Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?2
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Dauri ko tara ba zai kawo karshen magudin jarrabawa ba -Musa Yunusa
Dalilina shi ne ba a bin tsarin dokar kasa yadda ya kamata saboda ana iya jingine doka a bi son rai. Idan ka ga doka ta hau kan mutum a kasar nan, to marar gata ne.
Sannan kuma su jami’an tsaro da ake turawa makarantu don kula da masu zana jarrabawar ana hada kai da su da malaman ana ba su toshiyar baki su bar mutum ya ci karensa ba babbaka.
Muddin ba a daina hada kai da jami’an tsaro da malamai ana ba su na goro ba, babu yadda za a yi dalibi ya daina satar jarrabawa saboda su suke taimakawa.