Shin ko akwai bambanci tsakanin bashi da rance?

Kalmomin nan biyu, ‘Bashi’ da ‘Rance’ suna da ma’anoni daban-daban, a wani wuroin kuma ana ganin kamar ma’anarsu daya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko akwai bambanci tsakanin kalmomin kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Akwai bambanci – Mukhtar Ahmad Musa Kutama, a Kalaba Mukhtar Ahmad […]

Shin ko akwai bambanci tsakanin bashi da rance?
Shin ko akwai bambanci tsakanin bashi da rance?

Kalmomin nan biyu, ‘Bashi’ da ‘Rance’ suna da ma’anoni daban-daban, a wani wuroin kuma ana ganin kamar ma’anarsu daya. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko akwai bambanci tsakanin kalmomin kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Akwai bambanci – Mukhtar Ahmad

Musa Kutama, a Kalaba

Mukhtar Ahmad Abubakar: “Ba daya ba ne, akwai bambanci tsakanin su. Shi bashi ana karbarsa ne bisa sharadin sai ranar da Allah Ya huwace za a biya ko kuma sai nan da wani sharadi za a biya. Rance kuwa wani abu ne da ake karba sai nan da wani takaitaccen lokaci za a dawo da shi. Ma’ana rance shi ba a dadewa, ba wani abu ba ne da zai dauki lokaci amma bashi abu ne wanda yake daukar lokaci kafin a biya.”

Ma’anarsu ta bambanta – Muhammad Akilu

Musa Kutama, a Kalaba

Muhammad Akilu: “Akwai bambanci, ba daya ba ne rance da bashi. Shi ba shi, ana yinsa ne tsakanin wadanda suka hada hulda ta kasuwanci ko wata mu’amala bisa yarda da amince wa juna, yayin da shi kuma rance wani abu ne na wani dan lokaci da ake yi wa ajali, saboda wanda ya karbi rance yana ganin ya fi karfin abun ne a wurin wanda ya karba. Rance ana iya karbarsa ma tun kafin ya fara kasuwanci idan har ma shi din ne zai yi. Idan kuma ma wata bukata ce ta taso wa mutum, zai iya karbar rance ya biya bukatarsa zuwa wani takaitaccen lokaci, ya mayar da abun nan da ya ranta. Don haka akwai matukar bambanci tsakaninsu.”

Sun bambanta da lokaci – Baba S.

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Baba S. Bokin Ofisa: “A ganina, bambancin da ke akwai tsakanin rance da bashi shi ne, shi bashi kafin ka dauke shi dole ne ka dauki wani wa’adi; in ma a rubuce ko da baki, sabanin rance da ba lalle ba ne ka rubuta yaushe za ka kawo. Kuma abin kara dubawa shi ne, rance shi kakan iya karbarsa ne nan take da nufin ba zai dauki lokaci ba, ba kuma tare da ka ce ga lokacin da za ka kawo shi ba, don mayarwa ga wanda ka karba a wurinsa.”

danjuma ne da danjummai – Alhaji Ibrahim

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Alhaji Ibrahim Ziyamis: “A ganina, da bashi da rance tamkar danjuma ne da danjummai, domin kuwa dukkaninsu abu guda ne. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, shi ba shi akan ba da shi ne da daukar lokacin da za ka biya shi; in ma a banki ne ko kuma a wurin wani mutum. To haka nan shi ma rance, akan iya karba ne da wani wa’adin biya kamar yadda yake a ka’idance. Don haka ni a ganina lalle da bashi da rance kusan dukkaninsu abu guda ne akan karba ko dauka ne da zimmar za ka biya shi wanda ka karba ko ka dauka daga gare shi, tunda ba kyauta ne aka ba ka ba. Shi ya sa na ce dukkansu abu guda ne.”

Kalmomin sun bambanta – Murtala Jangebe

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Murtala Jangebe: “Ni a ra’ayina, akwai banbanci tsakanin rance da bashi. Idan aka ce bashi, ana nufin ka bai wa mutum wani abin da yake bukata zuwa wani kayyadadden lokaci kamar kudi ko kaya, wanda addini ya yarda kafin ka ba shi to a rubuta a takarda, cewa ka amsa kuma za ka maido da shi zuwa wani lokaci mai tsawo ko gajere. Wannan shi ne bashi, amma rance shi ne irin abin da ’yan kasuwa suke yi kamar su ce ba ni kaza ko ranta mani kaza zan maida maka. Idan ka zauna wajen ’yan kasuwa za ka ji wani ya ce ranta mani miliyan biyu ko biyar, wannan shi ne rance.”

Babu bambanci tsakaninsu – Muhammad Manaja

Shu’aibu Ibrahim, a Gusau

Muhammad Manaja: “Ni a ra’ayina, babu bambanci tsakanin bashi da rance. Idan aka ce bashi, kana nufin a taimaka maka da wani abu zuwa wani lokaci. Haka kuma abin yake ga wanda ya ce ka ba shi rance, shi ma yana nufin ka ba shi abin da yake nema daga gare ka zuwa wani lokaci mai tsawo ko gajere. Don haka da bashi da rance dukkansu sunansu guda kuma manufarsu guda, babu bambanci.”