Shin muna da Hatsi a rumbunan adana abinci na kasa kuwa?

Rabon abinci na kofi daya daga rumbun ajiya ba zai magance matsalar da ake ciki ba na karancin abinci.

Shin muna da Hatsi a rumbunan adana abinci na kasa kuwa?

Ministan Noma; Sanata Abubakar Kyari

Wannan ita ce tambayar da aka yi wa Ministan Noma da Samar da Abinci na Kasa, Sanata Abubakar Kyari a yayin da ya amsar kiran Kwamtin hadin gwiwa na Majalisar Dattijai da na Wakilai kan tattalin arziki a zaman su da ya halarta a bisa gayyatarsu.

Kwararru a harkar noma sun dade suna nuna shakkunsu kan matsayi da kuma yadda ake tafiyar da tsari da kuma matsayin da rumbunan adana abincin na kasa suke ciki la’akari da irin hadarin da ke cikin samun karancin abinci ko kuma rashinsa gaba daya.

Tun lokacin annobar cutar Kwarona da irin tasirin da ta yi kan rayuwar jama’a na koma baya da fukoki da dama a rayuwar yau da kullum da dan Nijeriya musamman tattalin arziki da kasuwanci da kuma harkar noma sakamakon rufekan iyakoki na kasa da kasa, wanda ya haifar da tsadar abinci mai alaka da karancinsa a rumbun ajiya na kasa, ya sa tararrabi a zukatan mutane kan wannan lamari.

Nijeriya na da rumbunan ajiyar hatsi guda 33 da kowannnensu ke iya daukar hatsi Metrik Tan miliyan 1 da 300,000.

Sai dai 19 daga cikin wadannan rumbunan an bayar da su haya ga ‘yan kasuwa a inda za su yi amfani da su na tsawon wasu shekaru da bai bayyan ba.

Ma’aikatarsa ba ta kuma bayar da cikakken bayanin yawan hatsin da ta ke ajiye a rumbunan ba saboda bayyani ne na sirrin kasa.

A makonnin da suka gabata ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu sakamakon matsin lamba da ‘yan majalisar kasa da kuma sauran ‘yan Nijeriya ya bayar da umarnin da fito da hatsi daga rumbunan adana hatsin na Gwamnatin Tarayya domin a rage radadin zafin da ake ciki a kasar na karancin abincin da kuma hauhawar farashinsa.

Kan wannan lamari ne ‘yan majalisar suka tambayi ministan, shin ko da akwai hatsin kuwa da kuma halin da rumbun ajiyar ke ciki da kuma wasu batutuwa, inda ministan ya ce musu da akwai hatsin kuma ba kamar yadda wasu ke fargaba ba, yana da yawan da zai kau da shakku.

Kafin ganawar ta su ce Ministan ya sanar da fito da Tan 42,000 daga rumbunan ajiyar hatsin kamar yadda shugaban kasa ya bayar umarni, yana mai cewa yin hakan wani babban mataki ne a yunkurin da gwamnatin ke yi na magance matsalar karancin abinci da kuma tsadarsa a cikin kasa.

Sai dai Ministan bai fadi ko hatsin da za a fito da shi gero ne ko dawa ko masara ko kuma shinkafa ko kuma alkama ce kuma daga wanne rumbun ajiyar cikin rumbunanta da ke wurare daban-daban na kasa.

“Fito da wannan hatsi zai taimaka wajen samun wadatar abincin a kasuwa wanda hakan zai sa a samu faduwar farashinsa, kuma zai kai ga samun sauki ga ‘yan Njeriya da iyalansu da ke ta faman kokarin neman na kai wa bakin salati” inji shi.

Kawo zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani abin ku-zo-ku-gani dangane da fito da hatsin da kuma tasirin haka a zahiri, musamman kan hakikanin yadda za a fito da hatsn da rarraba shi ga jama’a da ke daukin ya zo gare su.

Hakan ya sa ake rade-radin cewa babu ma hatsin. Sai dai a cewar Ministan, za a ba Hukumar Bayar da Agaji ta NEMA hatsin domin su suke da sahihin sunayen wadanda suka fi bukatarsa a cikin al’umma a matsayinsu na fukara’u wanda suka fi kowa talauci.

“Su suka san inda aka fi bukatar hatsin nan, su suke da tsarin safararsa da wuren ajiyarsa kafin su rarraab shi ga talakawa.

“Tuni muka soma aiki da su kanhaka domin mun bukaci da su ba mu tsarin yadda za su gudanar da aikinsu, mu kuma sai mu hanzarta fito da hatsin mu kuma danka musu” in ji Ministan.

Yayin da yake tofa albarkacin baikinsa kan lamarin, Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa AFAN Kabiru Ibrahim ya ce, da sauran rina a kaba, domin rabon abinci na ‘Kwaf daya’ daga rumbun ajiya na gwamnati ba zai magance matsalar da ake ciki ba na karancin abinci ba a kasar nan an dindindin.

Ya ce dole sai Gwamnatin Tarayya ta kakkafa manya-manyan wuraren ajiye abincin yadda ya kamata a yankunan kasar nan guda shida, ta haka ne za a shawo kan matsalar baki dayanta.

Hakan ma idan ta yi sai ta yi masa ginshikai manya-manya na samar da abincin don ajiya da adanawayadda ya kamata da sarrafa shi da rarraba shi da kuma yadda jama’a za su yi amfani da shi.

“Amma kuma babban ginshikin kar ta tsaya da rabon kayan abinci na lokaci guda kawai, gwamnati ta tallafa wa manoma da a yanzu shine ta samar da tsaron da za su iya koma wa garuwansu da kauyukansu su ci-gaba da nomansu cikin kwanciyar hankali.

“Sannan ta samar da kimiyya da kuma fasahar da za sa a samar da ingancin amafanin gona da dabarun noman na zamani da kuma dabarun kasuwancin kayan giona na zamani” in ji shi.

Yanzu dai an sa wa gwamnati ido kan yadda za yi wannan rabo da fatan ganin ba za a yi irin rabon tsohuwar ministar Buhari ta jinkai ta yi na tallafin Kwarona da kuma fatan sababbin dabarun kawar da talauci, yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja