Shin ko ya dace gwamnati ta yi musayar ’yan matan Chibok da ’yan Boko Haram?
A farkon makon nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana aniyyarsa na tattaunawa da kungiyar Boko Haram don kubutar da ‘yan matan Chibok, bayan wani faifan bidiyon da kungiyar ta fitar kwanakin baya, wanda a ciki take bukatar a yi musayar su da dakarun Boko Haram da suke tsare. Ga abin da wakilanmu […]
A farkon makon nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana aniyyarsa na tattaunawa da kungiyar Boko Haram don kubutar da ‘yan matan Chibok, bayan wani faifan bidiyon da kungiyar ta fitar kwanakin baya, wanda a ciki take bukatar a yi musayar su da dakarun Boko Haram da suke tsare. Ga abin da wakilanmu suka tattaro mana dangane hakan:
Ya dace a yi musayar– Ilyasu Angonta
Daga Kabir S/Kuka, Katsina
Ilyasu Angonta: “Ina ganin idan akwai damar yin haka, kamar yadda kungiyar Boko Haram ta yi alkawari in an sako su, su kuma za su bayar da wadannan ‘yan mata, to ya dace ayi hakan. Babu abin da ya fi zaman lafiya. Ya dace a tattaunawa don samun shawara ta kawo maslaha.”
Ina goyon bayan musayar – Bello Sabon Dawa
Daga Kabir S/Kuka a Katsina
Bello Sabon Dawa: “Ni ina ganin ba kawai a saki mutanensu ba ko su su sako namu ba. Aa’a,yana da kyau a zauna da su farko don tattaunawa wanda hakan zai bayar da damar sanin ko su wanene su? Su wake tare da su? Hakan zai kawo karshen wadannan tashe-tashen hankulan da kuma samun sahihiyar hanyar zaman lafiya a kasa.”
Ya dace a yi sulhun – Alhaji Huseini
Daga John D Wada, Lafiya
Alhaji Huseini Mohammed: “Ni dai ina ganin ya kamata Gwamnatin Tarayya ta amince ta yi sulhu da wadannan ’yan Boko Haram. Amma shawara da zan ba wa gwamnati shi ne ta tabbatar ’yan kungiyar din sun fara sako ’yan matan kafin ayi wannan sulhun. Kada tayi garajen sako mambobinsu da ke tsare. Amma ta gaya musu su sako matan kafin a sako musu mambobin. Idan sun mika kai sai gwamnati ta duba ta yi musu afuwa don su ma ’yan Najeriya ne kamar kowa don a samu zaman lafiya.”
Bai dace a yi musayar ba – Usman Adamu
Daga John D Wada, Lafiya
Alhaji Usman Adamu Doya Hamsin: “A nawa ra’ayin bai dace Gwamantin Tarayya ta amince da wannan bukatar da ’yan Boko Haram ba. Don har yanzu ba a tabbatar da su wanene ainihin shugabannin kungiyar ba. Shawarata ga gwamnati shi ne kada ta yarda tayi musayar mambobin Boko Haram da matan Chibok kamar yadda ’yan kungiyar ke bukata. Maimakon haka ta ci gaba da kokari da take yi na ceto matan har lokacin da Allah zai ba ta nasarar dakile ayyukan wadannan miyagun mutane kwata-kwata a kasar nan baki daya kamar yadda ta fara.”
Kada a yi musayar – Alhaji Ado
Daga Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Alhaji Ado Sulaiman (Sarkin Hausawan Akinyele): “A gaskiya wannan musayar fursunoni ‘yan Boko Haram da ‘yan matan Chibok ba ta da amfani a yanzu. Tun kafin matsalar tayi nisa ya kamata a duba yiwuwar haka ba yanzu da bakin alkalami ya bushe ba. Ina so ka lura cewa an riga an gurbata rayuwar wadannan ‘yan mata wanda daya daga cikinsu ma da aka kubutar da ita ta furta da bakinta cewa, ta fi so ta koma wurin tsohon mijinta, dan Boko Haram.”
Bai dace a yi musayar ba – Alhaji Salisu
Daga Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Alhaji Salisu dan Arewa: “Bai kamata a yi wata musaya ba domin idan aka kuskura aka sallamo ‘yan Boko Haram da ke tsare, to suna iya zama wata babbar matsala kamata ya yi iyayen wadannan ‘yan mata su yi hakuri su mika al’amarin nan baki daya ga Allah. Ban ga amfanin yin wannan musayar ‘yan Boko Haram da ‘yan matan Chibok ba. Kamata ya yi a kyale su a hannunsu idan kuma ya kama a rasa su ne to gara a rasa duka bangarorin biyu.”