Shiri domin gamuwa da Allah (15)
Farkon wannan wata ne muka yi bikin cikan shekara 55 a matsayin kasa mai ’yancin kanta. Mun samu ’yanci ne daga karkashin masu mulkin mallaka. Wannan abin godiya ne sosai ga Ubangiji Allah domin yadda Ya rike mu a matsayin kasa daya, ba mu rabu ba, ba mu lalace ba, kuma Allah Ya sa mu […]
Farkon wannan wata ne muka yi bikin cikan shekara 55 a matsayin kasa mai ’yancin kanta. Mun samu ’yanci ne daga karkashin masu mulkin mallaka. Wannan abin godiya ne sosai ga Ubangiji Allah domin yadda Ya rike mu a matsayin kasa daya, ba mu rabu ba, ba mu lalace ba, kuma Allah Ya sa mu ci gaba a fannoni daban-daban; eh gaskiya ne a sauran fannoni da dama da ya kamata mu yi aiki a kai; wannan zai kunshi kai da ni da kowa. Mu ci gaba da yi wa wannan kasa addu’a, muna rokon Allah Ya taimake mu cikin dukan abin da muke yi; kada mu manta da yin addu’a domin wadanda ke matsayin manya, musamman ma wanda yake shugabancin wannan kasa, Shugaba Muhammadu Buhari. Gaskiyar ita ce; yana bukatar adduo’inmu idan har muna so ya ci nasara a cikin gyaran da yake so ya kawo cikin wannan kasa tamu.
Bari mu komo ga binciken da muke yi, za mu soma sa hankali ne a kan wadanda ba su san Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsu ba, irin wadannan mutane sun riga sun kawo kansu karkashin wata irin la’ana da babu wanda zai iya taimakonsu sai Allah da kansa; kuma taimakon a cikin Yesu Kiristi da kansa ne. Maganar Allah a cikin Littafin Yohanna sura Uku, aya goma sha bakwai zuwa ashirin da daya; Yesu Kiristi ya yi magana da kansa yana cewa: “Gama Allah Ya aiko da dan cikin duniya, ba domin ya yi wa duniya shari’a ba; amma domin duniya ta tsira ta wurinsa. Wanda yana ba da gaskiya gare shi ba a yi masa shari’a ba; wanda ba ya ba da gaskiya ba; an rigaya an yi masa shari’a, domin ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe kadai na Allah ba, Shari’a fa ke nan, haske ya shigo cikin duniya, amma mutane suka fi son duhu da haske, domin ayyukansu miyagu ne. gama kowane ne wanda yake aikata mugunta, kin haske yake yi, kuma ba ya zuwa wurin haske domin kada ayyukansa su tonu; Amma wanda yake aikin gaskiya, yana zuwa wurin haske, domin a bayyana ayyukansa.”
daya daga cikin babban dalilin da zai sa mutum ya fuskanci fushin Allah shi ne matsayin dangantakarmu da Yesu Kiristi, tun daga farko dai mun san cewa mutum ya yi zunubi ya kuma kasa ga darajar Allah. Lokacin da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi a gonar adnin, Allah Ya rigaya Ya ba da wannan kashedi cewa, an halalta wa mutum ya ci daga cikin kowane itace wanda yake cikin gonar adnin; amma Allah Ya ba da wannan umarni kada mutum ya ci daga cikin itace da ke cikin tsakiyar gona, ya gaya wa mutumin da ya halitta; duk ranar da ya ci daga cikin wannan itace , za ya mutu – “Ubangiji Allah kuma Ya dokaci mutumin, Yana cewa, an yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sake, amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ba ka ci: cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.”(Farawa 2 : 16 -17). Wannan shi ne umarnin da Allah da kanSa Ya ba wa mutum. Shaidan ya zo ya rudi mutum a cikin Littafin Farawa 3 : 1 – 4 wanda yake cewa: “Amma maciji ya fi kowace dabbar da Ubangiji Allah Ya yi, hila, ya ce wa macen, ashe Allah Ya ce, ba za ku ci daga dukkan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce wa macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona, an yarda mana mu ci, amma daga ’ya’yan itace da ke cikin tsakiyar gona, Allah Ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taba ba, domin kada ku mutu. Sai macijin ya ce wa macen, ba lallai za ku mutu ba.”
