Shin kin amincewa da kudurin kafa Peace Corps da Shugaban kasa ya yi ya dace?
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin kafa rundunar Peace Corps bayan Majalisar Dokoki ta kasa ta aike masa da kudurin dokar domin ya rabbata hannu a kai. Bayan zauruka biyu na majalisar sun sun amince. Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce inda wadansu daga cikin ‘yan majalisar suke cewa za […]
A kwanakin baya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudurin kafa rundunar Peace Corps bayan Majalisar Dokoki ta kasa ta aike masa da kudurin dokar domin ya rabbata hannu a kai. Bayan zauruka biyu na majalisar sun sun amince. Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce inda wadansu daga cikin ‘yan majalisar suke cewa za su yi gaban kansu idan har Shugaban kasa ya ki amincewa da dokar. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane, kuma ga abin da suke cewa:
Ina goyon bayan Shugaba Buhari – Muhammad Warshu Adam Matankari
Daga Abba Ɗalibi, Legas
Muhammad Warshu Adam Matankari: “Ina goyon bayan kin sanya hannu da Shugaba Buhari ya yi na tabbatar da hukumar ‘Peace Corps’ bisa dalilan da Shugaban kasa ya bayar na cewa aikin da suke so a ba su dama can aiki ne na jami’an tsaro da kasar nan ke da su a baya don haka ba zai ba da ma’ana ba idan aka kirkiro sabuwar hukuma a ba ta aikin da wata hukuma ke yi a baya. Sannan akwai maganar da Shugaba Buhari ya yi ta rashin isassun kudin gudanar da wannan hukuma, kuma abu ne da muka sani don haka kamata ya yi a kara wa jami’an da muke da su a baya kaimi a inganta su a kyautata aikinsu da yawan jami’ansu hakan ka iya kyautata halin tsaro kuma a haka za a samu karin guraben ayyukan yi kamar yadda ake fata idan an kafa rundunar ta Peace Corps don haka ra’ayina abin da Shugaban kasa ya yi daidai ne.”
Buhari ya yi daidai – Mustapha Muktar
Lubabatu I. Garba, Kano
Mustapha Muktar: “Ni a ra’ayina wannan abu da Shugaban kasa Muhamamdu Buahri ya yi ya yi daidai lura da yanayin tattalin arzikin kasa da ya tabarbare musamman ganin kwanan nan aka fito daga masassarar tattalin arziki da kasar ta samu kanta a ciki. Kin ga idan aka samar da wannan hukuma sai an yi mata kasafin kudi nata na kanta, to da a yi wannan ai gara a dauki kudin a yi amfani da su wajen yin wasu ayyuka da suka shafi al’umma. Haka kuma ina ganin irin kudin da gwamnati ke kashewa a harkar tsaro sun yi yawa, maimakon a rika kashe wadannan kudade kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali ko ta yi amfani da kudin wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar nan. Idan aka samu rayuwar al’umma ta kyautata to ba za a samu mai laifi ba ballantana jami’an tsaron su yi wani aiki. Muna da wadatattun jami’an tsaro a kasar nan. Su kansu Peace Corps din idan an dauke su ba a san ma aikin da za su yi takamaimai ba.”
Hakan ya yi daidai don a tsabtace harkar tsaro – Nasiru Muhammad
Lubabatu I. Garba, Kano
Nasiru Muhammad: “A ra’ayina Shugaban kasa ya yi daidai da ya ki amincewa da wannan kudiri, musamman idan aka yi la’akari da halin rashin tsaro da kasar nan ke ciki. Idan an duba yadda aka dauki ma’aikatan ba gwamnati ce ta yi aikin ba, babu wani tantancewa haka kawai aka dauki mutane kara-zube. Ba a san ko su wane ne ba. watakila ma a je a dauki mutanen da za su iya kawo wa kasa matsala ko su zama masu tona asirin gwamnati. Kamata ya yi gwamnati ce za ta dauki duk ma’aikatan wata hukumar tsaro tare da sanya wasu ka’idoji, kamar yadda ake bi a wajen daukar ’yan sanda. Kin ga tun daga matakin farko sai mai unguwa ya sanya wa mutum hannu, sannan sai mutum ya samu wani jami’in dan sanda ko soja wanda zai sanya hannu tare da bayar da kwafin katin shaidarsa da lambar wayarsa da duk wasu bayanai masu muhimmanci game da shi. To kin ga babu jami’in tsaron da zai sanya hannu a kan mutumin da bai sani ba.”
Ina goyon bayan Shugaban kasa – Alhaji Mu’azu Ado Garu
Umar Akilu Majeri, Dutse
Alhaji Mu’azu Ado Garu: “Ni wallahi ina goyon bayan Shugaban kasa Buhari a kan kin sa wa dokar hannu, ya yi daidai domin in da da ni zai yi shawara, ba za a sa wa dokar hannu ba saboda ba su da wani amfani a wajen ’yan Najeriya. Domin babu wata kasa a tarihin duniya da ta taba daukar tsaron kasar ta damka a hannun wadansu mutane ko ta bai wa wata kungiya. A ganina damka tsaro ko sa su cikin jerin jami’an tsaro na da hadari saboda su kungiya ce kuma ba a karkashin kowa suke ba. Don haka babu bukatar a ce an ba su gashin kansu kamar sauran jami’an tsaro.
Shugaban kasa Buhari ya yi daidai – Abubakar Ahmed Garba
Umar Akilu Majeri, Dutse
Abubakar Ahmed Garba: “A Najeriya ba ma bukatar karin wadansu jami’an tsaro, wadanda muke da su sun ishe mu domin muna da ’yan sanda muna da sojoji da kwastam da sauransu. Yanzu abin da Najeriya take bukata ba karin hukumomin tsaro ba ne, bukatarmu a samar da harkokin inganta rayuwar al’umma. Saboda haka kin amincewar Shugaban kasa a kan ya sa wa dokar hannu ya yi daidai. Kuma ni a ra’ayina wadannan jami’ai na Peace Corps ba su da wani amfani a wajen al’ummar kasar nan.”
Samar da hukukmar zai taimaka – Alhassan Muhammad Hassan
Abbas Ɗalibi, Abekuta
Alhassan Muhammad Hassan: “A gaskiya wannan tsari na Peace Corps alheri ne ga al’ummar kasa domin duk abin da aka ce zai inganta tsaro abin a yi maraba da shi ne, kuma cin moriyar abin shi ne yadda za a samar wa matasa guraben aikin yi, ka ga idan aka assasa wannan abin matasa da yawa za su samu aikin yi ka ga hakan abu ne mai kyau don haka ya kamata Shugaban kasa ya sanya hannu, wannan shi ne ra’ayina domin ba a san irin salon da wannan runduna za ta zo da shi ba wajen inganta tsaro saboda hukumomin da muke da su na tsaro a baya suna da alamun rauni in ka yi la’akari da abubuwan da suke faruwa a kasar nan a yanzu. Don haka muddin sanya wa wannan doka hannu ba zai tabarbara tattalin arzikin kasar ba kamar yadda Shugaban kasa ya ce, babu kudi to ya kamata ya sanya hannu, wannan shi ne ra’ayina.”