Shin ko kwalliya ta biya kudin sabulu kan rawar da Najeriya ta taka a wasannin Olympics a kasar Brazil?
A watan jiya ne aka kammala wasannin Olympics a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. Wakilanmu sun tattaro mana ra’ayoyin jama’a dangane da rawar da kasar nan ta taka lokacin gasar. Ba mu yi kokari ba– Kabiru Mai Adashi Daga Hussaini Isah, Jos Alhaji Kabiru Mai Adashi: “A gaskiya ni a ganina ’yan wasan […]
A watan jiya ne aka kammala wasannin Olympics a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. Wakilanmu sun tattaro mana ra’ayoyin jama’a dangane da rawar da kasar nan ta taka lokacin gasar.
Ba mu yi kokari ba– Kabiru Mai Adashi
Daga Hussaini Isah, Jos
Alhaji Kabiru Mai Adashi: “A gaskiya ni a ganina ’yan wasan Najeriya ba su yi kokari ba, a wajen wasannin Olympics da aka gudanar a bana. Domin gwamnatin Najeriya ta samu matsaloli da dama kan horar da ’yan wasan da suka wakilci kasar nan a wajen wasannin. An sa son zuciya a ciki, ba a debi ’yan wasan da ya kamata a deba ba, kudin abincin ’yan wasan da kudin masaukinsu ma ya gagara. Saboda haka ba su taka rawar gani ba a wajen wadannan wasanni.”
Sun taka rawar gani– Salisu Mai Kananzir
Daga Hussaini Isah, Jos
Alhaji Salisu Adamu Mai Kananzir: “A gaskiya kwalliya ta biya kudin sabulu game da rawar da ’yan wasan Najeriya suka taka a wajen wasannin Olympics da aka gudanar kwanakin baya a kasar Brazil, musamman a bangaren wasan kwallon kafa. Don haka ni a ganina Najeriya ta yi kokari a wajen wasannin.”
Mun yi kokari– Alhaji Shehu
Daga Abbas dalibi, Abeokuta
Alhaji Shehu Usman (Shugaban kugiyar magoya bayan kulub ɗin Manchester United a Najeriya): “Eh, alhamdulillahi mu da muke kula da yanayin da kwallon kafa ke tafiya a duniya ganin yadda abin ya faru, amma duk da haka ’yan wasan Najeriya sun zo na uku abin a yaba ne. Musamman idan aka yi la’akari da yadda suka makale a Amurka jim kadan gabanin fara wasan.”
Mun taka rawar gani– Adam B
Daga Abbas dalibi, Legas
Adam B Adam: “A gaskiya ’yan wasan Najeriya sun taka rawar gani a gasar domin duk abin da aka ce ya kunshi kasashe goma sha, sai ga shi Najeriya ta zo ta uku a fagen kwallon kafa. Duk da matsalolin da ’yan wasan suka fuskanta, to ai ka ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai dai gazawar da gwamnati ta yi a yi kokari a gyara nan gaba domin an san da za a yi gasar amma har sai da ya rage ’yan kwanaki ba a shirya masu ba, a haka ’yan wasan suka makale a kasar Amurka.”
Najeriya ta yi kokari– Bashir Mali
Daga Hamza Aliyu, Bauchi
Alhaji Bashir Mali: “Hakika Najeriya ta yi kokari sosai kuma ta taka rawar gani a gasar duk da cewa ba mu samu abubuwan da muke bukata ba, amma muna godiya ga Allah bisa yadda aka kammala wasan cikin kwanciyar hankali da lumana. Tabbas ’yan wasan sun taka rawar gani kuma a fahimtata sun fi kasashe da dama kokari mun dawo gida da tagulla ne sabanin abin da muka tsammaci za mu samu a lokacin gasar.”
Kwalliya ta biya kudin sabulu– Bala Hassan
Daga Hamza Aliyu,Bauchi
Alhaji Bala Hassan: “Najeriya ta taka rawar gani sosai a wasannin Olympics kuma tabbas kwalliya ta biya kudin sabulu. Muna fatar za a ci gaba da ba da goyon baya ga ’yan wasan tunda yanzu mafi yawansu matasa ne masu jini a jika. Wajibi ne masu horar da ’yan wasan Najeriya su dage sosai domin ganin kasar ta fita kunya tunda yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ne ke mulki.”