Shin taron da Buhari ya yi da gwamnoni zai magance matsalar tsaro?
Matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan ta zama ruwan dare, inda a kusan kullum sai ka ji an kai hari wani gari ko a sace mutane domin neman kudin fansa, baya ga rikicin Boko Haram da dai sauran matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan. Wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin wadansu jama’a kan shin taron […]
Matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan ta zama ruwan dare, inda a kusan kullum sai ka ji an kai hari wani gari ko a sace mutane domin neman kudin fansa, baya ga rikicin Boko Haram da dai sauran matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan. Wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin wadansu jama’a kan shin taron da Shugaba Buhari ya yi da gwamnonin jihohi 36 da kuma shugabannin tsaro kan tabarbarewar tsaro zai iya magance matsalar?
Babu wani amfani da taron zai yi – Bolori Muhammad M Lantewa
Muhammad Aminu Ahmad
Ba yau aka fara irin wannan taro ba, amma me ya haifar? Mun dade muna jin ana irin yin tarurruka makamacin haka, babu wani abu da muka ga ya canja kullum a gidan jiya muke a harkar tsaro a wannan kasa. Sai dai tunda wannan taro shi ne irinsa na farko a shigowar wannan gwamnati muna fata za a dauki wani mataki da zai kawo karshen wannan matsala ta rashin tsaro da kasar nan take fama da ita.”
Ba zai sauya komai ba – Umar Ahmad Abubakar Gombe
Dalhatu Liman
Ba tun yau aka saba kiran irin wannan taro na masu ruwa-da-tsaki ba, a fadar Shugaban Kasa domin tattauna matsalar tsaro a kasar nan.
Ganawar da aka yi da gwamnoni da kuma hafsoshin tsaro ba za ta sauya komai ba, muddin ba a fito an dauki kwararan matakan da za su yi wa tufkar hanci ba. Dole gwamnati ta tashi tsaye wajen inganta jami’an tsaro, ta ba su kayan aiki na zamani, a rika ba su duk wasu hakkokinsu da kudaden alawus. Wadannan matsaloli ne da ba sa bukatar kiran taro a fadar Shugaban Kasa kafin a magance su.”
Lallai hakan zai bunkasa tsaro – Zainab Yusuf (Zee ’Yar Mamanta)
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Kwarai kuwa, hakan zai kawo ko ya rage aukuwar kai hare-hare da yin garkuwa da mutane a sassan kasar nan. Idan Shugaban Kasa ya samu hadin kan wadannan shugabanni wato gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaro, to za a yi wa tufkar hanci, kuma yin hakan shi ne daidai.”
Zai Taimaka wajen Magance Matsalar – Auwal Rabi’u Abdullahi Jos
Dalhatu Liman
Hausawa suna cewa da dan gari ake cin gari. Wannan taron zai bayar da gudunmawa kwarai wurin magance matsalolin tsaro da suke addabar jihohin Najeriya. Su kuma gwamnonin, Allah Ya ba su ikon ba da gudunmawa 100 bisa 100 wurin tona asirin ’yan ta’adda a jihohin da ake fama da rashin tsaro. Ga, jami’an tsaron Najeriya, mun sani kuma tarihi ya nuna cewa kwararru ne wurin magance matsalolin tsaro. Muna rokon Allah Ya kara musu basira da karfin gwiwa wurin tabbatar da zaman lafiya a jihohinmu. Muna rokon Allah Ya ba mu zaman lafiya a jihohinmu da Najeriya baki daya.”
Babu abin da zai canja –Ummulsalma Ibrahim
Ahmed Garba Mohammed a Kaduna
Sau nawa aka yi irin wannan taro amma babu abin da ya canja? Saboda haka ina da shakku duk da Shugaban Kasa ya gana da su babu wani abu da zai canja domin ai ba yau aka fara irin wannan taron ba, a can baya da aka yi me ya haifar babu sai dai kawai mu ci gaba da taya su da addu’a.”
Hakika zai taimaka wajen shawo kan matsalar – Sani Kawu Muhammad Wudil
Muhammad Aminu Ahmad
Ni dai a ra’ayina, taron insha Allahu zai taimaka wajen kawo zaman lafiya, domin idan an ce an zauna hakan babu tautaunawa a tsakanin manya, to ba za a gano hanyoyin da za a kare wadannan matsaloli da suke tafiya a cikin wannan kasa tamu ba. Yin hakan yakan iya sa wa daga ciki akwai wadanda za su iya zuwa kananan hukumomi ko kauyukansu da za su iya ba da bayanai na wasu batagari da ke zama a tsakanin al’umma. Don haka yin wannan taro zai taimaka sosai wajen dakile matsalar tsaron da muke fama da ita.”