Shin dan sandan Najeriya abokin kowa ne?

A wannan makon,  M. A. Faruk Sakkwato 08036029098, ya nazarci salon maganar da ake ta nanatawa, wato ‘dan sanda abokin kowa’ sannan ya rubuta want ton tsokacin:   Hukumar ’yan sanda, an kirkire ta ne bisa ga manufar tabbatar da doka da oda ga jama’ar kasa, domin su zauna lafiya, sa’annan su kula da masu […]

Shin dan sandan Najeriya abokin kowa ne?

A wannan makon,  M. A. Faruk Sakkwato 08036029098, ya nazarci salon maganar da ake ta nanatawa, wato ‘dan sanda abokin kowa’ sannan ya rubuta want ton tsokacin:

 

Hukumar ’yan sanda, an kirkire ta ne bisa ga manufar tabbatar da doka da oda ga jama’ar kasa, domin su zauna lafiya, sa’annan su kula da masu aikata laifuka.

Daga cikin ayukkan ’yan sanda, dole ne su tsare tare da kula da lafiyar jama’ar kasa, tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Hakkin ’yan sanda ne su kula da masu batarwa da satar dukiyar kasa, kamawa da tsare masu laifi kafin a zartar musu da hukunci.

A dokar kasa ko dokar ’yan sanda, ya zama wajibi su gudanar da ayukkansu na tsawon sa’o’i 24. Kasancewar su masu kula da doka da oda ne, za su kasance suna tsayuwa da yawo a kan manya da kananan tituna da kasuwanni da wajen tarukan jama’a da sauransu, domin tabbatar da tsaro ga jama’a da kare dukiyoyinsu. 

A hukumar ’yan sanda, akwai sassa da dama, kamar sashen samo bayanai (C.I.D.) da sashen ’yan sandan tafi da gidanka, akwai rundunar ’yan sandan dawaki da dai sauran sassa. Duk wadannan, an samr da su ne da nufin tabbatar da doka da oda ga jama’a.

Gwamnati tana iyakar nata kokari ga hukumar ’yan sanda na biyan su albashi yadda ya kamata. An saya musu jirage da motoci da manyan babura ga dawakai da manyan karnuka, ga gidaje gwamnati ta samar musu, kai har da bashin kayayyaki da na kudade, duk an samar musu domin kara inganta ayukkansu. Su kuma su kara kwazo da himma wajen tsarewa da kare jama’a da dukiyoyinsu.

Ita kuma al’umma tana ba da muhimmiyar gudunmuwa ga hukumar ’yan sanda da jami’anta, domin su ji dadin gudanar da ayukkansu cikin sauki da samun nasara, ba tare da cin zarafin wani ko wata ko wasu ba, ta hanyar ba da hadin kai da samar da muhimman bayanai ga jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro. Ta haka ne za a samu nasara wajen zakulo miyagun mutane da bata-gari da ke cikin al’umma.

A fannin ’yan sanda, ana son su kasance masu yin aiki bisa tsakani da Allah da bin dokokin da aikin ya tanadar da kare hakkin bil’adama, ta yadda za su gane mai gaskiya da marar gaskiya, mai laifi da marar laifi. Kada su ci zarafi ko musguna wa ga jama’ar gari. Ta haka ne martaba da darajar aikin ’yan sanda za ta daukaka.

Tambaya a nan ita ce, shin dan sanda abokin kowa ne?  Amsa: E, a’a! Dalili kuwa shi ne, a yanzu sunan ’yan sanda da martabar aikinsu sun fadi ga al’umma, sanadiyyar zalunci, cin zarafi da gallaza wa jama’a. Ga rashin sanin makamar aiki, keta haddi, tafka miyagun laifuka, shan barasa da kayan maye da kuma karbar hanci da rashawa da sauran miyagun ayyuka da mafi yawancinsu ke aikatawa.

Idan jama’a sun lura da idon basira, suka yi nazari, za mu gane cewa duk fitunu da masifu da rigingimu da ke faruwa a kasar nan, duk yawanci ’yan sanda ke haddasa su, sanadiyyar zalunci.

A duk safiyar Allah ta waye, in har ba ka gani ba, to za ka ji an ce wani ko wasu ’yan sanda sun tabka wata aika-aika ko sun ci zarafin jama’a ko yi musu barazanar harbi. Kai, har ta kai ga kisa ta hanyar harbi, ba don komai ba sai don zalunci da jahilcin rashin sanin makamar aiki. Idan sun tashi gallaza wa jama’a, ba ruwansu da babba ko karami, tsoho ko yaro, matar aure ko budurwa. 

Tilastawa a ba da na-goro (cin hanci) ya zama ruwan dare ga ’yan sanda a kan manya da kananan tituna da kuma wuraren zamansu ko kuma in ka je ofisoshinsu ko kuma lokacin bincike. A halin yanzu duk laifin da mutum ya aikata, komai muninsa, idan za ka bayar da cin hanci to kai ka tsira daga sharrnsu.

Daga cikin munanan ayyukan wasu ’yan sanda, sukan shiga cikin gungun ’yan fashi da makami, su je su aikata fashi ko sata. Sukan bayar da aron kayan aikinsu kamar bindiga, tufafi, harsashi ga miyagun mutane, a je a yi fashi da makami, a biya su. Sukan shiga cikin ’yan dabar da ke shaye-shayen kayan maye da barasa, a sha tare da su. Su ne ke tilasta wa jama’a dole su bayar da hanci, su ne safarar miyagun makamai da sauran ayyukan assha. Wadannan su ne ke hadassa gaba da kiyayya da faduwar daraja da mutuncin jami’an ’yan sanda da aikinsu ga al’umma

Ina mafita? Shawara a nan ita ce, gwamnati da hukumar ’yan sanda su kara sanya ido ga ayyukan jami’anta. A rika shirya masu tarukan kara wa juna sani, domin sanin mene ne aikinsu, su san yadda za su yi hulda da jama’a da sanin yadda za su gano mai laifi da marar laifi. Idan za a dauki sabbin jami’an ’yan sanda da jami’an tsaro, sai a koma a tsarin farko na sanin tarihi da asalin mutum. A samu shaida ga hakimi ko mai unguwa ko dagaci ko jama’ar da ke makwabtaka da shi, domin kauce wa daukar bata-gari da miyagun iri.

Ku kuma ’yan sanda ku ji tsoron Allah a duk inda kuka samu kanku a wurin aiki. Ku cire kwadayi da tunanin tara dukiya a kan haramun, ba bisa halali ba. Ku sani, kwadayi da son rai da zalunci, su ne ke jawo muku bakin jini ga al’umma kamar karnuka. Ku rika gode wa Allah a kodaayaushe. Ku sa kishin kasa da taimakon jama’a a zukatanku.

Mu kuma Al’umma, mu rika girmama doka da oda, mu kyautata halayyarmu domin samun nasara a rayuwarmu. Mu ji tsoron Allah, kada mu bayar da cin hanci ga jami’an ’yan sanda ko jami’an tsaro. Mu rika taimaka wa jami’an ’yan sanda da na tsaro da bayanai, domin samun zakulo miyagun mutane a cikin al’umma.

Daga karshe, ina mai addu’ar Allah Ya shiryar da mu, shiri na addinin Islama. Allah Ya ganar da mu gaskiya, ita ce gaskiya, Ya ba mu ikon bin gaskiya, Allah Ya tona asirin miyagun mutane makiya Musulunci amin. Allah Ya sa za a samu gyara ga hukumar ’yan sanda da sauran hukumomi a kasar nan, amin.