Shinkafar waje ta fara bacewa daga kasuwanni
Buhunan shinkafar kasashen waje da gwamnati ta hana shigo da ita ta fara bacewa a kasuwannin Kudu maso Yamma. Kuma karancin irin wannan shinkafa ya haifar da tashin shinkafa ’yar waje daga Naira dubu 15 zuwa dubu 18 da 500 a daidai lokacin da ake gudanar da hada-hadar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara. Kuma hakan […]
Buhunan shinkafar kasashen waje da gwamnati ta hana shigo da ita ta fara bacewa a kasuwannin Kudu maso Yamma. Kuma karancin irin wannan shinkafa ya haifar da tashin shinkafa ’yar waje daga Naira dubu 15 zuwa dubu 18 da 500 a daidai lokacin da ake gudanar da hada-hadar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar Shekara. Kuma hakan ya sa mafi yawan masu amfani da shinkafa sun koma sayen shinkafar gida. Binciken da Aminiya ta gudanar a wasu kasuwannin sashen ya nuna cewa ita ma shinkafar gida an fara samun karancinta dalilin rububin sayenta da ake yi a daidai wannan lokaci. Kuma farashinta ya karu daga Naira dubu 14 zuwa dubu 15 a kan buhu.
Wata mai sayar da buhunan shinkafar waje a Kasuwar Bodija, Ibadan wadda ta ki amincewa a dauki hotonta ko shagonta, kuma ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Mako uku ke nan da masu shigo da shinkafa daga waje suka dakata daga tuntubarmu. Shi ya sa mafi yawancinmu muka kara farashin shinkafar da muke da ita kafin isowar wannan lokaci.”
Bayanan da wakilinmu ya tattaro daga wasu garuruwa a jihohin Oyo da Osun da Ondo sun nuna cewa farashin buhun shinkafa ’yar waje ya fara ne daga Naira dubu 17 zuwa 18 da 500. Amma a jihohin Legas da Ogun farashin yana sama yana kasa.
Tashin farashin shinkafar a wannan lokaci yana da nasaba da sanarwar kama buhun shinkafa dubu 40 da ta haura Naira miliyan 279 da Kwastam ta FOU mai kula da sashen ta yi ne.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a ofishinsa a Legas, Kwamandan Hukumar, Kwanturola Muhammed Aliyu ya ce hukumar ta kama shinkafar ce a mako shida na watanni hudu na karshen shekara da aka fi aikata ta’asa a cikinsu. Ya ce, a bana an samu raguwar ayyukan fasakwauri a wannan sashe idan aka kwatanta da bara.
Kwanturola Aliyu ya ce “Ga dai babban zabe ya zo kusa, kuma ga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara da mutane suke so su yi amfani irin wannan shinkafa da aka hana shigo da ita, saboda haka muka tashi tsaye wajen sanya ido sosai muka kai ga wannan nasara.”
Ya nuna takaici kan yadda masu fasakwauri ’suke ci gaba da shigo da shinkafa daga waje alhali akwai irinta da ake nomawa a Najeriya da za ta iya ciyar da kasar nan. Ya kawo misali da Dawanau da Kura a Jihar Kano da Mamasuka a Jihar Sakkwato inda ake dakon dubunan shinkafa da ake nomawa a cikin gida ana fita da ita zuwa kasar Nijar. “Da irin wacce ake nomawa a Abakaliki, wannan kadai ta isa ta ciyar da kasa da abinci tare da samar da kudaden shiga da za su bunkasa tattalin arzikin kasa,” inji shi.
“Kuma mun kama buhunan tabar wiwi 3,700 da suka kai na Naira miliyan 379 da aka shigo da su ta kan iyaka a jihohin Oyo da Ogun. Ina matukar farin ciki da wannan kame a daidai wannan lokaci, domin idan ta fada hannun wadanda za su yi amfani da ita, Allah kadai Ya san aika-aikar da za ta haifar a kasar nan,” inji shi.