Ina so mu lura sosai da wannan hira da ta wakana tsakanin macen da maciji: A cikin sura biyu na Farawa, Allah Ya rigaya Ya ba su wannan umarni na kada su ci daga cikin ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta, bayan wannan gargadi, sai Ya ba su dalilin da ba Ya so su ci daga cikin wadannan ’ya’yan itacen. A ranar da suka ci, lallai mutuwa za su yi, a cikin sura uku kuma sai Shaidan ta wurin macijin ya zo yana mata hira, ya ce mata ba lallai ne za su mutu ba, haka nan ta yarda da shawarar da Iblis ya ba ta, ta diba ta ci, ta kuma sake dibawa ta kai wa maigidanta Adamu ta ba shi, shi ma ya ci. A lokacin da mutum ya aikata wannan laifi ba su haihu da matarsa ba tukuna, mu sani miji ne ya ke dauke da IRI cikin maniyins, da suka aikata wannan zunubi, dukan abin da yake dauke da shi ne ya la’antu, shi ya sa maganar Allah take cewa: Gama dukkan mutane sun yi zunubi sun kasa kuma ga darajar Allah. Zunubi ya shigo cikin duniya tun kafin a haifi mutum na farko, shi ne ya shafi dukan ’ya’yan da Adamu da Hauwa’u suka haifa, sun haife su ne a lokacin da sun rigaya sun karya umarnin da Allah Ya ba su. Mu sani cewa idan mutum ya aikata zunubi; ba kawai sashin rayuwarsa ne ya aikata zunubin ba; shi da kansa ne da dukan abin da rayuwarsa ta kunsa; shi ya sa ’ya’yan da Adamu da Hauwa’u suka haifa a cikin zunubi ne aka haife su. A cikin Littafin Romawa 3 : 23, maganar Allah na cewa: “Da yake dukkan mutane sun yi zunubi sun kasa kuma ga darajar Allah.” Haka nan cikin Romawa 6 : 23 maganar Allah na cewa: “ Gama hakkin zunubi mutuwa ne; Amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.” Mu san wannan sosai, kodayake mutum ya yi laifi, amma duk da haka Allah Yana kaunarsa. Dalilin da ya shigo cikin wannan duniya ke nan domin ya cece mu daga zunubanmu. Mu shari’a wanda Allah da kanSa Ya zartar, cewa Hakkin Zunubi mutuwa ne, idan kuwa dukkan mutane sun yi zunubi babu shakka hukuncin mutuwa na har abada yana zaune bisa kowane dan Adam. Abu daya ne kawai zai iya zaro mutum daga karkashin wannan hukunci na Allah, wato yarda da shirin ceton da Allah Ya yi ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.
Mu dawo Yohanna 3 : 17 – 19. Maganar Allah tana cewa: “Gama Allah Ya aiko dan cikin duniya; ba domin ya yi wa duniya shari’a ba; amma domin duniya ta tsira ta wurinsa, wanda yana ba da gaskiya gare shi ba a yi masa shari’a ba; wanda ba ya ba da gaskiya ba, an rigaya an yi masa shari’a, domin ba ya ba da gaskiya ga sunan da haifaffe na Allah ba. Shari’a fa ke nan, haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka fi son duhu da haske, domin ayyukansu miyagu ne.” Idan mutum bai san Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ba, gaskiyar ita ce irin wannan mutum yana karkashin la’ana ta farko wadda ke bisan kowane dan Adam wanda bai karbi Yesu Kiristi a matsayin Ubangijinsa da mai cetonsa ba. Tambaya ta farko a yau ita ce, shin wane ne Yesu Kiristi a cikin rayuwarka? kin Yesu Kiristi a matsayin mai ceto kiyayya ne tsakaninka da Allah, sai mu yi tunani sosai a kai.
Ubangiji Allah Ya taimake mu, mu gane hasken da Yesu Kiristi ya kawo cikin wannan duniya, amin.