Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Dokar ta zo daidai da lokaci -kasimu Assada
Dokar nan ta zo daidai da lokaci, ta dace sosai a rika amfani da ita ko zai kawo a rage gurbatattun malamai da dalibai a kasar nan. Ci-bayan da ake ta samu a kullum ta haujin ilmi ya ta’allaka ne ga sako-sakon dalibai da suka mayar da kansu ’yan cin jarabawa kawai ba wai suna karatu ne don su gane ba, amma wannan dokar za ta sa su canja halinsu na yin sako-sako da ilmi don sun san in suka yi satar jarabawa har aka kama su to boni ya ci su dole su kiyaye su daina. Da haka ya faru ko an samu nasara, ka ga haka gaskiya ya yi daidai.
Sai dai wani hanzari, ba gudu ba, gwamnati ta taimaka wajen magance matsalar ilmi, ba wannan kadai za a tsaya ba a ce kuma ya yi daidai ba.