Shin Zamfara Najeriya ce ko Nijar?

Ina neman alfarmar gidan jaridar nan mai albarka don neman amsar wasikata mai taken: “Shin Zamfara Najeriya ce ko Nijar? Da farko ina taya Shugaba Buhari murnar cikar burinka na matsawa mataki na gaba wato cin zabe. Shugaban Najeriya, na zabi in fara da wannan take na wannan wasika tawa bisa ga hali da  yanayin […]

Shin Zamfara Najeriya ce ko Nijar?
Shin Zamfara Najeriya ce ko Nijar?

Ina neman alfarmar gidan jaridar nan mai albarka don neman amsar wasikata mai taken: “Shin Zamfara Najeriya ce ko Nijar?

Da farko ina taya Shugaba Buhari murnar cikar burinka na matsawa mataki na gaba wato cin zabe.

Shugaban Najeriya, na zabi in fara da wannan take na wannan wasika tawa bisa ga hali da  yanayin da muka ga gwamnatinka na yi dangane da sha’anin tsaron jiharmu mai albarka wato Zamfara gidan noma da kiwo.

Ina son in kara shaida maka game da halin tagayyara da al’ummar karkara na Jihar Zamfara ke ciki a daidai wannan lokaci. Maganar gaskiya, Jihar Zamfara na ci gaba da zama dandalin zubar da jinin bayin Allah wadanda suka tsaya tsayin daka sai kai, duk da barazanar da suka sha.

Ya Mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari! Jihar Zamfara fa yanzu masu mulkinmu babu ruwansu da rayukan da ke salwantuwa a duk rana ta Allah a jihar, su dai kawai babban burinsu shi ne yaya za su yi  su samu damar cin zabe, duk da ko can ba wani kazar-kazar suke yi ba na dakile wannan matsala.

Ya Mai girma Shugaban Kasa! Ina son in tabbatar maka cewa, duk wani abu da za su fada maka na dadin baki kada ka yarda don babu wani abu da suke yi na dakile wannan matsala.

Hakika Jihar Zamfara yanzu ta kai wani hali da ya kamata ka shigo ko kuma kakaba mana dokar ta-baci da kuma sake fasalin wannan aiki na tsaro.

Yanzu haka yankin da nake tun bayan kamawar watan Fabrairun bana, mun samu rashin rayuka sama da 30 amma har yanzu maganar nan da nake ba a turo mana jami’an tsaro ba, don haka babu wanda ya zo mana jaje daga cikin mahukuntanmu. Abin takaici da Allah wadai har sun mai da lamarin siyasa suna fadin magoya bayan wani dan siyasa ne ake kashewa ba nasu ba don kawai mun ki goyon bayansu.

Duk da kai din ma ya kamata ka canja irin yadda kake ware jiharmu ta Zamfara kamar dai ba ’yan kasa ba. Don mun ga irin haka ya faru a Jihar Sakkwato ka tura musu da sakon jaje haka a Kajuru ta Jihar Kaduna ka tura musu da sakon jaje, amma a cikin makon nan da ya gabata irin hakan  ta faru a garin Kawaye a Karamar Hukumar Anka a nan Zamfara inda aka kashe mutum 13 aka yi awon gaba da mata 40 daga cikin har da mai garin na Kawaye da iyalansa sai kuma Kware a Karamar Hukumar Shinkafi an kashe mutum 32 sun kuma dawo ranar Lahadi sun mamaye garin sun kashe wadansu kai dai sai wanda ke jihar nan kawai zai iya fadin halin da muke ciki.

Irin wannan muke dauka kamar ka ware mu ne ba ka son daukar lamarinmu daya da na sauran jihohi.

Ya Mai girma Shugaban Kasa! Don Allah da AnnabinSa ka waiwayo jiharmu ta Zamfara kafin su ida ganin bayanmu domin yanzu dai a gaskiya mun fid da kauna daga mahukuntan jiharmu ta Zamfara.

Na gode, Allah Ya sa a yi mulki na gaba lafiya Ya kuma ba da nasara.

Daga Ibrahim Ma`azu Mada Bakenawa Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. 08166494442, 07084400431.