Shin dakatar da shirin Ruga da gwamnati ta yi ya dace?

Shirin Ruga da Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar aiwatarwa don saukaka rikicin Fulani makiaya da manoma, ya jawo cece-kuce a kasar nan, inda  a wasu jihohi aka yi zanga-zanga nuna kyama ga shirin. Hakan ya sa gwamnatin ta dakatar da shirin, wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a kan dakatar da shirin nan na RUGA ga abin […]

Shin dakatar da shirin Ruga da gwamnati ta yi ya dace?

Shuaibu Garba

Shirin Ruga da Gwamnatin Tarayya ta kudiri aniyar aiwatarwa don saukaka rikicin Fulani makiaya da manoma, ya jawo cece-kuce a kasar nan, inda  a wasu jihohi aka yi zanga-zanga nuna kyama ga shirin. Hakan ya sa gwamnatin ta dakatar da shirin, wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a kan dakatar da shirin nan na RUGA ga abin da suke cewa:

Ba mu ji dadin tsayar da shirin ba  – Alhaji Hassan Kuraye

Daga Ahmed Kabir S/Kuka

A gaskiya ba mu ji dadin tsayar da wannan shiri ba, domin hakan ya nuna kamar an mayar da Fulani tamkar ba ’yan Najeriya ne ba. Muna ganin an bullo da tsarin da zai magance yawo da duk wasu matsalolin da ake fuskanta a tsakanin makiyaya da manoma ta hanyar tsugunar da Fulanin waje daya, ta yadda za su samu makaranta, asibiti da sauran duk wani kayan more rayuwa, ga kuma wajen kiwon dabbobinsu wanda kowa ya sani in babu nama babu zaman lafiya, amma a ce an dakatar. Gaskiya ba a yi adalci ba.

Dakatarwar ta yi daidai  – Abdullahi Binda

Daga Ahmed Kabir S/Kuka

Wannan canji da gwamnati ta yi na janye batun shirin RUGA an yi daidai. Idan muka lura da halin rashin tabbas da muke ciki kan batun tsaro, idan aka ce za a matsa cewa sai an aiwatar da shirin, to Allah ne kadai Ya san abin da zai biyo baya a  Arewar ma ba wai Kudu ko wasu kabilu ba. A ce za a tsugunar da shanu akalla dubu biyu ko uku a waje daya, kuma ba mallakin mutum daya ba, ai an san sai matsalar ta fi ta yanzu. Amma a koma tsarin da ake da shi a da na fitar musu da burtali da makiyayarsu da mashaya, shi ne ya fi kyau ba a ce suna waje daya ba. Sannan a dauki tsattsauran mataki ga masu cinye makiyaya shi ne kawai mafita.

 

Dakatar dashi ba alheri ba ne – Hussaini Hammangabdo

Daga Amina Abdullahi Yola

Shirin Ruga tun dama yana nan ba a habbaka shi ba ne. Jiha ita take da hurumi wajen kaddamar da wannan tsari bisa ga yadda take gudanar da ayyukanta na gona.

Amma da yake cece-kuce ya yi yawa sai aka yi wa habbaka arziki da ke tattare da dabbobi fahimta na daban aka yi mata musaya da Ruga. A koyaushe abubuwan da mutane ke fadi, dakatar da shi ba alheri ba ne ga makiyaya saboda shiri ne wanda zai wanzar da zaman lafiya a tsakanin manomi da makiyayi amma a matakin jiha.

Jama’a ne suka yi wa shirin wata fahimta ta daban domin a gaskiyar zance bai dace ba. Saboda wanda ya karanta ya duba, taswirar abin da yadda shirin yake lallai zai warkar da matsalar tashin hankalin da ke faruwa a tsakanin  manoma da makiyaya, don haka dakatar da shi bai dace ba mutane ne suka yi ma shirin mummunar fahimta.

Dakatarwar ba ta dace ba – Shu’aibu Garba

Daga Jamilu Adamu

Dakatarwa ba ta dace ba, dalili shi ne Fulani a wannan kasar an mayar da su saniyar ware babu wani abu da Fulani suke amfana da shi a kasar nan. Shirin samar da ruga na Gwamnatin Taraiya zai taimaka wa Fulani sosai, musanman ma wajen kawo karshen rikice-rikice da kasar nan ke fama da su, shirin zai taimaka wajen samar da lafiyayyun shanu da madara mai ingancin da nama mai kyau. Sannan shirin zai taimaka wajen ilimantar da ’ya’yan Fulani cikin sauki. A karshe ina kira ga gwamnati ta sake duba wannan al’amarin da kyau domin shi ne kadai mafita.

Dakatarwar ta yi daidai –Barnabas Manyan

Daga Amina Abdullahi Yola

Ra’ayina game da dakatar da shirin Ruga shi ne, tun a da can ma da ake yawo da shanu bai dace ba. Ya kamata duk wanda zai yi kasuwanci ya nemi fili ya sanya shanunsa a ciki. Ya daina shigar da shanu a gonakin mutane. Hakan ya sanya wadanda suka tashi suka ga ana yi shi ya sa suma suke yi. Tunda manomi ba zai iya daukar gonansa ya tafi da ita ba amma za a iya korar shanu daga wata kasa zuwa wata kasa. Gwamnati ya kamata ta ranta wa Fulani kudi ta yadda kowannensu zai samu fili inda zai kebe shanunsu da garkensu. Saboda kada a samu matsala a tsakanin manomi da makiyayi. Dakatar da Ruga da Shugaban Kasa ya yi, ya yi kyau domin bai kamata  Gwamnatin Tarayya ta karbi filin jama’a da karfi domin ba Fulani ba. Kamata ya yi a basu kudi kowa ya je garinsa inda ya fi wayo ya ajiye garkensa a ciki da iyalansu yadda hankalin kowa zai kwanta.

Bai dace ba – Abubakar Muhammad

Daga Jamilu Adamu

Dalili shi ne idan ka dubi irin rikice-rikice da ake samu a tsakanin makiyaya da manoma, yin ruga zai taimaka matuka wajen rage wadannan rikice-rikice. Sannan idan aka duba irin guduNmawar da makiyaya suke bai wa kasar nan, ko ba komai ai ya dace a taimake su. ruga na da matukar mahimmanci ga ’yan kasa musamman ma makiyaya. Ina kira ga gwamnati ta sake duba wannan al’amarin da kyau domin zai taimaka wajan kawo zaman lafiya a kasar nan.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara