Shinkafar lambu da miyar kaza

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Tare da fatar an yi Sallah lafiya. Kamar yadda nake fada a kullum akwai hanyoyi da dama da ake bi don girka abinci daban-daban kuma akwai hanyoyi da dama wadannda ake bi don girka shinkafa walau dafa-duka ko fara ko kuma ta lambu. […]

Shinkafar lambu da miyar kaza

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Tare da fatar an yi Sallah lafiya. Kamar yadda nake fada a kullum akwai hanyoyi da dama da ake bi don girka abinci daban-daban kuma akwai hanyoyi da dama wadannda ake bi don girka shinkafa walau dafa-duka ko fara ko kuma ta lambu. Yana da kyau a koyi nau’o’in girke-girke domin yi wa baki da manyan gobe. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Shinkafa
  • Karas
  • Koren wake
  • ‘Peas’

Hadi              

A samu shinkafa a yi mata tafasar farko sai a wanke a tsame ta. Sannan a kankare karas a yayyanka shi kanana sannan a samu koren wake a wanke sai a yayyanka kanana a sake ajiyewa a gefe. A samu peas a wanke sai a ajiye a gefe.

A sake zuba wani ruwan zafi a wuta bayan ya tafasa sai a zuba shinkafar da yankakken karas da koren wake da peas su dahu tare.

A wanke kaza sai a tafasa da albasa da gishiri da thyme. Bayan ya silalu yayi laushi, sai a sake yanka wani albasa da tumatir da attarugu. A fara soya albasa sannan tumatir da attarugun. Idan sun soyu, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa kadan.

A dauko wannan silalen naman kazan a zuba da dan romo kadan domin inganta miyar. Hmmn! Lagwada!

Za a iya hada wannan girkin da sauce din kaza ko na koda.