Shin kana cikin ’yan gatan Allah a Ranar kiyama?(1)

Masallacin Bilal bn RabahGodiya ta tabbata ga Allah abin da ke cikin sammai da kasa naSa ne. Shi ne Abin godiya a Lahira, kuma Shi Mai hikima ne Mai bayar da labari. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, “Ya halicci mutuwa da rayuwa domin […]

Shin kana cikin ’yan gatan Allah a Ranar kiyama?(1)
Shin kana cikin ’yan gatan Allah a Ranar kiyama?(1)

Masallacin Bilal bn Rabah
Godiya ta tabbata ga Allah abin da ke cikin sammai da kasa naSa ne. Shi ne Abin godiya a Lahira, kuma Shi Mai hikima ne Mai bayar da labari. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, “Ya halicci mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba ku Ya ga wane ne mafi kyan aiki, kuma Shi Mabuwayi ne Mai yawan gafara.” Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, mai bushara da gargadi, kuma fitila mai haskakawa, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar tashi daga kaburbura.
Bayan haka, ya ku ’yan uwan imani! Hakika Allah Ya siffanta ranar kiyama, kuma Ya siffanta halin da mutane za su samu kansu a cikinta. Ya bayyana siffar kubutattu da ake girmamawa, don Musulmi ya yi kwadayin kasancewa cikinsu. Ya bayyana hali da siffar wadanda ake yi musu azaba da wulakanci, don Musulmi ya guji ayyukansu. Hakika Manzon Allah (SAW) a cikin wani Hadisinsa, ya bayyana nau’o’in wadansu mutum bakwai daga cikin bayin Allah, da Allah zai sanya su a inuwarSa Ya girmama su, Ya natsar da zukatansu, Ya kwantar musu da hankali a wancan rana da ake halarta. Su wane ne wadannan mutum bakwai? Wadanne abubuwa ne siffofinsu? Wannan tambaya ce mai muhimmanci. Da amsarta ta kasance majahuliya wadda Allah kawai zai kebanta da ita a cikin gaibinSa, da bai bayyana ta ba, da sai dai mu yi ta hasashe don gano yanayin wadannan mutum bakwai da irin ayyukansu, ta yadda za mu yi koyi da su mu kasance cikinsu. To amma sai Mai girman daraja, Ya siffanta mana su kyakkyawar siffantawa, Ya yi dalla-dallar bayani kansu ta bakin AnnabinSa (SAW). Sai Manzo (SAW) ya ambace su daya bayan daya, a cikin hadisin da Shaihunnan Hadisan nan biyu da Ahmad da Nisa’i suka ruwaito daga Abu Huraira (RA) cewa: “Mutum bakwai, Allah Zai sanya su a cikin inuwarSa, a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Wato shugaba adali da matashin da ya taso cikin bauta wa Allah, da mutumin da zuciyarsa ke ta’allake da masallaci, idan ya fita daga cikinsa har ya dawo gare shi. Sai kuma mutum biyu da suka so juna don Allah, suka hadu a kan haka, suka kuma rabu a kan haka, sai mutumin da ya tuna Allah yana kebe shi kadai, amma ya zubar da hawaye, da kuma mutumin da wata mace mai matsayi da kyau ta neme shi da zina, amma ya ce, ina tsoron Allah Ubangijin halitta, da kuma mutumin da ya yi sadaka, ya boye ta, ya zamo hannunsa na hagu ma bai san abin da dama ta bayar ba.”
A wannan Hadisi Manzon Allah (SAW) yana bayyana halayen wadannan mutum bakwai daga cikin Musulmi a yinin kiyama. Yana bayyana halayensu a yini Mai girma. “Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta.” (k:83:6).
Wannan yini ne mai wahalarwa da tsoratarwa, mai tsawon da bawa ke matukar bukatar wani abu daga rahamar Allah da zai kwantar masa da hankali, ya kosar da shi daga kishi, ya amintar da shi daga tsoron da yake ji. To a wannan babban yini ne- Allah Mafi karimcin masu karimci, kuma Ubangijin halitta- Zai karrama wadansu mutum bakwai daga cikin bayinSa. Sai ga shi Manzon Allah (SAW) yana siffanta mana ayyukan wadannan mutane, domin mu kwaikwayi daya daga cikinsu, kuma domin mu tsarkake ayyukanmu, mu samu wannan daraja madaukakiya, mu samu wannan karramawa mai girma, mu kubuta a ranar da yara ke zama masu furfura, ranar guje wa iyaye, ranar da uwa ke jefar da jaririnta da take shayarwa, ranar da Annabawa suke cewa a cikinta “Ya Ubangiji! Sauki! Sauki!!
Siffa ta farko daga aikin mutum bakwai din nan ita ce:
Shugaba adali: Shugaban da yake tsoron Allah game da talakawan da yake kiwo, yake daidaita kansa da su, yake tausaya musu ya ji kansu. Ya kwato hakkin wanda aka zalunta daga azzalumi, kamar yadda mazajen farko na wannan al’umma Halifofin Manzon Allah (SAW) suka aikata.
