Shin murkushe kashe-kashen rayuka zai kawo masu zuba jari kasar nan?
Salam, Edita don Allah ka ba ni dama na yi tsokaci dangane da canjin gwamnatin da aka samu a Najeriya ganin yadda an dade ana zaman rashin kwanciyar hankali. Tabbas rashin zaman lafiya ya kawo rashin shigowar baki daga kasashan duniya to amma yanzu gashi an sami canji wanda mu talakawa muke sa rai dace […]
Salam, Edita don Allah ka ba ni dama na yi tsokaci dangane da canjin gwamnatin da aka samu a Najeriya ganin yadda an dade ana zaman rashin kwanciyar hankali. Tabbas rashin zaman lafiya ya kawo rashin shigowar baki daga kasashan duniya to amma yanzu gashi an sami canji wanda mu talakawa muke sa rai dace wa zaman lafiya zai kankama. Abin tanbaya ko bakin da suke a kasashan duniya daga ciki har da Turawa za su dawo Najeriya domin zuba jarinsu?
Kira ga ’yan Najeriya
Assalamu alaikum Edita, tare da fatan kana lafiya. Bayan haka ina so ka ba ni dama na yi kira ga ’yan uwana ’yan Najeria akan ta ya Janar Muhammadu Buhari addu’a Allah Ya ba shi ikon cika alkawarin da ya dauka wajen yakin neman zabe. Bayan haka ina kira ga jama’a da su yawaita alkhairi komai kankantansa, domin samun tsira gobe kiyama.
Daga Nana Fiddausi Abdullahi da Aishat Ibrahim Salihu, 2348136502319.
Kira ga gwamnonin Najeriya
Salam, gwamnonin Najeriya mun ji kunyi zaben shugabanku. Hakika wannan ba zai taba cire ku daga tudun mun tsira ba, har sai kun biyawa al’ummarku bukatunsu domin haka ne kawai zai sa ku cire mana kitse daga wuta.
Daga Hafizu Balarabe Gusau, 07035304499.
Kira ga Isa Yududa
Assalamu alaikum, Editan Aminiya ina so ka ba ni dama na yi kira ga gwamnan Jihar Bauchi mai barin gado wato Malam Isa Yuguda, cewa ya yi wa Allah da manzonsa ya biya ma’aikatan jihar albashin ko za su kawo karshen yajin aikin da yanzu haka ya gurgunta al’amura a jihar. Yanzu haka an rufe
makarantu da asibitoci dama kotuna da sauran wuraren amfanin jama’a. Yau dai komai ya tsaya tsak a jihar a sakamakon wannan yajin aiki da ya shiga mako na biyu domin a gaskiya ba daidai ba ne gwamnati tayi watsi da mutane a bar ma’aikata su shiga yajin aiki. dalibai masu karban kudin tallafin karatu wato scholarship sun fara shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga a Bauchi akan kin biyansu kudin su da gwamnati ta yi. Haba gwamna Yuguda ko ka fi so a yi rabuwan dutse hannun riga ne kai da mutanen Bauchi kowa yasan da cewa kafa karba kudi daga Gwamnatin Tarayya, amma ka ki biyan ma’aikata hakkin su.
A gaskiya ma’aikata da ’yan fensho suna cikin mummunan yanayi yau kusan wata 22, amma babu albashi babu dalilinsa a Jihar Bauchi. Gaskiya nikan inaga gwamnatin PDP mai barin gado tana so ne ta gadar wa gwamnatin APC, matsaloli a jihar, domin yau idan ka dubi matsalolin kasan an shirya gadan zare ne ga Gwamna mai jiran gado wato Barista M.A Abubakar, ga matsalan albashin watanni biyu ga matsalan ’yan fensho ga matsalan kudin masu sharan titi, ina kira ga gwamnatin APC, da cewa ya zamo wajibi ta binciki wannan gwamnati mai barin gado.
Daga Ahmadu Manager Bauchi, 08065189242.
Matasan Jihar Kano da miyagun kwayoyi
Ba komai ke kara ta’azzara ta’ammali da miyagun kwayoyi ga matasan Jihar Kano ba, illa rashin ayyukkan yi da ya yi ma matasan jihar katutu. domin haka ya kyautu hukumomin jihar su mike tsaye wajen samar ma matasan hanyoyin dogaro da kai.
Daga Abdulmalik Saidu Gusau, 08069807496.
Kira ga rundunar ‘yan sandar kasar Nijar
Assalamu alaikum. A gaskiya matakin da rundunar ‘yan sandar kasar Nijar suka dauka na kama dan gwagwarmayar nan wato Malam Moussa Tchangari dangane da wallafa wani rahoto akan korar mazauna tafkin Chadi da gwamnatin Nijar ta yi. Gaskiya wannan ba karamin kuskure ba ne da kuma take hakkin ‘yancin dan Adam na fadin albarkacin bakinsa, don haka muna kira ga gwamnatin Nijar, akan cewa ta gaggauta sakin Malam Moussa daga inda ake tsare da shi matukar gwamnatin na bukatar samun zaman lafiya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasashen duniya.
Daga Kwamared Nura Bello Daraja Kaset Gusau, 08032558025.
Kira ga Gwamnatin Jihar Yobe
Assalamu alaikum Aminiya, ku ba ni dama na yi kira ga gwamnatinmu ta Jihar Yobe dangane da kasafin kudin wannan shekara da ta gabatar. Hakika mun ga yadda aka kasafta kudin cikin tsari mai kyau. Don haka muke fatan za’a aiwatar da wadannan biliyoyin yadda ya dace ta yadda zai amfani Talakawan Jihar Yobe bawai wasu tsiraru ba a shekarun baya. Daga karshe nake addu’ar Allah Ya ja zamanin Jihar Yobe cikin ci gaba, walwala da kwanciyar hankali.
Daga Usman bin-Affan Damaturu, Jihar Yobe