Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?1
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Wannan dokar ta yi tsauri -Aminu Bates
Wannan dokar ta yi tsauri da yawa. Bai kamata a yi wannan danyen hukunci na rashin ba mutum damarsa ba. Kafin yin doka, ya kamata a fito da hanyoyin inganta ilmi mana! Yara ba wadataccen karatu da aka ba su kuma so ake su ci jarabawa; ga malaman nasu mafi yawa ba su da kwarewa da za su koyar da yara; dalibi bai samu an karantar da shi ba, lokacin jarabawa ya zo an kawo masa takardar tambayoyin da amsarsu. Malaminshi bai koya masa ba, yana tunanin yadda zai yi, sai malamin ya kawo masa mafita ta hanyar rubata masa amsa ga allo ko wata takarda daban sai ya kwashe, me zai hana gobe ya zo da nasa abin satar jarabawa?