Shin Buhari ya takaita bincikensa a kan gwamnatin Jonathan ko ya hada da gwamnatocin baya?
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar kafa kotun musamman ga majalisa, wadda za ta saurari kararrakin cin hanci da rashawa kawai. Ko ya dace a takaita binciken ga gwamnatin Goodluck Jonathan, ko a hada da gwamnatocin baya? Babu laifi idan aka hada da na baya – Alhaji Shehu Alhaji […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar kafa kotun musamman ga majalisa, wadda za ta saurari kararrakin cin hanci da rashawa kawai. Ko ya dace a takaita binciken ga gwamnatin Goodluck Jonathan, ko a hada da gwamnatocin baya?
Babu laifi idan aka hada da na baya – Alhaji Shehu
Alhaji Shehu Ahmadu (Mai Sobo): “Binciken da gwamnatin ke gudanarwa abu ne mai matukar fa’ida. Ba abin da za mu ce sai godiya ga Allah .Ya kamata a yi binciken da kyau, idan aka fadada shi babu laifi,sai dai kar wannan al’amarin ya karkata alkiblar wannan gwamnatin mai albarka domin hana yi wa jama’a ayyukan da za su hana yi wa jama’a ayyukan inganta rayuwarsu.”
A hada da gwamnatocin baya – Alhaji Rabo
Daga Muhammad danladi Ibrahim, Minna
Alhaji Rabo Mai kwai: “Gaskiya wannan binciken da Shugaba Muhammadu Buhari ya fara abu ne mai kyau domin kuwa ina matukar jin dadin haka. Ko a lahira ma sai an gudanar da binciken da zai sa a ware na wuta da na aljanna.Ina matukar goyon baya a fadada binciken zuwa mulkin tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo. Har ila yau, yakamata ya haska fitilar binciken har zuwa cikin hadimansa da kuma ministocin da zai nada.”
Kada a takaita binciken ga Jonathan kadai – Auwal
Daga Musa Kutama, a Kalaba
Auwal A. Suleman: “Gaskiya ina ganin cewa bai dace a takaita binciken akan gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Johanathan kawai ba. Domin kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulkin kasar nan ya yi alkawarin ba zai bar duk wanda ya saci kudin kasa, saboda haka kowaye a bincike shi don yin haka zai yi maganin masu son yin sata a gwamnatinsa.”
A binciki har gwamnatin Obasanjo – Abdu Ibrahim
Daga Lubabatu I. Garba
Abdu Ibrahim: “Ya binciki gwamnatin Goodluck Jonathan da ta Olesegun Obasanjo kasancewar gwamnatocin biyu danjuma ne da danjummai. Idan an duba mutanen da suka yi gwamnatin Obasanjo kusan su ne suka yi gwamnatin Jonathan don haka gaba dayansu ya kamata a bincika. Babu gwamnatocin da aka sami kudi a kasar nan kamar lokacin wadannan gwamnatoci.”
Binciken ya tsaya kan Jonathan kawai – Sulaiman Saminu
Daga Lubabatu I. Garba
Sulaiman Saminu: “Ina ganin ya kamata gwamnatin Shugaba Muhamamdu Buhari ta tsaya ta yi bincike sosai a kan gwamnatin Goodluck Jonathan, domin ita ce gwamnatin da aka yi wadaka da dukiyar kasa. Idan aka tuna an sami kudi masu yawa a kasar nan, sai dai babu wasu ayyukan azo a gani da aka yi wa talaka daga su sai ’ya’yansu suka kwashe dukiyar.”
Kada a bar kowa – Bashir Abubakar
Daga Musa Kutama, a Kalaba
Bashir Abubakar Ahmad Sheka: “A yi adalci kowa a bincike shi saboda an dade ana zargin badakala a kasar nan da gwamnatocin baya suka yi, sun dade suna facaka da dukiyar kasa su yi yadda suka ga dama da ita misali duba ma’aikatar man fetur.”