Shin har yanzu Kano da Legas na da tasiri ga nasarar dan takarar shugaban kasa?
Legas da Kano ke kan gaba wajen yawan masu katin zabe, amma wanda ya ci zabe ba shi da rinjaye a jihohin
Zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, ya zo da sabbin abubuwa a tarihin siyasar Najeriya.
Baya ga nasarar da dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu ya samu, ya zamo mutum na biyu a Najeriya da ya ci zabe a karon farko da ya tsaya takara, bayan margayi Umaru Musa ’Yar Adua.
- Zamantakewar aure: Dalilin da mata ke neman shawara a kafofin sada zumunta
- Ka nemi lauyoyi ka nufi kotu —Martanin APC ga Atiku
Haka zalika, Tinubu ya zamo dan takarar shugaban kasa na farko da ya ci zabe ba tare da samun kuri’u mafiya rinjaye a Kano da Legas ba, jihohin da wasu ke ganin babu dan takarar shugaban kasa da zai kai labari ba tare da ya ci su ba.
Wannan tunani ba ya rasa nasaba da kasancewarsu jihohin biyu wadanda suka fi saura yawan al’umma da kuri’u, da kuma salon siyasarsu da ya bambanta da na saura.
Duk da cewa cin wadannan jihohi ba sharadi ba ne wajen lashe zaben shugaban kasa, ’yan takara da ’yan siyasa sukan bugi kirji a matsayin masu rinjaye, idan jam’iyyarsu ta samu galaba a mazabarsu, jiharsu ko yankin da suke mulki ko wakilci a lokacin zabe.
Sai dai a jihar Legas, mahaifar sabon zababben shugaban kasar Najeriya, abokin hamayyarsa dan Jam’iyyar LP,Peter Obi, wadnda ya zo na uku a zaben shugaban kasa ne ya samu kuri’a mafi yawa.
A Kano kuma, tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, ne ya samu kuri’u mafiya rinjaye, amma kuma ya zo na hudu a zaben shugaban kasa.
Karancin fitowar masu zabe ne —Masani
Kasancewar wannan ne karo na farko da aka taba samun haka a tarihin siyasar Najeriya ya sa muka tuntubi masana kan ko dama muhimmancin Legas da Kano ga tumbatsar dan takara zance ne kawai na baka.
Farfesa Kamilu Sani Fagge mai sharhi ne kan al’amuran siyasa, kuma malami a tsangayar Kimiyyar Siyasa da ke Jamil’ar Bayero ta Kano, ya ce samun kujerar shugaban kasa ba tare da kuri’un Kano ba da aka gani a wannan karon, ya faru ne saboda karancin wadanda suka fita zabe a bana.
Farfesa Kamilu Fagge ya ce idan aka yi la’akari da yawan wadanda suka yi zabe a Kano da Legas, za a ga sun yi karancin da ya sanya ba a samu wata tazara sosai ba tsakanin duka ’yan takarar.
“A baya saboda mutane na fitowa da yawa daga jihohin su yi zabe, ya sa ko iya su kadai dan takara ya samu za ki ga ya kusa kai labari saboda kuri’unsu kadai sun fi miliyan 10.
“To amma a wannan karon kuma gaskiya saboda ba a fito da yawa ba, shi ya sa ma za ki ga babu wata tazara sosai tsakanin ’yan takarar baki daya.”
Tasirin hakan
Ya ci gaba da cewa hakan ne ya sa “Gaba daya tazarar kuri’un da suka samu a kasar ma ba ta yi yawa ba; Kin ga batun a ce jihohin sun rasa tasirinsu ma babu shi.
“Amma fa mutane su sani tasirin zai ci gaba da karfi ne, idan jama’a sun fito zabe da yawa.
“Sannan wani abu da ya kara sanyawa bayan rashin yawan kuri’u a jihohin biyu Tinubu ya samu nasara, shi ne tasirin da jam’iyyun duka suka yi a sassan Najeriya baki daya.
“Wannan ya taimaka a faduwar dan takara a Kano da Legas, har ma da Kaduna, da saura manyan jihohi.
“A takaice dai idan mutanen jihohin ba sa fitowa zabe da yawan da aka san su da shi, tasirin jihohin zai kau, ya zama ba su da wani bambamci da sauran kananan jihohi, to ko bai ci zabe ba”, in ji Farfesa Fagge.
A ranar 22 ga watan Oktoban 2022 ne dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar daga cikin mutane 93,469,008 da suka yi rajistar zabe a Najeriya, jihohin ne ke kan gaba inda Leags ke da 7,060,195 , Kano kuma 5,921,370, sai Kaduna mai biye musu da 4,335,208.
Sai dai yayin tattara sakamakon zaben ranar 25 ga Fabrairu, hukumar ta ce mutane 1,335,729 ne suka yi zabe a Legas, Kano kuma 1,702,005, wanda hakan ke nuna duk da cewa Legas ce ke kan gaba a yawan masu rajistar zabe, amma wadanda suka fito kada kuri’a a Kano sun fi wadanda suka fito a Legas yawa.