Shin rashin sanya matasa a cikin siyasar ne matsalar Najeriya?

Batun sanya matasa ko ba su damar tsayawa takara na kara tayar da kura a kasar nan, inda wadansu ke ganin yawancin ‘yan siyasar Najeriya sun tsufa, wadansu kumake ganin abin da babban zai hango, yaro bai iyawa domin suna ganin ta yaro kyau take yi ba ta karko. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya […]

Shin rashin sanya matasa a cikin siyasar ne matsalar Najeriya?

Batun sanya matasa ko ba su damar tsayawa takara na kara tayar da kura a kasar nan, inda wadansu ke ganin yawancin ‘yan siyasar Najeriya sun tsufa, wadansu kumake ganin abin da babban zai hango, yaro bai iyawa domin suna ganin ta yaro kyau take yi ba ta karko. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ta bakin mutane, kuma ga amsoshin da suke bayarwa:


Babu matsala in ba matasa a siyasar kasar nan – Halima Isma’il Aliyu

Ahmed Garba Mohammed, Abuja


Halima Isma’il Aliyu (Baby):  A nata ra’ayin ta ce a  gaskiya rashin matasa a siyasa ba matsala ba ce saboda wani lokacin ma sanya matasa a harkar siyasa ke kawo rudani da tashin hankali.  Mafi yawan matasa ana amfani da su ne wajen yin bangar siyasa don wadansu su amfana.

A bangaren shugabanci kuwa, lokaci bai yi ba da za a rika ba matasa dama suna yin shugabanci a Najeriya domin matasan yanzu sai a hankali, ba abin da suka sanya a gaba sai son mallakar abin duniya ko ta halin kaka. Da yawa daga cikin matasan yanzu ba su da wani buri illa su auri mata da sayen motocin kece raini da gina manyan gidaje  da sauransu amma ba tunanin yin shugabanci na adalci ne a gabansu ba.


Rashin ba matasa dama 

ba matsala ba ce – Ado Musa Goje

Ahmed Garba Mohammed, Abuja


Ado Musa kaura Goje a nasa ra’ayin ya ce, gaskiyar magana ba rashin ba matasa dama a dama da su a siyasar kasar nan ne matsalar ba.  Babbar matsalar da ke damun kasar nan ita ce na rashin shugabanni nagari.  Shi shugabaci ba babba, ba yaro muddin idan za a yi adalci.

A ganina idan har shuganannin da ake ganin shekarunsu sun yi nisa amma suna yin kuruciyar bera wato sata to ina ga in am ba matasa dama da ake ganin su ’yan bana bakwai ne masu son kyale-kyalen duniya ai wasoso kawai za su rika yi da dukiyar al’umma ba tare da sun tsinana komai ba. 

Don haka a nawa ra’ayin ba batun  rashin ba matasa dama a siyasar kasar nan ne matsalar ba, matsalar ita ce ta rashin jin tsoron Allah a yayin da ake gudanar da shugabancin.


Babbar matsala ce rashin ba matasa dama – Malama A’isha Lawal (Momie)

Daga Ahmed Garba Mohammed a Abuja


Malama A’isha Lawal (Momie):  A nata ra’ayin ta nuna ko shakka babu rashin ba matasa dama a siyasar kasar nan babbar matsala ce.  Idan aka yi la’akari da yadda tsoffafi suka yi baba-kere a siyasar kasar nan shekara da shekaru su ke mulki alhali sun ki ba matasa dama, wannan ba karamar illa ba ce. Hasalima ana bukatar sababbin jini game da masu rike da madafun iko a duk fadin duniya ba Najeriya kadai ba.  Idan aka lura yanzu manyan kasashen duniya ciki har da Najeriya Afirka suna zabar matasa ne a matsayin shugabannin kasashensu.  Na baya-bayan nan shi ne yadda aka zabi matashi a matsayin shugaban kasar Laberiya wato George Weah, hasalima tsohon dan kwallon kafa ne.  Don haka muddin ana so abubuwan siyasa su daidaita a kasar nan sai an rika ba matasa dama ana damawa da su.


Rashin kishi ne matsalar – Garba Ahmed

Ahmed Garba Mohammed, Abuja


Garba Ahmed:  A nasa ra’ayin game da rashin ba matasa dama a siyasar kasar nan, ya ce ba a nan gizo ke sakar ba. Matsalar ita ce ta rashin kishin kasa. Duk wanda aka ba shugabanci muddin ba zai nuna kishin kasa a shugabancin ba, to dole ne a samu matsala walau tsoho ne shi ko matashi.

Abin da ya sa kasashen duniya suka ci gaba shi ne nuna kishin kasarsu, amma mu a nan gida sai ka tarar da zarar an ba wani mulki walau tsoho ne ko matashi sai ya shiga yin handama da babakere. To a nan ai ka ga ba batun cewa a ba matasa dama don a dama da su ne matsalar ba, matasalar dai ta nuna kishin kasa ne.


Masu kishin kasa muke 

bukata – Aliyu Khaleed

Isiyaku Muhammed, Kaduna


Aliyu Khaleed: “Najeriya na bukatar mutane masu kishin kasa ne. Ya kamata mu gane cewa mulki na bukatar hikima ne ba wai shekaru ba. Masu iya magana na cewa “amfani shekaru kawai don kirga ne” sannan da yawa daga cikin matasan da ke cikin yanzu ba sa yin abin da ya dace. Kawai ya kamata mu duba wadanda za su iya ba tare da la’akari da shekarunsu ba. Ya kamata a ba kowa damarsa na tsayawa takara.”



Lokaci ya yi da za a ba matasa dama – Hajiya Bilkisu Abdullahi

Ahmed Garba Mohammed, Abuja


Hajiya Bilkisu Abdullahi:   A nata ra’ayin ta ce rashin ba matasa dama ana damawa da su a siyasar kasar nan shi ke kawo koma-baya. In aka lura da yadda kasashen duniya suke zabar matasa a matsayin shugabannin kasashensu, mu a nan Najeriya ba haka abin yake ba.  Alal misali dauki kasar Faransa inda suka zabi matashin shugaba. Ka dubi Koriya ta Arewa, nan ma matashi ne a matsayin Shugaban kasa.

Yanzu fa duniya ta canja, ana yi ne da masu jini a jika da kuma masu kaifin tunani, tunda ana amfani ne da kafofin sadarwa irin na zamani wajen gudanar da shugabanci.  To mene ne amfanin a rika amfani da tsofaffin da tunda aka karbi mulkin kasar nan a 1960 kawo yanzu suke shugabanci?  Gaskiya lokaci ya yi da za a ba matasa dama wajen yin shugabanci a kasar nan.