Shin hana almajirai bara da Gwamnatin Kano ta yi ya dace?
Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta kafa dokar hana almajirai bara, inda suka bayyana ra’ayoyinsu game da wannan doka. Ga yadda ra’ayoyin suka kasance: Ya dace amma – Mahi Ahmad Balarabe Daga Lubabatu I. Garba, Kano Matakin hana bara da gwamnatin ta dauka ya dace, sai […]
Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda Gwamnatin Jihar Kano ta kafa dokar hana almajirai bara, inda suka bayyana ra’ayoyinsu game da wannan doka. Ga yadda ra’ayoyin suka kasance:
Ya dace amma – Mahi Ahmad Balarabe
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Matakin hana bara da gwamnatin ta dauka ya dace, sai dai kafin hakan kamata ya yi gwamnatin ta dauki matakin hana malamai daukar almajirai masu yawa. Kowa ya karbi almajirai daidai girman makarantarsa. Wannan zai sa kowane malami ya iya kula da almajiransa ta hanyar sama musu isasshen makwanci da abincinsu da sauransu.
Ta samu hadin kan sauran gwamnoni – Bashir Aminu Garba
Daga Lubabatu I. Garba, Kano
Kafin gwamnati ta yi hakan ya kamata ta nemi hadin kan sauran gwamnonin kasar nan yadda za su yi doka ta bai-daya ta hanyar mayar da kowane malami da almajiransa jiharsa tare da umartarsu su koma kauyensa su rika karatu a can. Hakan zai sa kowane almajiri ya zauna ya yi karatunsa a gaban iyayensa kamar yadda sauran ’ya’ya ke yi.
Bai dace a hana ba – Zainab Bala
Daga Amina Abdullahi, Yola
A ra’ayina bai dace ba. Saboda akwai talauci a tsakanin al’umma da dama. Mafi yawancin almajiran akwai wadanda iyayensu suka rasu, kuma kasancewar matsi da rashi, su kansu dangin yaran da kyar suke samar wa nasu iyalan abinci, ta yaya za su samar wa ’ya’yan ’yan uwansu da suka rasu? Hakan nake ganin yake sanya dangin yaran sanya su almajiranci.
Ina goyon bayan hana bara amma… – Aliyu Muhammadu
Daga Dalhatu Liman Abuja
Maganar hana wa mabarata na kan titi da kwaro-kwaro a birane bara, a gaskiya ina goyon bayan wannan. Amma ba na goyon bayan hana almajiran allo bararsu, saboda a ganina suna da rana ga kowa a kasar nan. Hatta ita gwamnatin kanta, tana sane da amfaninsu. Ba zan taba goyon bayan a rusa almajiran allo ba. Saboda su mutanen gwamnatin su ne ke zuwa wurin malaman wadannan almajirai suna neman addu’o’in dacewa da samun biyan bukatu. Amma yanzu su ne za su ce a rusa tsarin? To inda da gaske gwamnatin take yi na hana barace-barace, to ta fara hana masu bibiyar ofis-ofis, suna maula. Amma ba wadannan yara marasa galihu da wadansu ma marayu ne za a hana wa neman abinci ba. A sake nazari gaskiya!
Hana bara bai dace ba – Hajiya Aminatu Ahmad
Daga Ahmed Mohammed, Bauchi
Gwamnatin da ba ta iya ciyar da dalibanta da suke makarantar boko ba, ita ce za ta ciyar da almajirai? Gaskiya ya kamata Gwamna Ganduje ya duba wannan yanayi, kuma ya sake tunani a ganina ba a ba shi shawarar da ta dace ba. Ya kamata ya gyara. Ai makarantun almajiran su ne makarantun talakawa da suke kai ’ya’yansu makarantun kasar waje, ai su ya kamata su gyara.
Hana bara bai dace ba – Sanusi Ahmad Dahiru
Daga Ahmed Mohammed, Bauchi
A gaskiya hana bara da Gwamnatin Jihar Kano ta yi bai dace ba, saboda ba ta tanadar wa masu barar abin da za su ci ba. A addinin Musulunci kuwa ba za ka hana mai bara, sai in ka tanadar masa abin da zai ci. Ya kamata masu mulki su ji tsoron Allah kada su tsokani Allah garin kokarin taba masa miskinanSa. Ya kamata Shugaban Kasa da sauran masu fada-a-ji su yi wa gwamnatin da ta hana bara kashedin ta yi hattara kar ta jawo wa Najeriya bala’i.