Ranar Mata: Shin daidaiton jinsi ne asalin abin da mata ke bukata?

“A fahimtata, mutuntawa da darajawa mace ke bukata, ba daidaito ba.”

Ranar Mata: Shin daidaiton jinsi ne asalin abin da mata ke bukata?

Daidaito tsakanin maza da mata na nufin yanayin samar da damammaki na nasarorin duniya kamar su ilimi, mukamai na siyasa, gudunmawa, daraja dan Adamtaka, da dai sauransu, ba tare da anyi la’akari da jinsi ba.

Ke nan yadda za a ba namiji dama, haka za a ba mace, hakan kuma zai yiwu ne kawai matukar al’umma ba ta kalli ’ya mace a matsayin nakasu ba, ko kuma ince al’umma ba ta nakasa ’ya mace ba.

Wasu kuma na kallon daidaito tsakanin mace da namiji a matsayin yanayin da ke samarwa mace damar ganin kanta a  tsarar da namiji, ta yadda zata yi komai kwatankwacin yadda namiji zai yi, ba tare da la’akari da al’adu da addini ba.

A matsayinmu na Hausawa, al’adunmu sun tafi a kan bambanci tsakanin jinsin mace da namiji, inda  a kodayaushe namiji shi ne gaba da ’ya mace. Haka zalika, addinan mu na Musulunci da Kiristanci  duk sun koyar da mu girman da ke tsakanin da namiji da ’ya mace ta fuskar mu’amala da shugabanci, don Aya guda Allah ya saukar aAlkur’ani cikin suratul Nisa’ai, aya ta 34 in da ya nuna girman namiji a matsayinsa na mai kula da hidimta wa mace ta fuskar kariya da samar mata da bukatunta na yau da kullum. Amma kuma hakan ba yana nufin addini ya nakasta mace ba ne daga samun nasara a rayuwa, sai dai a ce ya ba ta gata sama da da namiji.

Masu iya magana kan ce idan ana son sanin ci gaban al’umma,  to a kalli yadda ta ke tafiyar da ’ya’yanta mata. Al’ummar da ta ta’allaka amfanin ’ya’yanta mata ga aure da haihuwa tana tattare da nakasu, domin nasarar al’umma na hannun ’ya’ya mata, kuma hakan zai yiwu ne kawai in har ba a tawayar da ita daga samun ilimi ba.

Annabi Muhammad SAW ya ce: “Wanda ya ilmantar da da namiji ya ilmantar da mutum daya, yayin da wanda ya ilmantar da a mace ya ilmantar da al’umma.”

Wannan ya isa mu nutsu mu fahimci mahimmancin ’ya mace ga kowace al’umma, kazalika tawayar da ita ga aure da haihuwa kamar tawayar da al’umma ne.

Allah madaukakin sarki da ya halicci ’ya mace ya shar’anta wasu hakkoki wanda su ke daidai da na da namiji amma al’adu da dama su ka zo zuka danne wannan hakokkin don kawai nakasta ’ya mace, hakan kuma na cikin manyan dalilan da ya kawo ci baya a alumma.

Abu mafi muhimmanci da mace ke bukata  don samun nasara a rayuwarta shi ne ilimi. Kamar yadda za a sanya da namiji a makaranta a tabbatar da ya samu ilimin boko (ko sana’a) da na addini haka mace ke da wannan bukatar, yanke mata bukatar nan kamar binne ta da ranta ne.

Mace na da bukatar a tsaftata mata hanyar samun ilimin nan ba tare da tozarci ko cin mutunci ba, hakan zai sa mata natsuwar yin ilimin cikin nasara har a yi girbi mai amfani.

Mace tana da buƙatar a barta ta yi aiki ko sana’a, tana samun kudin shiga ta yadda za ta kula da kanta ta kula da iyalinta. Hakan na kara wa al’umma  ɗaukaka ta fuskar arziki saboda karuwan kudin shiga da al’ummar za ta samu ta hannun macen.

Mace tana bukatar goyon baya daga mazan da ke kewaye da ita, tun daga mahaifinta, ’yan uwanta maza, mijinta da kuma ’ya’yanta maza. Hakan kan zama  kamar ana ciccidata ne don hayewa tsanin nasara.

Idan muka koma tarihin Sahabbai, za mu ga yadda Annabi (SAW) ya basu damammaki kamar ba su damar fita jihadi da sauran maza, damar yin aikin jinya, ba su damar yin sana’o’i  da dai sauran su.

A fahimtata, ita mace ba daidaito ta ke bukata wajen samun nasara a rayuwa ba. Mutuntawa, darajawa sannan a sauke mata hakkin ta na ’yar Adam mace ke bukata, sannan a warware duk wani tawaya da al’adu suka dabaibayeta da su. A bar ta ta nemi ilimi cikin natsuwa da tsafta ba tare da ta fuskanci tozarci da cin mutunci ba.

A bar ta ta yi sana’arta hankali kwance tun daga aikin ofis har zuwa kasuwanci ba tare da an katange ta daga wata damar ba don a raunanata, ko a muzanta ta, ta hanyar cin zarafinta a matsayinta na ’ya mace.

A barta ta shiga harkar siyasa saboda ta wakilci ’yan uwanta mata, ko ba komi ciwon ’ya mace, na ’ya mace ne.

Yin hakan zai ba ta damar samun nasarori da ci gaba a rayuwa, har ma ta samu kwarin guiwar tarbiyyantar da yaran da za su taimaka wajen ci gaban al’umma.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele