Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?3
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Ba tara ko dauri ne zai kawo karshen magudin jarrabawa ba -Abdurrahman Tela
Ni a tawa fahimtar daurin ko tarar ba shi ne zai kawo karshen magudin jarrabawa ba a kasar nan.
Abin da zai kawo karshen magudin jarrabawa shi ne a kawo karshen cin hanci da rashawa. Shi ne kawai mafita. Magance cin hanci da karbar rashawa shi ne kawai mafita.
Akwai wadanda sun yi shekaru da yawa suna zana jarrabawa ba sa ci. Ka ga ko nawa mutum yake da shi zai iya kashewa wajen bayar da na goro ga malamai don ya samu ya ci. Domin wani ba ruwansa da shiga gidan yari, in dai zai ci jarrabawa shi zai iya biya.