Shin Obasanjo ne zai tsayar wa jam’iyyu ’yan takara?
A lokacin da jiga-jigan jam`iyyar PDP, mai mulkin gwamnatin tsakiya, kama daga kungiyar Gwamnonin jihohinta zuwa `yan Kwamitin Amintattunta da kuma `yan Kwamitin Zartaswarta na kasa baki daya a tarurrukansu daban-daban a cikin watan Satumban da ya gabata, suka amince da cewa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, shi ne zai kasance daya tilo dantakarar jam`iyyarsu […]
A lokacin da jiga-jigan jam`iyyar PDP, mai mulkin gwamnatin tsakiya, kama daga kungiyar Gwamnonin jihohinta zuwa `yan Kwamitin Amintattunta da kuma `yan Kwamitin Zartaswarta na kasa baki daya a tarurrukansu daban-daban a cikin watan Satumban da ya gabata, suka amince da cewa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, shi ne zai kasance daya tilo dantakarar jam`iyyarsu na neman shugabancin kasa a zabenshekarar mai zuwa. Ita kuwa babbar jam`iyyar adawa ta APC, cewa ta yi zata bude kofar takararta a dukkan mikamai ga dukkan membobinta masu sha`awar haka da aniyar bada dama a yi da dukkan mai sha`awa.
Bisa ga karatowar lokacin takarar fitar da gwani ne ya sanya wasu jiga-jigan jam`iyyun biyu a ranar Juma`ar da ta gabata suka kai ziyara gidan tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun. Ayarin jiga-jigan jam`iyyar APC a karkashin jagorancin babban jagoranta na kasa baki daya Alhaji Ahmed Bola Tinubu, su suka fara isa gidan tsohon shugaban kasar, gama ganawarsu ke da wuya, sai ga ayarin jam`iyyar ta PDP, ya yi sallama a karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark darakiyar Gwamnan Jihar Delta, Emmanuel Uduaghan, shugaban kungiyar gwamnonin jam`iyyar.
Idan dai mai karatu bai banta ba, bayan kafuwar jam`iyyar APC, ta hadakar wasu jam`iyyun adawa hudu a bara (ACN da ANPP da CPC da wani bangare na jam`iyyar APGA), an ruwaito tsohon shugaban kasa Obasanjo yana fada wa ayarin jiga-jigan APC din da suka kai masa ziyarar bangirma cewa, shi ne babban Ubangidan jam`iyyar ta APC.
Bayan kammala ziyarar ayarin APC an ji shugaban ayarin Alhaji Tinubu, yana fada wa manema labarai cewa sun zo ne su tattauna da Cif Obasanjo akan yadda za su ceci `yan kasar nan. “Ba mu da masaniyar komai da komai, don haka muna bukatar mu yi tuntuba. Kazalika, mun yi la`akari da cewa tsofaffin yaransa ne suke son tsayawa takarar neman shugabancin kasar nan cikin jam`iyyarmu ta APC, don jin kowace shawara zai ba mu akan kowannensu ya sa muka ziyarcesa.” Inji tsohon gwamnan jihar Legas.
Ya ci gaba da cewa “Na buda maku da yawa, wajen sanar da ku abin da ya kawo mu nan, Ina jin na zama mai saukin kan gaske da na fada ma. Amma ba zan fada ma ba inda maganarmu ta kwana akan ganawarmu, amma dai ka samu damar na fadama abin da ya kawo mu, amma karshen zance baka ji daga bakina ba. Tunaninka naka ne, kasan dai shi (Obasanjo) dan jam`iyyar PDP ne, don haka sai mu tsaya akan haka.” In ji Tinubu.
A ayarin PDP, an ruwaito Gwamnan Jihar Delta Mista Uduaghan yana fada wa manema labarai cewa: “Ziyarar tamu tana da nasaba da kokarin lalubo hanyoyin sasanta `yan jam`iyyarmu da aka bata mawa, kuma Cif Obasanjo ya tabo batutuwa masu yawa da suka shafi jam`iyyarmu da kasa baki daya, batutuwan da za su kara motsa jam`iyyarmu,” in ji gwamnan.
Mai karatu, ka ji abin da ya kai wancan ayarin manyan jam`iyyu biyu gidan Cif Obasanjo, da ake kyautata zaton daga cikinsu Allah zai ba daya daga cikin dantakararsu nasara cin zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Babu wani abin labarai ko mamaki idan aka ce ga jiga-jigan jam`iyyar PDP na kasa baki daya sun niki gari sun je wajen Obasanjo, don neman mafita akan harkokin jam`iyyarsu, bisa ga matsayin da ya rika a cikinta da irin rawar da ya ci gaba da takawa bayan ya bar mulki a shekarar 2007. Sanin kowane a kasar nan tsohon shugaba kasa Obasanjo shi kadai ya dauko tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa bayan ya kammala zango biyu na Gwamnan Jihar Katsina 1999 zuwa 2007, ya ba shi takarar neman shugabancin kasa a shekarar 2007, shi da shugaban kasa mai ci yanzu Dokta Goodluck Jonathan yana Gwamnan Jihar Bayelsa a zaman mataimaki.
