Shin zuwan mata Umarah ba muharrami maslaha ce?
A addini ba haka abin ya ke ba.
Wasu malaman addinin Islama a Najeriya sun bayyana fahimtarsu kan hukuncin bai wa mata damar zuwa Umarah ba tare da muharrami ba.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar da ke lura da aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta sanar da sahale wa mata zuwa aikin umarar ba tare da muharramin ba, inda wasu malaman ke ganin babu laifi da cewa maslaha ce muddin za a bi matakan da suka da ce.
- Kotu ta umarci Gwamnatin Najeriya ta bai wa mata kashi 35 na mukamai
- Saudiyya ta ba mata damar zuwa Umarah ba tare da muharrami ba
Tun bayan fitar sanarwar mutane suka soma tofa albarkacin bakinsu na ganin cewa wannan sabon mataki da hukumar aikin Hajji ta Saudiyya ta fitar ya ci karo da tsarin addinin Musulunci kuma kamar karan tsaye bisa ga dokokin addinin.
Mutanen sun dogara da hadisin manzon Allah da ya yi umarni kan kada mace ta yi tafiyar da ta wuce kwana uku ba tare da muharrami ba, wanda suma hukumomin saudiyya ke akan wannan fatawa a baya.
Sai dai a yanzu hukumomin sun sauka daga kan wannan fatawa inda suke ganin ba lallai ba ne sai macen tana da muharrami tukun da ta je aikin Umarah kasar ba saboda wasu dalilai.
Tun a baya an sha tambayar malamai akan ko ya halarta mace ta tafi aikin Umarah ita kadai ba tare da muharrami ba saboda wani dalili, ciki har da manyan malaman Saudiyyar kuma sun bayar da amsar cewa hakan bai hallata ba bisa nassi na shari’ar addinin Musulunci ciki har da manyan malaman kasar kamar su Sheikh Alfawzan.
Wannan ya sa Aminiya ta yi kokarin ji ta bakin malamai kan wannan mataki.
Sheikh Shehu Nasiru Muhammad wanda malami ne a bangaren koyar da Addinin Musulunci a Makarantar Horar da Malamai da ke Ringim a Jihar Jigawa, ya bayyana cewa wannan mataki sam ba tsarin addinin musulunci ba ne, kawai dai duk sabbin tsare-tsare ne na kasar Saudiyya na ganin sun faranta wa kasashen Yamma.
“A addini ba haka abin ya ke ba, akwai hadisai masu dinbin yawa cikin litattafan Buhari da Muslim da suka yi hani da mace ta yi tafiya ita kadai ba tare da muharrami ba.”
Har ila yau, ya kara da cewa tsarin halittar mace yana da bukatar a ce tana kusa da wani musamman a ce a yanayi na tafiya wanda ko namiji a wasu lokutan yana bukatar taimako.
“Sai dai kuma idan akwai wani kwakkwaran dalilin da ya sa cire dokar zai fi alkhairi fiye barinta, amma kuma ya zama wajibi su hukumar su fitar da kwakkwaran tsarin da zai ba wa mata damar aikin ba tare da matsala ba kuma cikun aminci. ” Inji Malamin.
Sai dai kuma Malam Muhammad Bashir Hassan Zuru wanda ya ke shugaban Gidauniyar Ci gaba ta Annasim Foundation for Societal Development da ke da ofishi a Zuru, jihar Kebbin Najeriya, ya bayyana cewa, wannan mataki na Saudiyya maslaha ce idan aka yi la’akari da wasu abubuwa.
Ya jaddada hadisin da yayi hani da mace ta yi tafiya ita kadai ba tare da muharramin ba, sannan kuma ya kara da cewa dama akwai sabanin malamai akan wannan batu.
Kuma har ila yau, ya ce idan a ka duba irin abin da wasu matan ke aikata wa a kasar yayin aikin hajji ko umarah da sunan muharrami ya kamata a cire dokar.
“Wadansu matan kana ganinsu kasan cewa ba muharramai ba ne, amma saboda a hukumance babu hali mace ta je aikin ita kadai domin sauke farali, ya sa dole su matan su nemi ko ma waye domin ya tsaya masu a matsayin muharrami, kuma wasu kan wuce gona da iri matuka a mu’amalarsu,” a cewar Malam Zuru.
Dama a baya dai, hukumar ta bai wa mata damar yin Umarah ba tare da muharrami mai shekara kasa da 40 ba, bisa sharadin cewa dole ne su kasance cikin wata tawaga ta mata.