Shin dauki-dora da jam’iyyu ke yi wajen fitar da ‘yan takara zai haifar da da mai ido?
Shin dauki-dora da jam’iyyu ke yi wajen fitar da ‘yan takara zai haifar da da mai ido?A makonni da suka gabata ne aka kammala sabubbukan fid da gwani na jam’iyyun siyasar Najeriya. Abin da ya kawo cece-kuce a yawancin jihohi shi ne yadda jam’iyyun suka yi dauki-dora wajen fitar da ’yan takara ba tare da […]
Shin dauki-dora da jam’iyyu ke yi wajen fitar da ‘yan takara zai haifar da da mai ido?A makonni da suka gabata ne aka kammala sabubbukan fid da gwani na jam’iyyun siyasar Najeriya. Abin da ya kawo cece-kuce a yawancin jihohi shi ne yadda jam’iyyun suka yi dauki-dora wajen fitar da ’yan takara ba tare da la’akari da wadanda jama’a suke so ba. Wannan matsalar ta jawo matsaloli a jihohi da sabani mai yawa. Wannan ne ya sa wadansu suke ganin irin wannan dauki-dora zai iya jawo shirya makarkashiya da munafunci a siyasar da siyasar ubangida. Wannan ya sa muka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga abin da suke fada:
Dauki-dora abu ne da ke haifar da illoli masu yawa – Nuraddeen Harande Mahe
Daga Nasiru Bello, Sakkwato
Nuraddeen Harande Mahe: “Dauki-dora abu ne da ke haifar da illoli masu yawa a gaskiya domin ba a daukar wadada al’umma ke so sai wadanda gwamnati ke ra’ayi. A gefen jam’iyyar adawa kuwa sai wanda wani jagora ke so ne za a dora, da ya samu nasara ba ruwansa da kowa sai ubangidansa wanda ya dora shi. Ba za a samu ci gaba ba kuma mutane ba su son wannan lamarin don babu ci gaba a cikinsa. Misali dubi Jihar Zamfara yadda mutane suka fito don yakar dauki-dora abin da ya sanya APC ta yi hasarar kujerunta gaba daya. Wannan matsala ce babba, jagororin sun lalata jam’iyya wajen kokarin sai sun dora wadanda suke so. In har ana son ci gaba dole a daina wannan dabi’ar a bar mutane su zabi abin da suke so.”
Wani lokacin yana da kyau – Nafisa Muhammed
Daga Nasiru Bello, Sakkwato
Nafisa Muhammed: “Wani lokacin hakan yana da kyau, misali Gwamna ne ya kare wa’adinsa na mulki, kuma ya yi ayyukan more rayuwa, yana iya dubawa in ya sauka wane ne zai maye gurbinsa ya ci gaba da wadannan ayyuka, ka ga ko zai lalubo wanda zai zama kamarsa ko mutane ba su sonsa. A nawa tunanin wadanda suka yi aikin kwarai ne suka fi yin dauki-dora duk da ana samun wadansu da ba su da gaskiya ba su aikata alheri ba su tsaya dole sai sun kawo wanda zai boye ta’asar da suka yi don kada asiri ya tonu ko a fallasa su. Don haka dauki-dora a shugabanci yakan yi kyau don komai yana da alfanu da akasinsa.”
Yana da kyau kuma bai da kyau – Auwali Differences
Daga Umar Mohammed Gombe, Abuja
Alhaji Auwali Adamu Differences ya ce, “A inda aka dauki wanda ya dace, saboda ana kaddara cewa jam’iyya za ta fi sanin wanda ya dace din, to yana da kyau. A inda kuma aka ki daukar wanda ya dacen, saboda son kai ko son kudi irin na ubannin jam’iyya, to bai da kyau. Mu dauki Zamfara da Kano a matsayin misali. Duk rikicin da ke faruwa yanzu haka a wadannan jihohi ya samo asali ne daga dauki-dora. Saboda haka a takaice, ina da ra’ayin cewa tsarin dauki-dora zai iya zama abu mafi dadi a Najeriya idan aka tafiyar da shi bisa gaskiya da amana. Har ila yau, zai iya zama tsarin da za a yi amfani da shi domin hana wadansu mutane dama su shigo a dama da su a harkokin siyasa.”
Jam’iyya ya fi dacewa ta tsayar da dan takara – Yahaya Bako
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Yahaya Bako dalibi dan kasuwa: “Na amince da salon fito da dan takarar da ya samu amincewar jam’iyyarsa ko da kuwa jama’ar mazabarsa ba su amince ba. Dalilina shi ne an yi kuskure a zaben shekarar 2015 a inda aka zabi wadansu ’yan Majalisar Tarayya da jihohi wadanda da gangan suka ki yi wa jama’arsu aiki tsakani da Allah. Wannan ne ya sa a yanzu jam’iyyun suka bullo da salon dora mutumin da suka sani kuma suka amince da amanarsa cewa zai yi wa kasa aiki. Irin haka ya auku a Jihar Neja da jam’iyya ta ki kyale yin ta-zarce ga wadansu ’yan Majalisar Tarayya. Yin haka zai haifar da da mai ido a siyasar Najeriya nan gaba.”
Hakan na iya haifar da matsala – Abubakar Zubairu
Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan
Abubakar Zubairu dan kasuwa: “Ina ganin dora dan takara da jam’iyyu suke so zai haifar da matsala kuma ba zai yi tasiri a nan gaba ba. Matsalar ita ce, jama’a suna ganin cewa wannan mutumin suke so ya wakilce su ita kuma uwar jam’iyya ba ta amince da shi ba. Ka ga dole a samu rabuwar kawunan jama’a da yake haifar da ficewar jama’a daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Misali an taba yin haka a Jihar Kano a inda jama’a suka tsaya kai-da-fata cewa muddin jam’iyyarsu ta ki tsayar da wannan mutumin da suke so, to ya koma wata jam’iyya daban da za su mara masa baya. Ya kamata jam’iyyu su yi taka-tsantsan domin guje wa komawa gidan jiya a maimakon ci gaba.”
Tsarin dauki-dora ya danganta – Mubarak Umar
Daga Umar Mohammed Gombe, Abuja
Alhaji Mubarak Umar ya ce, “A nawa nazari da fahimtar, dauki-dora iri biyu ne, ya danganta da tsari ko mubaya’ar da al’ummar suke yi wa jagoransu. ’Yan siyasa suna da dalilai da yawa na dora wanda suke so ya gaje su, a wasu wuraren, hakan yana haifar da da mai ido, a wasu kuma akasin haka. Misali, Shugaban da Allah Ya jarabce shi da son al’ummarsa, yake kuma fatan ganin ci gabanta, ko yana kan mulki, ko ba ya kai, zai so a ce ya dora magaji wanda zai ci gaba da ayyukan alherin da ya faro. Amma a daya bangaren, dauki-dora na haifar da rikici irin na siyasa, wanda yakan iya tsayar da harkokin ci gaban al’ummar. Hakan na faruwa sakamakon son zuciya da ake sanyawa a gaba fiye da damuwar jama’a.”