Shin tsoffin shugabanni na tasiri wajen samun mulkin Nijeriya?

Siyasa kasuwar buƙata ce, kowa inda zai samu riba ko biyan buƙata yake karkata.

Shin tsoffin shugabanni na tasiri wajen samun mulkin Nijeriya?

Siyasar ubangida wani abu ne da ya jima yana haifar da ce-ce-ku-ce, musamman a lokutan zabe, sai dai bayan ga batun ubangida akwai wasu kusoshi na kasa irin tsoffin shugabanni da ake ganin kan yi tasiri ko taka rawa wajen tafiyar da harkokin siyasar kasar nan.

Kusan kowane dan siyasa a kasar nan ba ya rasa wani wanda yake yi wa biyayya, baya ga tsofaffin shugabanni da ake yi wa kallon suna da tasiri ko bayar da gudunmawa wajen tafiyar da tsari na dimokuradiyya.

Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya shekara 25 da suka gabata ake ganin yadda wasu ’yan siyasa da ke takara ko hankoron takara kan tattauna ko ziyarta da mu’amala da tsoffi ko shugabannin na siyasa.

A lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo akwai wadanda suka rika ganin cewa tsohon Shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Babangida ya bayar da gudunmawa wajen dora shi a kujerar mulki.

Sannan akwai wasu ’yan siyasa na wannan zamani, irin su Mista Peter Obi na Jam’iyyar Labour da ake gani ko zargin Obasanjo ya mara masa baya a takararsa ta zaben 2023.

To sai dai wani abu da ya fi jan hankali a wannan lokaci shi ne yadda mutanen da ake ganin na da karfi a siyasar Nijeriya ke bibbiyar tsoffin shugabannin suna tattaunawa da su.

Me ake tattaunawa?

Duk da dai babu wani da zai iya fitowa ya ce ga takamaiman abubuwan da ake tattaunawa a lokacin wasu ziyarce-ziyarce da ake ganin ’yan siyasar na yi.

Misali, a kwanan nan an ga tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar na irin wannan ziyara, ciki har da wadda ya kai wa tashon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Daura.

Haka kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, wanda shi ma ake ganin take-takensa na kokarin taka rawar gani a zabe mai zuwa, ya kai irin wannan ziyara ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kwanakin baya da kuma tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

Shi ma Mista Peter Obi yana ta karakaina da gudanar da wasu ayyukan da ke kama da neman hadin-kai ko shirya kansa gabannin zaben 2027.

Masana harkokin siyasa sun ce, idan aka yi la’akari da tsarin siyasar kasar nan, kusan duk wannan ba wani abu ne sabo ba.

Hanya ce ta kulla kyakkyawar alaka da neman gwada sa’a a kan wasu bukatu.

Ta yaya tsofaffin shugabanni ke tasiri?

Masana harkokin siyasa irin su Farfessa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero da ke Kano ya jadadda cewa, ire-iren wannan ziyara ko ’yar kebiya tsakanin ‘yan siyasa ba bakon abu ba ne.

Farfesa ya bayar da misali da wasu fitattun ’yan siyasa a baya da suka nemi takara da amfani da salon neman goyonbaya daga wasu tsofoffin shugabannin kasa domin ganin sun yi tasiri.

Ya ce, ana kokari ne na neman goyon-bayan manyan ‘yan siyasa duk da cewa kowa na da nasa.

“Galibi akan yi hakan ne saboda idan takara ta samu ko lokacin zabe ya zo, ba zai yi suka ba ko bata dan takara”.

Haka kuma salon ne na hadin-kai ko hada karfi da karfe wajen tafiya tare, saboda ’yan siyasa da zarar an gama zabe hankoronsu shi ne zabe na gaba.

Farfesan ya ce, sirrin takara ko siyasa ba sai ana jam’iyyar guda ba, saboda akwai hikima da kowane dan siyasa ke da ita wajen bayar da gundumawa da ke tasiri matuka a lokutan zabe.

Ya bayar da misali da zaben 2023, inda Peter Obi ya samu goyon-bayan Obasanjo, don haka ana ganin tasiri a siyasa ko takara idan aka yi amfani da tsofaffin shugannin kasa.

Farfesa Kamilu ya ce, duk da cewa cin zabe ba wai dole sai da wani tsohon Shugaban Kasa ba, akwai wani salo ko tasiri na jan hankalin magoya-baya su yi koyi ko aiwatar da abin da suke ganin shi ubangidansu ke yi.

Sannan ana hakan wajen neman taimako daga ketare saboda a wurare daban-daban idan aka samu irin wannan, suna yi wa mutum hanyar samun kudi da goyon-bayan kasashe.

Farfesan ya kuma tabo batun masu hannu da shuni da za su iya amfani da tasirinsu wajen ganin dan takara ya kai labari, muddin an tsaya masa.

Babu jam’iyya a wannan harkar

Farfesa Kamilu ya bayyana cewa, akwai shekaru na siyasa da rayuwa da idan mutum ya kai ko rikakken dan siyasa to yakan juya akalar wasu tsare-tsare.

Kamilu ya ce, kawai abin takacin shi ne yadda galibi kowa bukatunsa kawai yake bai wa fifiko a lokuta da dama na siyasa.

Masanin ya ce, siyasa kasuwar bukata ce, kowa inda zai samu riba ko biyan bukata yake karkata.

Don haka a cewarsa akwai rawar da kowane dan siyasa ke takawa ba wai kawai tsofaffin shugabannin kasa kadai ke takawa ba idan aka zo batun zabe da takara.