Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?4
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Lallai dokar za ta rage yin magudin jarrabawa -Abdullahi Suleiman
Malam Abdullahi Suleiman, Hedmasta ne a Firamaren L.E.A Fulani Road, Tudun Wada, Kaduna ya bayyana ra’ayinsa kamar haka: A gaskiya dokar za ta hana ko rage yin magudin jarrabawa a kasar nan. Da ma tun farko rashin irin wannan doka ce ta sa ake yawan samun magudin jarrabawa a kowane mataki. Da ana hukuncin da ya dace da tuni an shawo kan matsalar. Amma yanzu da gwamnati ta fito da wannan tsari ko shakka babu za a samu raguwa ko share masu aikata magudin jarrabawa a kasar nan.