Shin nagartar dan takara ya kamata jama’a su duba lokacin zabe ko jam’iyya?
Gobe Asabar ce jama’a za su fita domin kada kuri’ar zaben gwamnoni da wakilan majalisun dokoki na jihohi. A lokuta da dama, akan samu muhawara tsakanin mutane kan cewa a rika duba mutane kafin a zabe su kamar yadda aka samu ’ya’yan Jam’iyyar PRP da suka lashe zaben Majalisar Wakilai a Jihar Bauchi, wadansu kuma […]
Gobe Asabar ce jama’a za su fita domin kada kuri’ar zaben gwamnoni da wakilan majalisun dokoki na jihohi. A lokuta da dama, akan samu muhawara tsakanin mutane kan cewa a rika duba mutane kafin a zabe su kamar yadda aka samu ’ya’yan Jam’iyyar PRP da suka lashe zaben Majalisar Wakilai a Jihar Bauchi, wadansu kuma suke tunanin ai idan ina jam’iyya kaza, to duk wanda ta tsayar shi zan zaba. Wannan ne ya sa wakilanmu suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane, kuma ga abin da suke fada:
Dan takara ya kamata a duba tunda jam’iyyunmu ba su ginu kan akida ba– Adam Isa Wali
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Adam Isa: “Magana ta gaskiya ita ce siyasar kasashen Afirka ta ginu ne a kan harkar rashin manufofi saboda rashin akida ta jam’iyya tare da gurbacewar zukatan ’yan siyasa. A kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, siyasar jam’iyya da na akida su suka fi tasiri, saboda daidaituwar zukatar al’umma da ginuwa a kan akida da kuma bin manufofin jam’iyya. Shi ya sa a can jam’iyya ke da tasiri matuka idan muka kwatanta da kasarmu Najeriya. Shi ya sa ma dan kasa na da hurumin fitowa takara ko da ba a tutan wata jam’iyya ba. Amma a Najeriya babu wannan.”
Wasu na fakewa da jam’iyya ce – Abdullahi Hakantake Suleja
Daga Adam Umar, Abuja
Alhaji Abdullahi Hakantake Suleja: “Dan takara ya kamata a duba ba jam’iyya ba. Saboda akwai mutanen da ba na kwarai ba da dama da ke fakewa da farin jini ko karfin jam’iyya su yi takara a karkashinta alhali ba al’umma ce a zukatansu ba. To idan aka yi nazari a kan dan takara ka ga an duba cancanta ke nan. Hakan zai tilasta wa su kansu jam’iyyu su tabbatar sun zabi mutane nagari a matsayin ’yan takararsu maimakon kama-karya da suke yi da kuma rage musu girman kai a kan sauran jam’iyyu da ke da manufofi na kirki da jagorori nagari.”
A siyasance dan takara nake dubawa – Hauwa Salisu
Musa Muhammad Kutama, Kalaba
Hauwa’u Salisu: “A siyasance dan takara za a duba ba jam’iyya ba domin idan dan takara ya fito a jam’iyyar da ba ta da farin jini ko magoya baya, farin jininsa da kaunar da jama’a suke yi masa zai iya taimakonsa ya samu nasara a zabe. Amma idan aka ce za a duba jam’iyya, wannan babu wani taimako da zai yi.”
Ya kamata a duba jam’iyyar da dan takarar – Rashidat Sha’aibu
Musa Muhammad Kutama, Kalaba
Rashidat Sha’abu: “Kamata ya yi a duba duka biyun, wato a duba jam’iyya a kuma duba dan takarar domin wata jam’iyyar idan ba ta tsayar da dan takara mai kwari ba sai ka ga an fadi zabe, amma idan ta tsayar da mutumin kirki sai ka ga an yi nasara, don haka a duba jam’iyya da dan takara, yin haka na da matukar tasiri.”
Dan takara ya kamata jama’a su zaba ba jam’iyya ba – Murtala Y. Idris Alkajuriyyu
Daga Ahmed Ali, Kafanchan
Murtala Yunus: “Ya kamata mu dauki darasi daga zaben 2015. Amma ta tabbata a halin yanzu lallai mu sani zabe ana gina shi ne bisa cancantar dan takara ba jam’iyya ko addini ba, don abin da ya gabata ya ishe mu ishara. Idan ka zabi dan takara don jam’iyya yana iya barin jam’iyyar cikin dare daya. In kuma don wani mutum ya sa ka zabi wani shi ma suna iya canja zamantakewa koma su bata. In kuma don ita jamiyyar da ake ya yi ce komai na iya faruwa, amma yana da wahala ka zabi mutum don halinsa a ce ya canja musamman in yana da kyakkyawan manufa da kudiri. Ka duba yankin Kudancin Najeriya za ka ga suna duba maslahar jihohinsu ta yadda ko da sun zabi Shugaban Kasa a wata jam’iyyar to sukan duba gwamna ko dan majalisar jiharsu su zaba a wata jam’iyya daban don kuwa shi ya san matsalar yankin da ya fito.”
Ya kamata mu rika la’akari da dan takara – Muftahulkhair Munir Malumfashi
Daga Adam Umar
Malam Muftahulkhair Munir Malumfashi: “A tawa fahimtar dan takara ya kamata a yi la’akari da shi a wajen yin zabe fiye da jam’iyya. Saboda kowace jam’iyya tana da mutanen kirki kuma tana da na banza. Ka ga ke nan ba daidai ba ne zabenmu ya karkata ga jam’iyya dungurungum ba tare da la’akari da ko wane ne jam’iyyar ta tsayar a matsayin dan takararta ba. Kamata ya yi mai yin zabe ya zakulo mutumin kirki da aka san shi da halin gaskiya ko taimaka wa al’umma wanda ya yi abubuwan alheri a wani mukami da ya rike a baya ko kuma tun lokacin ma bai kai ga rike kowane irin mukami ba.”