Shin da gaske rigakafin COVID-19 na hana kamuwa da cutar?
Binciken jami’ar Oxford ya nuna allurar na rage yaduwar cutar, ba kamuwa da ita ba.
Duniya ta jima da yarda cewa allurar rigakafin COVID-19 na rage barazanar kamuwa da cutar mai tsanani, ko ma ta kai mutum ga kwanciya a asibiti.
Sai dai abin da har yanzu ba a kai ga tantancewa ba, in ban da a ’yan kwanakin nan, shi ne ko za ta iya rage barazanar yada cutar ga wasu.
- Matsafa sun kwace bindiga daga hannun ’yan sanda a Bayelsa
- An kama uba ya kai ’yan daba su doki malamin ’yarsa a makaranta
Tuni dai kasashe da dama suka sanya yin rigakafin a matsayin wani muhimmin sharadi na yin kusan dukkan muhimman abubuwa, ko ma nuna shaidarta kafin mutum ya sami izinin shiga kasashe da dama.
Ko a nan Najeriya, Jihohi da dama sun ce dole mutane su yi rigakafin muddin suna son cin gajiyar abubuwan gwamnati da dama.
Shin allurar na rage yaduwar cutar?
Wani bincike da jami’ar Oxford ta Burtaniya ta gudanar a kan samfurin Delta na cutar a kwanakin baya ya nuna cewa nau’in Pfizer da AstraZeneca na raigakafin su kan iya taka rawa wajen takaita yada cutar ga wasu.
Binciken dai ya duba kimanin mutum 1,500 da suka kamu da ita daga cikin kusan mutum 100,000 masu dauke da ita.
Mutanen da aka yi gwajin a kansu dai sun hada da wadanda aka yi wa rigakafin da wadanda ba a yi musu ba, da nufin gano wadanda suka fi barazanar yada ta, inda aka gano allurorin Pfizer da AstraZeneca suna da matukar tasiri wajen takaita yada ta.
Kazalika, bincike ya nuna dukkan allurorin biyu na rage yaduwar cutar, amma ta kamfanin Pfizer ta fi tasiri.
A baya dai, binciken da aka gudanar ya nuna cewa wadanda aka yi wa rigakafin da wadanda ba a yi musu ba suna da matsayi daya na cutar a jikinsu, amma wadanda aka yi wa na da karancin barazanar yada ta ga wasu.
Abu mai muhimmanci a fahimta shi ne wadanda aka yi wa rigakafin na samun wata kariya ta yadda garkuwar jikinsu za ta tsinkayi kwayar cutar sannan ta yi kokarin yakarta da sauri fiye da wanda ba a yi masa ba, kuma jikin nasa ba zai fahimce ta da wuri ba.
To sai dai wani hanzari ba gudu ba, binciken ya gano cewa sannu a hankali, kariyar da jikin wanda aka yi wa rigakafin ke samu kan gushe daga jikinsa bayan wani tsawon lokaci.
Watanni uku bayan an yi a wasu mutane rigakafin AstraZeneca, jikinsu ya nuna cewa suna da barazanar yada ta ga wasu kamar sauran wadanda ba a yi wa allurar ba.
Bugu da kari, binciken ya nuna cewa rigakafin ba tabbacin kariya ba ce cewa wanda aka yi wa ba zai taba kamuwa da cutar ba a nan gaba.
Madogara: Aljazeera