Shin hukuncin daurin shekara biyar ko tarar Naira dubu dari biyu zai rage magudin jarrabawa?5
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka: […]
Gwamanatin Tarayya tana yunkurin gyara a dokar jarrabawa inda take da nufin sanya hukuncin daurin shekara biyar ko tarar N250,000 kan duk dalibin da aka samu da magudin jarrabawa. Shin daurin ko tarar za su iya taimakawa wajen kawar da magudin jarrabawar. Zauren Muhawara ya ji ta bakin wasu jama’a daga sassa daban-daban, kamar haka:
Dokar ba za ta rage magudin jarrabawa ba -Abdullahi Bamalli
Abdullahi Lawal baidu (Bamalli), Malami ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) ya bayyana ra’asyinsa kamar haka: Duk da yunkurin gwamnati take na kokarin hana magudin jarrabawa hakan ba zai yiwu ba saboda tun farko ba ta dora turbar ilimi a bisa ingantacciyar hanya ba. Ana samun ilimi mai nagarta ne tun daga matakin farko watau na firamare zuwa jami’a amma a kasar nan abin ba haka yake ba dalili kenan da ya sa abubuwa suka tabarbare musamman a kan harkar ilimi. Don haka abu ne mai wahala a yanzu a ce za a samu canji duk da dokar da gwamnati ke kokarin yi a kan wannan batu.