Shin doka ba ta aiki a kan Soja ne?
Yadda motar sojoji ta murkushe wata budurwa tare da wadansu fasinjoji a cikin Keke NAPEP, ya sanya nake kira ga mahukuntan Jihar Yobe da jagororin sojojin da ke jagorantar yaƙi a Jihar Yobe game da yadda jami’an soji suke gudanar da aikinsu a jihar. A ranar Asabar din makon jiya an samu wani hadari a […]
Yadda motar sojoji ta murkushe wata budurwa tare da wadansu fasinjoji a cikin Keke NAPEP, ya sanya nake kira ga mahukuntan Jihar Yobe da jagororin sojojin da ke jagorantar yaƙi a Jihar Yobe game da yadda jami’an soji suke gudanar da aikinsu a jihar.
A ranar Asabar din makon jiya an samu wani hadari a cikin garin Damaturu a Kwanar Nagwange wanda ganganci da nuna isa da rashin bin doka. Hakan yana daya daga cikin abin da ya haifar da wannan hadari. Sojojin sun bi ta kan wani mai Keke NAPEP da fasinjojinsa wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran Husaina Bello, ɗaya daga cikin fasinsojin.
Tabbas al’ummar Jihar Yobe musamman na garin Damaturu sun kwana cikin jimamin faruwar wannan hadari. Ga duk wani mutum da ke Jihar Yobe ya san irin cin zarafi da rashin bin doka da sojoji ke nuna wa al’ummarmu. Sojojin sun sha fasa wa masu Keke NAPEP gilashi ko tamfol idan aka samu cinkoson ababen hawa a kan titi. Sakamakon ganin un sanye da rigar sarki ya sa suke cin zarafin kowa.
Idan wata gardama ta hada ku da su ka nuna ja sai a yi kokarin danganta ka da Boko Haram. Duk wani abu da ya zamo layi ake bi akasarinsu sai su nuna su ba za su bi ba.
Muna kira ga Gwamnatin Jihar Yobe da kungiyoyin kare hakkin dam Adam su sanya baki a wannan lamari su tabbatar an biya diyyar wannan baiwar Allah. A kuma kula da wadanda suka raunata, manyan jami’an soji su ma su ja kunnen kananan jami’an da ke sanadiyar rasa rayukan al’umma. A tabbatar an dakatar da tukin ganganci, domin kuwa wannan ba shi ne na farko ba.
Sa’idu Abdullahi [email protected]