Shin Zamfara ta shirya karbar almajirai daga jihohi?

Duk da bayyana aniyarta ta karbar bakin almajirai, har yanzu babu wani shiri a kasa da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi game da hakan. A kwanakin baya ne Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa ba za ta kori almajiran wasu jihohi daga Zamfara ba. Da yake karbar wasu malamai da suka kai masa ziyarar […]

Shin Zamfara ta shirya karbar almajirai daga jihohi?

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara

Duk da bayyana aniyarta ta karbar bakin almajirai, har yanzu babu wani shiri a kasa da Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi game da hakan.

A kwanakin baya ne Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa ba za ta kori almajiran wasu jihohi daga Zamfara ba.

Da yake karbar wasu malamai da suka kai masa ziyarar barka da sallah, Matawalle ya kuma ce gwamnatinsa na maraba da almajiran da aka kora daga wasu jihohi masu son zuwa Zamfara don ci gaba da karatunsu.

Wasu masharhanta na ganin kalaman gwamnan a matsayin bijirewa ce ga matakin da gwamnonin Arewa suka yanke na mayar da kowane almajiri jiharsa ta asali don dakile yaduwar cutar coronavirus.

Shirin karbar almajirai daga jihohi

Sai dai wani jami’in gwamnatin jihar ya da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa Aminiya cewa babu wani da jihar ta yi na karbar almajiran.

Jami’in  Aminiya ya kuma ce har babu wani tanaji da aka yi na samar da wurim kwana ko abincin su almajiran.

“Yanzu haka ana maganar akwai almajirai sama da miliyan biyu a wannan jihar. Ka duba kaga yadda suke yawo bisa tituna kuma idan ka ce na wasu wuri ma su zo ina zaka sa su?

“Na yi tsammanin cewa idan ma za a yi sanawar irin wannan to sai an yi shiri mai kyau,” inji shi.

Taimakon makarantun allo

Wani malami mai karantar da almajirai a garin Gusau mai suna Aliyu Haruna ya shaida wa wakilinmu cewa korar almajairai daga jihohi ba shi ne mafita ba.

“Kamata ya yi gwamnati ta shigo ta tallafa wa irin wadannan makarantu na allon wurin samar da wurin kwana, kiwon lafiya da kuma abinci.

“Hakan zai hana zuwa barace-barace kuma yaran za su samu natsuwar yin karatun,” inji shi.

A cikin watan Disamban 2019 ne wani darakata a Ma’aikatar Kasafin Kudi ta jihar, Hamza Salisu ya ce akwai almajirai miliyan biyu a jihar ta Zamfara.

Ya fadai hakan ne awurin wani babban taro da kungiyar Save The Children ta shirya a garin Gusau.