Amma tabbas ya zama abin labari da ban mamaki a ce da kai yau ga jiga-jigan babbar jam`iyyar adawa mai kwadayin karbar mulki daga jam`iyyar dake rike da shi ta je neman fatawar wa za ta tsayar a zaman dan takararta ga shugaban jam`iyyar da ke mulkin. Ya kamata a daidai wannan gabar in yi wa mai karatu, karatun bayani akan irin yadda shugaba Obasanjo yake ko ya zauna da manyan `yan takarar neman shugabancin kasa uku na jam`iyyar adawa ta APC, wato Janar Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso.
Kowa ya sa ni cewa tunda Janar Buhari ya shiga siyasa ya kuma zama dan takarar neman shugabancin kasa a inuwar rusasshiyar jam`iyyar adawa ta ANPP a shekarar 2003, suka shiga adawa da shugaba Obasanjo, wanda har ta kaisu ga Kotun jin kararrakin zaben 2003, dadin-dadawa kuma har Cif Obasanjo ya kammala mulkinsa na zango na biyu, duk da damar da kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba Janar Muhammadu Buhari a zamansa na tsohon shugaban kasa ya kasance mamba a Majalisar kasa, amma babu tarihin da rana daya Janar din ya taba halartan wancan taro a lokacin Obasanjo da ma zuwa yanzu. Ka ga kenan duk tsawon wannan lokaci Janar Buhari babban dan adawa ne ga gwamnatin PDP.
Shi kuwa Alhaji Atiku Abubakar yake sohon mataimaki ga Cif Obasanjo har tsawon shekaru takwas, a ciki da wajen kasar nan kowa ya san irin sabarta juyartar da shiga da Cif Obasanjo, musamman a shekarar 2007, da Atikun ya fito karara ya nunacewa ko ta halin kaka sai ya gaji Obasanjo. Ta kai `yan kasa na ganin in banda jajircewa irin ta Atikun a wancan lokacin Obasanjo so ya yi ya daure shi, amma dai hakan bata faru fa saboda Kotuna da Atiku ya rika garzayawa.
Shi kuwa gwamna Kwankwaso kasancewarsa gwamann Jihar Kano, tun a shekarar 1999 zuwa 20003, suke tare da Cif Obasanjo, da kuma ya fadi zaben 2003, Cif Obasanjo ya yi masa Minisatan Tsaro. Yanzu dinma duk da ya koma jam`iyyar APC, yana nan a matsayinsa na dan gidan Cif Obasanjo. Da wannan mai karatu a bayyyane take babu yadda za a yi Obasanjo da bakinsa ya ce da ayarin na APC, su bada takara ga Buhari ko Atiku, don kuwa kowannensu in ya samu mulki za ta iya kaisu fagen su daure Obasanjo, amma da gudu zai iya goyon bayan a ba Gwamana Kwankwaso takara. To, ba ma wannan ba, hatta su kansu jiga-jigan jam`iiyyar APC irinsu Alhaji Tinubu, za su fi sha`awar a ce Gwamnan Kwankwaso suka tsayar takara ba sauran wadancan biyun ba, don ko ba komai ai Kwankwaso ya yi gwamna sun yi gwamna, kuma ratarsu da shi a shekaru ba wata mai yawa ba ce, sannan kuma za su fi sha`awarsu kwaikwayi tsarin PDP na sanya tsofaffin gwamnoninsu a zaman shugaban kasa ko mataimakinsa, kamar yadda tarihi ya tabbatar yanzu tun daga kan Atikun zuwa marigayi `Yar`aduwa da shi kan shi shugaba Jonatahan da Alhaji Namadi Sambo da suke mulki yanzu.
Wannan ba komai ba ne illa tsarin salon shugabannin kasar nan na siyasar yaro da ubangida, ta yadda za a ci gaba da tabka barna ba a hukunci. Dubi dai irin yadda yau shekaru bakwai Hukumar yaki da ta`annati da kudin jama`a ta EFCC, take ta fama da shari`ar wasu tsofaffin gwmnonin jihohi, amma yanke hukunci ya faskara, don kawai a lokacin da suke kan mulki su suke dora kowane shugaban kasa.
`Yan uwa Barka da Sallah, mu kuma ci gaba da addu`a.