Abubakar As-Siddik (RA) ya fadi a cikin hudubarsa ta karbar halifanci kamar yadda Ibn Kasir ya ruwaito a Albidayah wan Nihayah cewa, bayan hamdala ga Allah da yabo gare Shi, ya ce: “Bayan haka, ya ku mutane! Hakika an dora min shugabancinku, alhali ba ni ne mafificinku ba. Idan na kyautata ku taimaka min, idan na munanta ku mikar da ni. Gaskiya amana ce, karya kuma ha’inci ce. Mai rauni a cikinku mai karfi ne a wurina, har sai na share masa hawaye in Allah Ya so. Mai karfi a cikinku mai rauni ne a wurina, har sai na kwato hakkin masu shi daga wurinsa in Allah Ya so. Babu mutanen da za su bar jihadi a tafarkin Allah, face Allah Ya doka musu kaskanci. Kuma mutane ba za su watsa alfasha a tsakaninsu ba, face Allah Ya mamaye su da bala’i. Ku yi min da’a, matukar ina da’a ga Allah da ManzonSa, idan na saba wa Allah da ManzonSa, ba ni da hakkin da’a, a kanku.” Wadannan su ne, kalmomin shugaba adali Abubakar As-Siddik, (Allah Ya yarda da shi, kuma Ya kara masa yarda.)
Ya ku ’yan uwa a cikin imani! Shugaba adali ba ya tsaya kan mai mulki kawai ba ne, a’a ya hada da duk wanda ke rike da wani al’amari da ya kunshi yanke shawara da jagoranci. Wani malami yana cewa, “Shugaba adali a wannan Hadisi, shi ne duk wanda ke sanya ido ko kula da wani al’amari na Musulmi.”
Na biyu shi ne: Matashin da ya tashi cikin da’a ga Allah. Wannan matashi ya rayu yana mai ibada ga Allah, mai karanta littafinSa, mai bin Sunnar ManzonSa (SAW), mai runtse ganinsa, mai tsare gabbansa daga abin da Allah Ya haramta. Ba ruwansa da giya ko kwaya ko abubuwa masu bugarwa. Shi dai ya tafiyar da lokacinsa wajen da’a ga mahaliccinsa. Abin sani Allah Ya karrama wannan matashi ne, domin ya yi yaki da son ransa, domin shi rai mai saba masa ne wajen bin Allah, amma duk da haka ya bautar da shi ga Allah. abu ne mai sauki a ga tsoho mai furfura da kwanansa ya yi kusan karewa yana ibada. Amma abu ne mai matukar wahala, a ce saurayi ya ji tsoron Allah, ya bauta maSa, a daidai lokacin da samartaka suke dibarsa, yake gabar balaga da kuruciya. Kuma wannan babbar azama ce da Allah Yake so.
Ya ’yan uwa a imani! Wannan matashi irinsa al’umma take so, don gyara makomarta da daukaka martabarta da tsare akidarta da mutuncinta da kore abokan adawarta. Matashi ne da yake rayuwa domin Allah! Matashi ne da yake gyara zuciyarsa da al’ummarsa da kasarsa.
Matasa ne da suke kaskantar da kai ga Allah, ba ruwansu da badala, masu nafilfili ne cikin dare, ba su halartar wurin batsa da nuna tsaraici, ba ruwansu da kade-kade. Ba su koshi da neman ilimi. Ba su kusantar mulhidai, su ne masu tsare tubalan addini, don haka suke da mutunci, kuma ba za su kaskanta ba.
Na uku shi ne: Mutumin da zuciyarsa ke ta’allake da masallaci, idan ya fita daga gare shi har sai ya dawo gare shi. Ya bayin Allah! Zuciya tana ta’allaka ne da abin da aka sabar mata. idan aka saba mata da da’a ga Allah da ikhlasi, sai ta ginu kan haka, ba za ta ji dadin sabanin haka ba. Idan aka saba mata da son sabo aka dauwamar da ita kan aikata haka, sai ta ta’allaka da shi. Don haka mutanen kwarai suna natsuwa ne da ambaton Allah Madaukaki. Saboda haka zukatansu suke ta’allaka da wuraren da’a, ba su jin dadi sai a wadannan wuraren, idan suka rabu da su, yanzu za ka ji suna shaukin komawa gare su. To wadannan suna daga cikin wadanda Allah Zai sanya a inuwarSa a yinin da babu inuwa sai inuwarSa.
Saboda haka ya kai bawan Allah! Ka tambayi kanka, shin zuciyarka tana ta’allake da masallaci ne, ko tana ta’allake da waninsa na daga wuraren wasanni da shagala da wargi? Wadannen wurare ne take haba-haba da shaukin zuwa? Ka sani mafificin bigire a bayan kasa, shi ne masallaci, ka nemi lada a masallaci, ka nemi shiga inuwar Allah a Ranar kiyama ta hanyar raya masallaci. Manzon Allah (SAW) cikin abin da Ibn Maja ya ruwaito daga Hadisin Abu Huraira yana cewa: “Abin da ke kankare zunubbai: shi ne cika alwala a lokacin da (taba ruwa) ke da wahala, da taka duga-dugai zuwa masallaci, da kuma jiran Sallah bayan Sallah.”