Shin kishi ne ko rashin imani?

Mafi akasarin mata sun dauki kishi da zafi, saboda zafin kishi mata da dama sun hallaka kishiyoyinsu da ‘ya’yan kishiyoyinsu, kai wasu ma har mazajen sun kashe duk sabo da zafin kishi. Wata macen da ka yi mata kishiya gwanda ta kashe ka ko kuma ita ta bar gidan; wata kuwa da zarar ka yi […]

Shin kishi ne ko rashin imani?

Mafi akasarin mata sun dauki kishi da zafi, saboda zafin kishi mata da dama sun hallaka kishiyoyinsu da ‘ya’yan kishiyoyinsu, kai wasu ma har mazajen sun kashe duk sabo da zafin kishi. Wata macen da ka yi mata kishiya gwanda ta kashe ka ko kuma ita ta bar gidan; wata kuwa da zarar ka yi auren shi ke nan ka yi bankwana da kwanciyar hankali sai dai tunani iri-iri daga wajen mata na hallakawa ko illatawa ga ‘ya’yan kishiyoyinsu, saboda bakin kishi. 

Akwai wadanda suka yi jefe-jefe na ‘ya’yansu cikin rijiya, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar ‘ya’yan, akwai wata mata da aka taba ba ni labarinta. iIta kuma ‘ya’yan kishiyarta tagwaye sabuwar haihuwa ta dauka ta zuba a garwar ruwan zafi suka mutu. Sannan akwai wata yarinya da ta ba ni labarin abin da kishiyar babarta ta  yi mata tana karama, har sai da na kusa zubar da hawaye, domin da kwananta ya kare da tuni da mutu a lokacin, irin wannan rashin imani ba za su lissafu ba. Kai mata me kuke nema ne a rayuwarku ta duniya? Haukatar da kishiya ko hallaka miji ba ku dauke shi a komai ba. 

A wannan lamari ba abin da yake ba ni haushi illa rashin hukunta irin wadannan mata masu bushewar zuciya. Rashin hukunta su ne kuma ke kara sa a samu wasu matan su aikata. 

Ya kamata duk wacce ta kashe dan kishiyarta a kashe ta, idan kika karya shi a karya ki, idan kika yanke masa harshe a yanke naki, idan kika kona shi a kona ki, idan kika cilla shi rijiya a cilla ki. idan kika ba shi shinkafar bera ke ma a tilasta miki ki ci, idan kika dura masa kalanzir  ke ma a dura miki, idan kaka kashe mijinki a kashe ki. To wallahi da an dan samu saukin wannan rashin imani. 

Muna fatan gwamnati za ta yi abin da ya dace a kan wannan al’amari, amma in har wance za ta kashe kishiyarta ta tsira, wance ta kashe mijinta ta tsira, wance ta kwara wa kishiyarta ruwan zafi ta tsira, ko ta kone ta tsira, to irin wannan ta’addanci ba zai kare ba daga wajen mata. Ya Allah Ka azurta mu da mata nagari. ’Yan uwa na matasa ku ce amin.

Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688/09073801967 naseer ya’aky <[email protected]