Shin ya kamata a zagi Yariman Bakura?
Iya abin da nake iya tunawa da ya sa Ahmad Sani Yariman Bakura ya yi kaurin suna a wannan kasa ta Najeriya, shi ne ya auri yarinya ‘yar shekara 13 daga kasar Misra! Wanda a tunanin wasu, Yariman ya aikata wani laifi da ake kira ‘’cin zarafin ‘ya’ya mata’’ ni kuma a tunanina sai nake […]
Iya abin da nake iya tunawa da ya sa Ahmad Sani Yariman Bakura ya yi kaurin suna a wannan kasa ta Najeriya, shi ne ya auri yarinya ‘yar shekara 13 daga kasar Misra! Wanda a tunanin wasu, Yariman ya aikata wani laifi da ake kira ‘’cin zarafin ‘ya’ya mata’’ ni kuma a tunanina sai nake ganin Yarima ya yi wata sunna daga cikin sunnonin manzon rahama mai tsira da aminci, a daidai lokacin da wasu masu mukami da matsayi irin nasa suke aikata abin da ya saba wa sunnar manzon Allah, ya saba wa al’ada kuma ya saba wa kowa ne irin addini mai asali daga Allah (Kiristanci ko musulunci).
Abin da ya fi shara shi ne a samu masu mukami irin Yarima sun aikata shi ne: Su tafi dukkan kasar da suke so a duniya (ta Larabawa ko Turawa) su aikata duk abin da suke so na na shan kayan maye da lalata. Masu matsayi irin na Yarima daga Najeriya ne aka tabbatar cewa dukkan wata Otal da take duniya, sukan iya zuwa can domin shakatawa kuma su kwana da kowace irin kalar mace suke so. Hakan wasunsu ke aikatawa kuma an san su, amma ba a zage su ba sai a zagi Yarima?
Kowace al’umma da ke rayuwa a wannan duniya, musulma ce ko marar addini ce, ta yadda da cewa aure ne hanya guda kacal sahihiyar hanyar tafiyar da sha’awar da ke tattare da duk wani bil’adaman da ya balaga (mace ce ko namiji) kamar yadda dukansu suka yi amanna da cewa karuwanci harkar banza ce kuma abar kyama. Don haka aure ba magana ce ta addini ko kuma yare ba , magana ce ta wanda ke son zuri’arsa su rayuwa akan rayuwa mai kyawo musulmi ne ko kirista. Magana ce ta wanda ke son yak are kansa daga aikata zinar da addininsa ya hana aikatawa. Kuma abin da Yarima ya aikata ke nan a lokacin da ya auri waccan yarinyar har zuwa yanzu da aka tayar da irin wannan Magana a majalisar Najeriya.
Takaddamar da ke kan gudana a majalisa ta neman hana aurar da yara ‘yan kasa ga shekaru goma sha takwas, wani al’amari ne mai ban haushi da kuma daure kai. Idan dai za a ce masu wakiltar jama’a ne da ake tunanin su ne ma’abuta hankali da hangen nesa za su nemi aiwatar da wannan doka, to abin sai dai mu ce INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN. A rina, wai an saci zanen mahaukaciya. Lalleai gaske dai ake ta yin yadda aka ga dama a Najeriya da dukiyarmu, ashe wasu wakilan da muke da su jahilai ne, dabbobi marasa tunani. Wai rashin amincewa da wannan dokar da Yarima da wasu masu imani irinsa dab a su yi ba, ita ce ta sa wasu marasa hankalin ‘yan jarida da kafiran da ba su san addininsu ba suke ta yayata kalaman tozarci da tallar Yarima a matsayin wani mai laifi.
Abin da zan gaya ma irin wadannan mutane shi ne: Ba Yarima ba, ai ko mahaukaci ya san kayyade cewar kada mace ta yi aure sai ta kai wasu shekaru shashanci ne! To macen da aka halicce ta da jaraba ta son saduwa da da namiji a kowane lokaci fa? Sai taje ta yi karuwanci? Ba su damu ba idan ta yi karuwanci, amma dai kada ta yi aure! Kunji wata sabuwar hauka. Ai ya kamata dai ko ba ku yi karatun littafan addininsu ba, to sai su tuntubi wadanda suka yarda da su (Turawa) su tambaye su, shin yanayin halittar ‘yan’Adam nau’i daya ce? Idan suka yi hakan za su san cewa, akwai yarinyar da ko ba ta kai shekara 13 ba, aurar da ita shi ne alhairi idan dai ba ana so ta yi zina ba ne.
Na sha mamakin, wai wanda ke rayuwa a cikin al’umma, shi ne zai kasa la’akari da yadda diya mata ke zama karuwai tsakanin karya da gaskiya kuma dare da rana, har ya samu kwarin guiwar neman ci gaba da fadada zaman ‘ya’ya mata a gida maimaikon aurar da su! Koda yake ba mamaki, tunda ga masu tallar Luwadi daga cikin miyagun shuwagabannin nan masu matsayi guda da Yarima, amma ba a taba gurfanar da ko aka saka musu kahon zuka ba sai shi da bai saba wa Allah ba, kuma bai sabawa al’ada ba.
Allah Ya sani kuma Ya gani, ka aurar da ‘yarka da shekara 14 ya fi alkhairi bisa ta koma karuwa. Amma dai idan ana ganin kamar karya nake yi, to mahaifi ya kira ‘yarsa ya tambaye ta tsakani da Allah me take bukata tsakanin aure da zaman gida, idan dai ta kirki ce mai son alkhairi ga kanta, to zai ji ta zabi gidan mijinta. Idan kuma ba ta zabi haka ba, to sai ya sa likitoci su duba lafiyarta, lalle akwai wata matsala. In kuma ba haka ba, to ya sani ‘yarsa ta zama karuwa.
Amma ba mamaki. Idan ina cewa karuwa ba za su fahimta ba. Ba ina nufin karuwar da ake biya kudi ko kuma karuwar da take da dakin kanta ba, ina magan akan karuwar da take zaune a gidan iyayenta, idan rana ta yi ta fita unguwa sai ta zarce dakin samarinta ko kuma ta rika labewa da mata ‘yan’uwanta suna madigo! Maganar ta yi zafi ko? To sai dai mu yi hakuri dukanmu, amma gaskiyar abin da ke faruwa kenan kuma kowa ya sani in banda ‘yan majalisar da ke neman aza wannan doka. Tir! ’Yan majalisa kun ji kunya. Allah Ya sa mu gama lafiya don alfarmar Annabi Muhammad SAW
Nasir Abbas Babi 08033186727/08095653401.