Shinkafa ’yar gida ta karbu a jihohin Yamma
…Kwastam sun kama fatun buhunan shinkafa makare a kwantaina Rahotanni sun nuna cewa, yanzu haka shinkafar da ake nomawa a Najeriya ta cika kasuwannin Kudu maso Yamma a daidai lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, jama’ar sashe sun rungumi wannan shinkafa ta gida hannu bibbiyu inda […]
- …Kwastam sun kama fatun buhunan shinkafa makare a kwantaina
Rahotanni sun nuna cewa, yanzu haka shinkafar da ake nomawa a Najeriya ta cika kasuwannin Kudu maso Yamma a daidai lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa, jama’ar sashe sun rungumi wannan shinkafa ta gida hannu bibbiyu inda ya kai ga bacewar shinkafar da ake shigowa da ita daga waje a cikin kasuwannin yankin. Da kyar da jibin goshi ake samun shinkafar waje a boye.
Kuma a daidai wannan lokaci ne Hukumar Kwasta ta kama wata kwantaina makare da fatun buhuna dauke da tambarin shinkafar waje da aka yi fasa kwaurinsu daga waje ta gabar tekun Apapa a Legas domin damfarar jama’a.
Aminiya ta ziyarci babbar kasuwar kayan abinci ta Bodija da ke Ibadan hedkwatar Jihar Oyo, inda ta gane wa idanunta yadda aka jibge shinkafar gida a shagunan kasuwar. Mafi yawancin ’yan kasuwar da aka zanta da su sun yi maraba da rufe kan iyakokin kasa da mahukunta suka yi.
“A yanzu kasuwancinmu yana bunkasa fiye da shekarun baya’. Kananan ’yan kasuwa suna rububin sarin shinkafar gida daga manyan ’yan kasuwa domin fataucinta zuwa garuruwan wannan sashe,” inji wani dan kasuwa.
Da yake zagayawa da Aminiya cikin kasuwar a matsayinsa na dan kasuwa, Sarkin Hausawan Bodija Alhaji Isyaka Bazamfare, cewa ya yi “Ka ga yadda shaguna da rumfuna suka cika da buhunan shinkafar da ake nomawa a Arewa kuma komai yawanta tana karewa cikin kankanen lokaci. Wannan ne ya sa mutanenmu da ke zaune a nan suke komawa Arewa domin noman shinkafa. Saboda haka nake yin kira ga Gwamnatin Shugaba Buhari ta ci gaba da rufe kan iyakokin kasa domin amfanin jama’a.”
Ita kuwa Hajiya Lola, cewa ta yi “Ni ba ’yar baranda ba ce kuma na dade ina amfani da dukiyata wajen gudanar da harkar kasuwancin shinkafa. Shinkafar gida ta samu karbuwa kwarai a wajen abokan huldarmu, shi ya sa muke bukatar ganin tana isowa cikin lokaci domin ba ma son ana dadewa kafin ta iso nan Ibadan daga Arewa. Muna da abokan hulda masu sayen shinkafar gida suna kaiwa wasu garuruwa. Ba ma bukatar dawo da shinkafar waje,” inji ta.
Alhaji Murtala Ashiru cewa ya yi, “A yanzu kullum tirelolin suna sauke buhunan shinkafa da suka yi sayo daga Arewa zuwa kasuwar nan inda muke sayarwa ba kakkautawa. A gaskiya muddin aka bude kan iyakokin kasa kuma aka ci gaba da shigo da shinkafar waje, to tabbas za a yi wa tattalin arzikin kasa cikas. Domin akwai mutane da yawa marasa aiki ko sana’a da yanzu suka rungumi harkar shinkafa. Kananan masana’antun cikin gida suna noman shinkafa da ta fi karbuwa a wurin jama’a saboda babu tsakuwa a ciki.”
Dan kasuwa Abdulkadir Yakubu, ya ce, “Idan harkar kasuwancin shinkafar cikin gida ta ci gaba kamar yadda take a yanzu to babu yadda za a yi mu yi farin ciki da bude kan iyakokin kasa. Ka ga a kullum ana kara samun ci gaba ta fannin gyara shinkafar gida da dabarun cire mata tsakuwa da haskenta da sanya ta cikin kananan buhu da sauransu. Muna sayar da buhu mai kilo 50 a kan Naira dubu 11,750.”
Wadansu masu karamin karfi da ke sayen mudu-mudu sun yi wa Aminiya bayanai kamar haka: “Na rabu da shinkafar waje kwata-kwata domin wannan ta gida ta fi waccan dadi da gardi.”
“Ban san haka shinkafar gida take da dadi ba sai yanzu da na fara sayenta na gane amfaninta.” “Gwamnatocin baya sun yi kuskure da suka kasa daukar matakin bunkasa noma wannan shinkafa a cikin gida tuntuni.”
A yayin da wannan shinkafa ta fara karbuwa ga jama’a masu fasa kwaurin shinkafa daga waje sun bullo da sabon salo na odar fatun buhuna da babu komai a cikinsu domin damfarar jama’a.
Da yake nuna fatun buhunan masu dauke da tambarin shinkafar kasar waje Kwanturola Muhammed Abba-Kura, ya ce burinsu bai cika ba domin Hukumar Kwastam ta gabar tekun Apapa a Legas ta yi nasarar kama kayan.
Shi ma Kwanturola M.U. Garba, na iyakar Seme cewa ya yi daga lokacin da gwamnati ta bayar da umarnin rufe kan iyakokin kasa zuwa yanzu hukumar ta kama buhunan shinkafa fiye da 5000 da aka yi fasa kwaurinsu daga waje. Shi kuwa Kwanturola Abdullahi Zulkifli, mai kula da jihohin Oyo da Osun cewa ya yi sun yi nasarar kama buhunan shinkafa fiye da 2,500 cikin wannan lokaci.