Shin ya dace gwamnati ta hana almajiranci?
Gwamnatin Tarayya tana shawarar hana almajiranci a fadin kasar nan, inda jama’a da dama ke bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan lamari, ganin yadda harkar almajiranci take a wannan kasa, wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin wadansu jama’a a sassan kasar nan: Zata iya hanawa – Hashimu Garba Daga Musa Kutama, Kalaba Eh! To in har za […]
Gwamnatin Tarayya tana shawarar hana almajiranci a fadin kasar nan, inda jama’a da dama ke bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan lamari, ganin yadda harkar almajiranci take a wannan kasa, wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin wadansu jama’a a sassan kasar nan:
Zata iya hanawa – Hashimu Garba
Daga Musa Kutama, Kalaba
Eh! To in har za ta yi abin da ya dace, za ta iya hanawa. Dalilina kuwa shi ne kamar yadda gwamnatin da ta gabata ta Goodluck ta dauko na kakkafa makarantun allo, kuma kada a yi ta jami’an Gwamnatin Goodluck a ce sai dan gata ne za a sa shi a makarantar a’a idan za a dauki dan kowa da kowa a sa to za ta iya hanayawa.
Matakin ya dace – Abdullahi Sani na Cibiyar IAR, Samaru
Daga Aliyu Babankarfi Zariya
Ni dai a ra’ayina matakin hana almajiranci da gwamnatin ke shirin dauka ya dace, domin a yanzu abin kara lalacewa yake yi.
Sai ka ga yaro dan shekara biyar ba wai ya rasa iyayensa ba ne, amma an rabo shi da garinsu an kawo shi inda ba ya da kowa da sunan almajiranci.
Na farko mutanen yanzu ba irin na da ba ne, amana ta yi karanci, ga rashin gaskiya da ya yawaita, ga rashin sanin mutuncin dan Adam.Kuma kowa kansa ya sani kawai hatta malamin da ka kai wa danka sai ka ga kokarinsa iyalansa ne kawai, bai damu da sauran yaran da aka ba shi amanarsu ba. Saboda canzawar al’umma a wannan zamani bai dace a rika daukar yara ana raba su da inda suke ba.
Kama ai yanzu ilimi ya yawaita a ko’ina. Don haka wannan shiri na hana almajiranci ina goyon bayan gwamnatin a kansa.
Matakin ya dace sosai – Malam Sanusi Abubakar
Daga Nasiru Bello, Sakkwato
Matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka ya dace sosai in aka yi la’akari da cewa addinin Musulunci ma ya hana bara. Ba wani magabaci a tarihi da za ka kawo ya taba zuwa yawon bara domin neman ilimi. Iyaye kawai su sako ’ya’yansu ga wani ya kula musu da tarbiyyar yaransu suna gida zaune abin da ke sanya wadansu malaman na lalata yaran su shiga rayuwa mai muni wadda ba mai son dansa ya shiga. Sai kuma su shiga da-na-sani. Mafi yawan masu zama ’yan daudu za ka samu almajiran ne, tun da iyayen sun ki hankalta su magance matsalar tabarbarewar tarbiyyar yaransu.
Bai dace a hana ba – Alhaji Ma’azu Is’haka
Daga Musa Kutama, Kalaba
Bai dace gwamnati ta hana almajiranci ba. Ba don komai ba sai don yaran nan da ke yawon almajiranci ba, ba gidajen gwamnati ko na masu mulki suke zuwa ba, wurin talakawa suke zagayawa mai niyya ya ba su, ba su tilasta wa mutum sai ya ba su. Mu abin da muke so a bari su yi ta yi bai dace ba a hana su.
Yin hakan abu ne mai kyau – Umar Hassan Tudun Jukun Zariya
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
Ai wannan kudirin da ya taso na hana almajiranci da Shugaban Kasa zai aiwatar ya dace kwarai da gaske musamman a wannan lokaci da almajiranci ya zama sana’ar bara. Domin Shugaban Kasa dan Arewa ne, kuma almajiranci wata matsala ce da ta dade tana damunmu a Arewa.
A matsayinsa na dan Arewa ya san almajiranci a da da yanzu, domin ai bara da sunan almajiranci kaskanci ne ga Arewa, don haka wannan wani hange ne mai kyau a kan Arewa.
Arewa tana da sana’o’inta da aka san ta da su, musamman noma da kiwo, sai aka koma ana bara da sunan almajiranci. Don haka ina goyon bayan wannan kudiri na hana almajiraci a wannan lokacin dari bisa dari.
Bai dace ba, a dai yi wa lamarin gyaran fuska – Nata’ala Sambo Babi
Daga Nasiru Bello, Sakkwato
Wannan maganar sam ba ta dace a kawo ta ba, akwai dai bukatar a yi wa lamarin gyaran fuska. Almajirci akwai shi cikin addini tun asali bai dace a hana abin da muke da shi a shari’a ba. Na yarda a yi masa kwaskwarima don wadansu malamai da mahaifan yara sun kauce hanyar da aka sani ta almajirci bai zai yiwu kana son danka ya yi karatu ba ka kasa daukar nauyin karatun, ka sake shi kawai ga duniya ka ce kuma ka yi abu mai kyau. Malami bai dace ya boye ’ya’yansa ba, ya rika sanya na wadansu aikin wahala don kawai an kawo su makaranta su nemi ilimi, a dora musu haraji su je gari su samo ko a tsiya ko lalama ya ce yana koya musu tarbiyya. Wadannan da wasu na daban ne ya kamata gwamnati ta duba da hanyoyin magance su ba hana almajirci ba.