Shin hakkin maye na da alfanu?

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa  cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin. Shin Hakkin Maye na da alfanu? Sakamakon bayanan da suka gabata a kan […]

Shin hakkin maye na da alfanu?
Shin hakkin maye na da alfanu?

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa  cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.

Shin Hakkin Maye na da alfanu?

Sakamakon bayanan da suka gabata a kan nau’o’in abinci masu inganta lafiyar sha’awa da yawa ’yan uwa mata sun aiko da tambayoyinsu game da inganci ko rashin ingancin hakkin maye, kayan mata ko kayan da’a.

 

*Amfani da ire-iren kayan karin kuzari ko motsa sha’awa, ya halatta a Musulunci, domin amfani da wani abinci, abin sha ko abin shafawa don neman waraka ko gyara wata tangardar da ta samu jikin dan Adam halal ne, matukar abin ba najasa ba ne, mushe ko mai sa maye, kuma matukar ba zai cutar da lafiyar mai amfani da shi ba ko yaya ne. Domin haram ne yin magani da abin da yake marar tsarki ko mai tsarki amma harammatacce ne ko mai cutarwa. Kuma Annabin Rahma (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: “Ya kasance ba cuta ba kuma mayar da cuta.”

* Sannan yana da kyau a kiyaye kada a yi almubazzaranci wajen amfani da su kuma kada mutum ya mayar da amfani da su dabi’a ta yadda kullum yana faman neman ire-irensu ba da wani kwakwkwaran dalili ba.

*Haka kuma bai dace ba yin amfani da su ba bisa ka’ida ba, wato bai halatta ga lafiyayyen mutum, namiji ko mace su yi amfani da su ba tare da bukatar hakan ta taso ba, kamar raunin mazakuta a dalilin wata rashin lafiya ko gabatowar tsufa, domin yawancinsu suna da wata illa tare ko yaya ne da amfaninsu, wadanda ba su da illa kuma ba amfanin shan su ga lafiyayyen mutum. “Magani dai kamar sabulu ne, zai wanke kaya fes, amma kuma a hankali zai kodar da su” haka wani mai hikima ya fada.

*In muka yi la’akari da yawancin kayan da’a da na karin kuzarin sha’awar da suka yawaita a cikin wannan kasa tamu za mu ga cewa yawancinsu ko dai akwai cuta ko kuma akwai cutarwa, don haka ’yan uwa sai a kiyaye  kuma a yi dogon nazari kafin amfani da su, don haka yana da kyau uwargida ta auna ta gani shin amfanin da za su yi mata amfani ne mai taimakonta a duniyarta da lahirarta ko kuwa amfani ne na jin dadi kalilan daga baya kuma ya haifar da wata gagarumar matsalar?

*Illar da ke cikin hakkin maye ta fi alfanunsa yawa, saboda yawanci ba wai aikin da aka ce suke yi lallai suna yi din ba, amma imani da suna yi din, shi ke sa suke alfanu sosai ga yawancin masu amfani da su. Kashi 70 cikin dari na wadannan magunguna suna aiki ne ta hanyar tsarin nan na ‘tsafi gaskiyar mai shi’ wanda a kimiyyance ake kira da ‘placebo effect’. In mutum ya sha sun yi masa aiki saboda ya yi imanin za su yi masa, illar na ga rashin sanin ainihin sinadaran da ke cikin wadannan hakukuwa da ganyayyaki da kuma irin illar da za su haifar ga jikin dan Adam, domin in mutum ya san illar da za su yi masa, to komai dadin alfanunsu dole mutum ya hakura.

*Sannan suna raba mutum da imaninsa, domin wasu kayan da’ar da tsafi ake hada su; don haka don guje wa fadawa ga halaka da kuma samun tsira ranar gobe Kiyama, sai a kiyaye su.

*Ya fi alfanu matan aure su dage wajen amfani da lafiyayyun abinci da abin sha da ganyayyaki, da kayan marmari da ’ya’yan itace sun fi tabbas kuma sun fi lafiya, maimakon a yi ta bata kudi da lokaci a kan abin da nan gaba yana iya haifar da matsaloli masu yawa har mu rika yin da- na- sanin amfani da su, domin akwai mamaki kan irin kudin da wadansu matan ke batawa wajen sayen irin wadannan kayayyaki.

*Yawaitar cutar kaba ta mahaifa da kansar mahaifa duk suna da nasaba da amfani da wannan kayayyaki da mata ke yi ba bisa ka’ida ba, da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.

*Kira ga mata masu tallata irin wadannan kaya a gidaje su ji tsoron Allah su bar sayar da shi ga ’yan mata marasa aure da karuwai, domin ku sani kuna samun zunubin wannan aiki duk lokacin da suka yi amfani da shi. Haka maza masu sayar da ire-iren kayayyakin nan a kasuwanni da tituna, ya fi kyautuwa ku kasance masu boye hajarku da tallarku, ana zuwa da yara kasuwa kuma suna ganin irin wadannan hajoji wanda haramun ne ga babba ma ya ga irin tsaraicin da ke dangane da irin hajoji balle kuma yaro, kallon irin wadannan takardu na bata fidirar da tsarkin ruhin yara kanana. Da fatan Allah Ya ba mu ikon gyarawa, amin.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.