugaban Kasa ke yi zuwa kasashen waje na da amfani ga ci gaban kasar nan, ta fannoni da dama, kama daga harkar bunkasar tattalain arzikin kasa da kawo ayyukan ci gaban al’umma.

Tafiyarsa zuwa Rasha ya sanya hannu a kan huldar da ta shafi inganta rayuwar al’ummar kasar nan. Haka a China da Saudiyya da sauran kasashen da yaje yana jawo mana alherai masu yawa. Don haka tafiye-tafiyen da Buhari ke yi babban alheri ne, ga mu al’ummar kasa da kasar baki dayanta.

 

Babu wani amfani – Aminu Mohammed

Daga John D. Wada, Lafiya

A gaskiya babu wani alfanu a tafiye-tafiyen Shugaba Muhammadu Buhari. Don ina so ’yan Najeriya su tuna cewa a lokacin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi ire-iren wadannan tafiye-tafiye kuma sau da yawa idan ya dawo yakan bayyana nasarori da ya cimma a tafiyar musamman idan an tuna a daya daga cikin tafiye-tafiyen tsohon Shugaban Kasa Obasanjo akwai lokaci  da ya dawo ya sanar da ’yan Najeriya cewa an yafe wa Najeriya bashin da wasu kasashe ke bin ta. Amma ka ga Shugaba Buhari ba ya haka. Sai dai kawai ka ji yau yana kasar nan gobe yana wancan.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara