Shin za ka iya barin matarka ko ’yarka ta shiga siyasa?

A daidai wannan lokaci da muke ciki na siyasa, musamman da a nan Najeriya take kara zafi, da kuma yadda mata suke ta fafutuka a kan lallai dole a rika sanya su a cikin harkokin siyasar kasar nan. Wasu suna ganin cewa kawai mata su zauna a gida su lura da harkokin gida, su bar […]

Shin za ka iya barin matarka ko ’yarka ta shiga siyasa?

Ba zan tava yarda ba – Idris Hamidu

A daidai wannan lokaci da muke ciki na siyasa, musamman da a nan Najeriya take kara zafi, da kuma yadda mata suke ta fafutuka a kan lallai dole a rika sanya su a cikin harkokin siyasar kasar nan. Wasu suna ganin cewa kawai mata su zauna a gida su lura da harkokin gida, su bar maza da siyasa domin akwai rudu a lamarin. Wasu kuma suna ganin ai ba komai, domin kuwa ko ba komai su ma matan ’yan kasa ne kuma mutane ne kamar kowa. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan ko za su iya barin matansu su shiga a dama da su a harkokin siyasa? Ga abin da suke fada:

Ba zan bar matata ba – Sanusi Mohammed Fari

Daga Magaji Isah Hunkuyi, Jalingo

Sanusi Mohammed  Fari, dan siyasa: “Ba zan bar matata ko ’yata ta shiga siyasa ba domin ba na so matata ko ’yata ta rika cudanya da maza kamar yadda mata ’yan siyasa ke yi. Kuma siyasa sana’a ce wanda akwai rashin kunya da bude ido. Ni kuma ina sun ’ya’yana mata da matata su kasance masu kunya kuma su zauna a gida kamar yadda al’adata da addinina ya tanadar.”

Ba zan bari ba – Ibrahim Jibrin

Daga Magaji Isah Hunkuyi, Jalingo

Ibrahim Jibrin: “Ba zan bar matata ko ‘yata ta shiga siyasa ba domin bana son inga matata ko ‘yata suna cudanya da maza kamar yadda mata ’yan siyasa ke yi. Yadda mata ’yan siyasa ke baro gidajensu su tafi harkan siyasa a wasu garuruwa ya saba wa al’ada da dokokin addinina. Saboda haka ba zan yarda matata ka ‘yata wata ta shiga siyasa ba.”

Gaskiya kishi ba zai bar ni ba – Hussein Ibrahim

Daga Abbas Dalibi, a Legas

Hussein Ibrahim Ahmad: “A ra’ayi na ba zan bar matata masoyiyata  ta yi siyasa ba domin ni mai matukar kishin  matata ne, muddin ta shiga siyasa za ta rika cudanya da mazan da ba muharamanta ba, kuma za ta rika zuwa yakin zabe, ka ga a nan ba zan iya gindaya mata doka ba ta kiyaye. Bugu da kari wasu lokutta ma tafiya zai kamata da zai kai ba za ta kwana a gida ba, wannan babba hadari ne, wannan zai sa ta zamo ba ta da lokacina da na iyali kuma ba za ta ga mutuncina ba, sai rashin kunya da karya da fadin rai musanman ma a ce tana da abin susan kumba. Haka zalika siyasar yau ba daya ba ce da ta wacce ta gabata lokacin marigayi Sa Ahmadu Bello Gamji da Abubakar Tafawa Balewa da Malam Aminu Kano da su Dokta Nnamdi Azikiwe da Chief Obafemi Awolowo. Sai bangaren mata irinsu marigayiya Hajia Gambo Sawaba da suka yi gwagwarmaya tare da Jam’iyyar PRP da marigayya Kulu Abata da su Laila Dogon Yaro. Yanzu siyasa ta kazance da kalaman batanci da rashin kunya da rashin mutunci da rashin kyakyawar akida.”

Ba zan taba yarda ba –  Idris Hamidu

Adam Umar, Abuja

Malam Idris A.Hamidu Madalla: “A gaskiya ita matata aure ne ke tsakaninmu, saboda haka maganar shiga siyasa bai taso ba. Ba yadda zan yarda ta rika zuwa taruka ko amsar waya ta ko ina da sunan siyasa. Musamman ma dai a irin kwamacalar siyasa irin tamu. Haka nan ita ma ‘yata ban ga yadda zan bari ta yi siyasa ba.

Dama daga makaranta sai gida, tana gamawa makarantar kuwa sai aure. Sai dai idan a gidan mijin ne can shi ya yarje mata ta yi to wannan kuma lamarinsu ne.”

Gaskiya ba zan bari ba a irin siyasar Najeriya ‑ Dauwd Isa

Adam Umar, Abuja

Malam Dawud Isa: “A gaskiya a yanayi irin ta siyasar kasarmu da nake gani, ni dai ba zan iya barin matata ko ’yata ta shiga harkar siyasa ba saboda ya saba da irin tarbiyanmu ta addini da kuma al’adarmu. Sai dai idab watakila za su gudanar da harkokinsu ne a kebe ta hanyan ware masu bangarensu daban sannan kuma a rika yin abun a tsabtace, to wannan daban. Amma a irin wannan siyasa tamu haka nan ka na tare da matarka a gida sai a kirata ana nemanta wajen taro wani zubin ma da tsakar dare ake fara taron nan, ka ga ai wannan ba abu ne da mutum zai yarda da shi ba.”

Zan iya bari saboda ana dakile hakkin mata a siyasa – Musa Yahaya

Daga Abbas Dalibi, a Legas

Musa Yahaya Nayis: “Ni a ra’ayina zan bar matata ko ’yata ta shiga siyasa domin da yawan lokuta idan ka kula yadda masu mulkin suke dakile hakkokin mata a bangaren cigaban da ya dace da su, hakan kan  samu nasaba da rashin jajirtatun mata masu kamala ne. Ayanzu haka muna kokarin hada cibiya ta mata masu mutunci wadanda kafin ka samu wanda zai iya kallon fuskarsu kai tsaye ya musu maganganun banza sai an tona, kuma yanayinsu kadai zai bada gudunmawa wajen kwatar wa mata ’yanci. Idan ana samun jajirattu irin wadannan mata suna shiga a dama da su a siyasa, za a samu cigaba a al’amuranmu na yau da kullum.”