Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah (3)
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jin kai ga talikai, kuma manuni zuwa […]
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jin kai ga talikai, kuma manuni zuwa ga samun alheran duniya da Lahira; Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsa cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta, Amin.
Bayan haka, mun kwana a karkashin bayanin aya ta 62 (Surar Naml), inda har muka kai ga Hadisin da Imam Ahmad ya ruwaito dangane da wani mutumin Balhajim da ya tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), kan me yake kira zuwa gare shi, aka ba shi amsa, sannan mutumin (bayan ya gamsu da amsar da aka ba shi) ya ce, “To, ba ni shawara (kan abin da ya kamata in yi).” Ga ci gaba:
Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Kada ka zagi (ko ka zargi) kowa; kuma kada ka raina kankantar kowane irin aikin kwarai, koda kimanin haduwa da dan uwanka (Musulmi) ne da sakakkiyar fuska (kana murmushi); ko kuma ka zuba wa wani mabukaci ruwa a cikin dan kofinsa (kokonsa) don ya kore kishinsa. Ka (rika) sanya wandonka zuwa rabin kwaurinka – ko kuma, in har ba ka so (yin) haka ba – to, ka sanya shi (wandon) ya kai zuwa idon sawunka. Ina gargadinka (ahir dinka), ka guji sakin wandonka ya wuce idanun sawunka, har ma ya rika jan kasa (ko kana take shi), domin (yin haka) nau’in jiji-da-kai (dagawa) ne, kuma Allah ba Ya son (mai) jiji-da-kai.”