Shin Burnham zai zama magajin Starmer a matsayin Firaministan Birtaniya?
Masana harkokin siyasa na ganin Burnham na da ƙwarewar sadarwa da jan hankalin jama’a.
Sabon ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya mai wakiltar mazaɓar Makerfield, Andy Burnham, ya samu kyakkyawar tarba daga ’yan jam’iyyar Labour a zauren majalisa bayan an rantsar da shi, lamarin da ya ƙara ƙarfafa hasashen cewa zai iya zama magajin Firaminista Keir Starmer a shugabancin jam’iyyar da kuma ƙasar.
Burnham ya shiga zauren Majalisar Wakilai ta Birtaniya ana masa tafi da murna daga ’yan jam’iyyar Labour, inda ya yi rantsuwar kama aiki tare da wasu sabbin ’yan majalisa biyu, Lara Bird ta jam’iyyar SNP da Douglas Lumsden na jam’iyyar Conservative.
- An dakatar da wani DPO daga aiki saboda karɓar na goro a Ribas
- Messi ya kafa sabon tarihin cin ƙwallaye a gasar Kofin Duniya
Yayin da yake ratsawa cikin zauren majalisar, Burnham ya riƙa sunkuyar da kai tare da murmushi ga ’yan majalisar da suka tarbe shi, kafin daga bisani ya gana da magoya bayansa a zauren Westminster.
Tsohon magajin garin Manchester ɗin ya daɗe yana da burin zama shugaban jam’iyyar Labour da kuma Firaministan Birtaniya.
Ya taɓa neman shugabancin jam’iyyar sau biyu a baya, amma ya sha kaye a hannun Ed Miliband a 2010 da kuma Jeremy Corbyn a 2015.
Burnham, mai shekara 56, ya fara zama ɗan majalisa a shekarar 2001, sannan ya riƙe manyan muƙamai a gwamnatocin tsofaffin firaministoci Tony Blair da Gordon Brown.
A shekarar 2017 ya bar majalisa domin tsayawa takarar magajin garin Manchester, inda ya yi nasara sau uku a jere, abin da ya sa ake yi masa laƙabi da “Sarkin Arewa” saboda yadda yake kare muradun yankin arewacin Ingila.
A baya-bayan nan, Burnham ya kasance cikin masu sukar wasu manufofin Keir Starmer, musamman batun rage tallafin jin daɗin jama’a, inda ya nemi jam’iyyar Labour ta rungumi manufofin da suka karkata daga wannan tsari.
Masana harkokin siyasa na ganin Burnham na da ƙwarewar sadarwa da jan hankalin jama’a, musamman bayan yadda ya yi fito-na-fito da tsohon Firaminista Boris Johnson a lokacin annobar COVID-19 kan batun tallafin da ake bai wa yankunan arewacin ƙasar.
Sai dai wasu na ganin har yanzu bai fayyace cikakken shirin da yake da shi wajen magance matsalolin tsadar rayuwa da tattalin arziki a Birtaniya ba.
Burnham, wanda ke da mata da ’ya’ya uku, ya shahara da wata akida da yake kira “Manchesterism”, wadda ya bayyana a matsayin tsarin gurguzu mai goyon bayan kasuwanci domin rage giɓin tattalin arziki da ƙara bunƙasa ci gaba.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da cewa shi ne zai gaji Starmer, kyakkyawar tarbar da ya samu a majalisa da kuma tasirinsa a cikin jam’iyyar Labour sun sa masu sharhi ke ganin yana cikin manyan ’yan takarar da za su iya zama Firaministan Birtaniya a nan gaba.
Starmer ya yi murabus
A safiyar wannan Litinin ɗin ce Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya sanar da yin murabus bayan shan matsin lamba kan jagorancinsa tsawon watanni.
A wani jawabi a wajen ofishinsa na 10 Downing Street, Starmer wanda ya hau mulki tun Yuli 2024, ya amince cewa ya rasa goyon bayan ’yan majalisar jam’iyyarsa ta Labour.
Ya ce ya shaida wa Sarkin Charles III shawararsa ta yin murabus domin a zaɓi sabon shugaban jam’iyyar Labour, wanda hakan zai sa a zaɓi sabon firaminista.
“Zan ci gaba da kasancewa a matsayin firaminista har sai takara ta kammala, sannan zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da miƙa mulki cikin tsari,” in ji shi.
Cikin yanayi na shessheƙar kuka ne Keir Starmer ya bayyana cewa zai haƙura da kowanne aiki tare da mayar da hankali wajen bai wa matar shi da yaranshi kulawar da ta kamata.
Murabus ɗin na Starmer kai tsaye ya buɗe wa Birtaniya ƙofar samar da firaminista na 7 cikin shekaru 10 a ƙasar, wadda ta faɗa cikin rikicin siyasa tun bayan ficewa daga ƙungiyar Tarayyar Turai.
Tsawon watanni Starmer ya shafe yana fuskantar matsin lamba tare da neman murabus ɗinsa, sai dai lamarin ya fi tsananta a yanzu tun bayan da Andy Burnham ya lashe zaɓe tare da dawowa Westminster.
Ikon Starmer ya fara raguwa tun bayan da Labour ta yi asarar kujeru a zaɓukan ƙananan hukumomi da na yankuna a watan Mayu.