Shin gwamnati ta dakatar da hada-hadar kuɗin intanet ta Binance a Nijeriya?
Gwamnati ta ɗauki matakin ne domin daƙile hauhawar farashin dala da faduwar darajar naira.
Rahotanni na cewa Gwamnatin Najeriya ta dakatar da hada-hadar kuɗin yanar gizo ta intanet ta dandalin Binance da sauran manhajoji da a Turance ake cryptocurrency.
An ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne a matsayin wani yunƙuri na daƙile hauhawar farashin dala da faduwar darajar naira.
- Kotu ta umarci ɗan Baba Impossible ya yi rantsuwa kan zargin dalla wa likita mari
- Gwamnatin Soji ta karya farashin shinkafa a Nijar
Masu musayar kuɗaɗe a kasar da kuma hukumomi na zargin masu hada-hadar kuɗi ta intanet da ba da gagarumar gudunmuwa wajen tashin farashin dala a kasar, abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.
Majiyoyi daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na kasar sun shaida wa Premium Times da yammacin Laraba cewa Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta mika musu umarnin dakatar da hada-hadar kuɗin intanet kuma sun fara aiki da shi.
Bayanai sun ce a jiya Larabar ne hukumomi suka bai wa kamfanonin waya na kasar umarnin toshe damar shiga manhajojin, domin hana masu hada-hadar kuɗaɗe ta intanet damar shiga su yi cinikayya.
Manyan kamfanin da matakin ya shafa a cewar bayanan sun haɗa da Binance, da Forextime, da OctaFX, da Crypto, da FXTM, da Coinbase, da Kraken da sauransu.
To sai dai su ma a nasu bangaren, tuni kamfanoni na hada-hadar kuɗaɗen ta intanet suka fara ɗaukar matakan daƙile cinikayya tsakanin dala da naira barkatai.
Wannan matakin da Gwamnatin Nijeriya ta ɗauka shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin matakan da take ɗauka don magance tashin farashin dala, abin da yake haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a kasar.